2025-07-30@19:22:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4994

«Idan mutum ya»:

    Ministocin harkokin wajen kasar Siriya da kuma na HKI zasu gudanar da taro a birnin Baku na kasar Azarbaijan a ranar Alhamis mai zuwa don tattauna maganar tsaro a kasar Siriya kamar yadda suka fada. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya bayyana cewa Asaad Al-Shaibani ministan harkokin wajen kasar Siriya da kuma ministan ayyuka na musamman na HKI Ron Dermer sun gudanar da taro a birnin Paris na kasar faransa a cikinn yan kwanakin da suka gabata, a halin yanzu kuma zasu gudanar da taron a birnin Baku na kasar Azrbaijan a ranar Alhamis mai zuwa. Labarin ya kara da cewa kafin haka dai Al-Shaibani ya ziyarci Moscow kamar yadda wata majiya wacce bata son a...
    Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa tun daga shekarar nan ta 2025 har zuwa 2026. IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya. Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa Asusun ya yi hasashen samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya da kashi 3.4 a 2025, ƙari a kan hasashen kashi 3.0 da ya yi a watan Afrilu. Haka kuma, IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai samun ƙarin bunƙasa da kashi 3.2 a 2026, saɓanin...
    “Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi.   A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da lamarin ya shafa. Makabartar Jajeri Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a Maiduguri, ta ce rundunar ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da abin ya shafa.   Ya kuma tabbatar da cewa, “Abin takaici, gine-gine takwas...
    Yau Laraba 30 ga wata, an kira taro a ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), inda aka yanke shawarar gudanar da cikakken zama na 4 na kwamitin koli na 20 na JKS a watan Oktoba na shekarar da muke ciki, domin nazari kan shawarar tsara shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15. Taron ya nuna cewa, lokacin gudanar da “Shirin shekaru biyar-biyar din na 15”, lokaci ne mai muhimmanci a fannin tabbatar da ingantaccen tushe, da kokarin raya zamanantar da kasar Sin bisa tsarin gurguzu. A yanzu haka yanayin ci gaban kasar Sin yana fuskantar manyan sauye-sauye masu sarkakiya, akwai kuma damarmaki bisa manyan tsare-tsare da ma kalubale...
    Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati. Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri  Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Bakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace. “Jihar Katsina na...
    Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.   Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.   Sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya yi namijin kokari wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da hadin kan kasa.   Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa, da fadar shugaban kasa, da sauran al’ummar Nijeriya da su goyi bayan nadin, inda ta ce hakan zai karfafa cibiyoyin gargajiya da kuma samar da hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar. Daga kanmu, magana...
    Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa. Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri  Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno An sanar da wannan naɗin ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa da Hukumar CDCFIB, ta fitar, wacce sakatarenta, Abdulmalik Jibrin, ya rattaba wa hannu. Wannan naɗin na zuwa ne bayan da shugaban hukumar na yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, ke shirin ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60 a duniya. Olumode Samuel Adeyemi yana da ƙwarewa da gogewa a aikin...
    Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
    Ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka da safiyar ranar Laraba a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ya haddasa ambaliya. Ruwan wanda ya fara sauka tun da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ya cika tituna da gidaje musamman a unguwannin Dala, Bulunkutu, titin Damboa, filin Polo, da Federal Low Cost. Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Ambaliyar ta haifar da cikas a rayuwar jama’a, inda ruwa ya lalata dukiyoyi mutane masu tarin yawa. Mutane da dama dun fice daga gidajensu domin neman mafaka, musamman waɗanda gidajensu ruwa ya mamaye. Hakazalika, wasu tituna sun shafe sakamakon mamakon ruwan, lamarin da ya hana mutane fita ko komawa gidajensu...
    Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari Shugabannin manyan hukumomin watsa labarai na ƙasa Hukumar Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) – sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, bisa rasuwar mijinta, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Daraktan Kula da Yankin Arewa maso Yamma na Rediyon Najeriya, Mallam Buhari Auwalu, shi ne ya gabatar da tawagar, inda ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasar a matsayin babban rashi ga iyalinsa, Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Yayin ziyarar, Daraktan Sashen Injiniya na Hedikwatar Rediyon Najeriya, Injiniya Sanda Askira, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin...
    Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno. Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza. Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000 ’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai. Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su. A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT. Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya,...
      Ministan Ƙasa na Ci Gaban Yankuna, Uba Maigari Ahmadu, ya yaba wa ci gaba da tattaunawa tsakanin jami’an gwamnati da shugabannin arewa yana mai cewa wannan “tattaunawa ce mai tarihi kuma cike da ƙarfi,” yana nuna cewa hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu ga Arewa ya fara samo asali kuma yana haifar da sakamako.   Yayin jawabi a taron gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello a rana ta biyu na zaman tattaunawa tsakanin gwamnati da alumma, ministan ya jaddada cewa wannan zama shi ne karo na farko a tarihin mulkin Najeriya inda ministoci, daraktocin hukumomi, shugabannin kwamitoci, da sauran manyan jami’an gwamnati daga Arewa suka “mika kansu don a yi musu tambayoyi” daga mutanen da suke yi wa hidima....
    Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar. Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su ne ci gaba da zama ginshikin dangantakar ƙasashenmu biyu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Ahmed Makama Hardawa, ya rasu. Marigayin ya rasu ne ranar Talata a Abuja, bayan ya yi fama da gajeruwar jinya. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ne ya tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa ranar Laraba. Muna tafe da karin bayani…
    A ci gaba da hare-haren da dakarun Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, yanzu adadin Falasdinawan da suka kashe ya kai 60,034. A cewar wasu alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, baya ga wannan, adadin wadanda aka raunata kuma a yanzu sun haura 145,870. Ma’aikatar ta kuma ce har yanzu ana zargin akwai mutanen kuma da ke karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa, wadanda ba za a iya ciro su daga ciki ba. Fiye da kaso daya cikin uku na mutanen yankin na shafe kwanaki ba su ci abinci ba, kamar yadda wani rahoton samar da abinci mai lakabin IPC na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar. Rahoton ya ce ana samun karin hujjoji da ke nuna ana fama da...
    Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi. Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna. Kwamandan NDA wanda tsohon dalibi ne a kwalejin ya bayyana jin dadinsa da yadda dalibai ke gudanar da ayyukansu ya yabawa mahukunta da ma’aikatan FGC Kaduna bisa yadda suke kiyaye ka’idoji. A nasa jawabin shugaban kungiyar tsofaffin dalibai ta FGC Kaduna, Kwamared Seyi Gambo ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da gudummawar ta wajen daukaka darajar kwalejin ta hanyar daukar matakai na koyar...
    An ceto dukkanin mutane 14 ba tare da wani ya ji rauni ba, amma abin baƙin ciki, wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Abba daga garin Funtua ya rasa ransa kafin isowar ’yansanda. A wani lamari da ya faru a ranar 28 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 11:27 na dare, an sake kiran ’yansanda daga ƙauyen Zagaizagi, inda aka sanar da su cewa wasu ’yan bindiga sum hari tare da sace wasu mutane ƙauyen. ’Yansanda sun isa wajen suka gwabza da ’yan bindigar, kuma sun samu nasarar ceto wasu mutane 14 da kuma ƙwato shanun da aka sace guda biyu. Amma, mutane biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun rasa rayukansu a harin. Rundunar ta ce har yanzu tana...
    Sakatariyar kungiyar kasashen yankin Caribeans  ( Caricom) ta bayyana cewa; kasashen yankin suna son ganin bunkasa alakar kasuwanci da abokansu na nahiyar Afirka.  Sakatariyar kuniyar ta kasashen Caribbian ta bayyana hakan ne a lokacin jawabin bude taron karawa juna sani a taron kasuwanci da zuba hannun jari a tsakanin yankin da nahiyar Afirka da aka yi a Grenada. Ta kuma kara da cewa:  Wajibi ne mu bude sabuwar kafar kasuwanci a tsakanin yankunan biyu, kuma ya kamata ace giman kasuwanci a tsakanin bangarorin biyu ya karu da kaso 3% na jumillar kasuwancinmu.” Kamfanin dillancin labarun “Reuters’ya bayyana cewa wannan matakin na kasashen Caribbean yana nuni da sauyi a huldarsa ta kasunwaci da Amurka da Canada da kuma kasashen turai da...
    ’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su....
    Kwamitin Majalisar Dattawa na bin Diddigi ya ba Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) wa’adin mako uku ya amsa tambayoyi kan rashin ba da ba’asi kan Naira tiriliyan 210 da ba a san inda suka shiga ba daga shekarar 2017 zuwa 2023. An dai bayar da wa’adin ne ga shugaban kamfanin na kasa, Bayo Ojulari, wanda ya bayyana a gaban kwamitin ranar Talata, bayan ya bayar da hakuri kan rashin bayyanarsa yayin gayyatar da kwamitin ya yi masa a baya. Yadda ’yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Ahmed Wadada Aliyu (Nasarawa), ya tsaya kai da fata cewa dole kamfanin ya bayyana inda...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa Labarai na Kaduna (KSMC), ne za a maye gurbinsa. Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang Gwamna Sani ya gode wa Farfesa Bello bisa ayyukan da ya gudanar, inda ya ce shi ne kwamishinan ilimi na farko a gwamnatinsa, kafin daga baya ya...
    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu. A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu. Sharuɗɗan da firaministan ya gindaya sun haɗa da: Amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar sake shigar da agaji Gaza Amincewa da yuarjejeniyar zaman lafiya na dogon lokaci wanda zai ”samar da ƙasashe biyu” Tabbatar da cewa ba za a ci gaba da ƙwace Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye ba Haka kuma Keir Starmer ya kuma sake jaddada buƙatun...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.   Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.   Gwamna Yusuf ya...
    ’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su. Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da...
    Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar.   Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi.   Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu.   Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
    Iran da Rasha sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kafofin yada labarai da yaki da labaran karya Jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali ya gana da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Talata inda suka yi musayar ra’ayi kan bunkasa hadin gwiwar kafofin yada labarai. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka hada da yiwuwar gudanar da harkokin yada labarai, da nazarin yiwuwar bunkasa hadin gwiwar kafofin watsa labaru, da hanyoyin yin tasiri a kafofin watsa labaru, da matakan hadin gwiwa don kara fahimtar ra’ayin jama’a a kasashen biyu. Bangarorin biyu sun yi tsokaci kan yadda kafafen yada labarai ke yada jita-jita da nufin yin zagon kasa ga dangantakar...
    Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin ayyukan raya kasar da take yi a yankin. Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kasa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Talata, Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), ya yi zargin cewa ana nuna wa yankin bambanci a muhimman manufofin gwamnati da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa. ACF ta ce hakan na faruwa ne duk da irin irin tarin gudunmawar da yankin ya ba gwamnatin mai ci a zaben 2023 da ya gabata. DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Remi Tinubu ta...
    Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Ya ce tallafin da kasarsa ke baiwa Tel Aviv yana nan daram. Fira ministan na Burtaniya ya jaddada cewa kin amincewar da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi na samar da kasashe biyu kuskure ne kuma kuskure ne na dabi’a da dabaru. Ya jaddada cewa dole ne a bude mashigar kasa sannan kuma a bar manyan motocin...
    Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga. Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci. A ƙarshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe mutane a Kauran Namoda a Jihar Zamfara. Sannan ƙungiyar Boko Haram har yanzu na ci gaba da zama barazana a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu. Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.   Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu...
    Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba,  Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma.   Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
    Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
    Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA). Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau Talata. Starmer ya ce za su amince da ‘yancin Falasɗinu idan har Isra’ila ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshen halin da ake ciki a Gaza ba, ciki har da tsagaita wuta da kuma tsarin samar da zaman lafiya na din-din-din. Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya A cewarsa, hakan...
    Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA). Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau Talata. Starmer ya ce za su amince da ‘yancin Falasɗinu idan har Isra’ila ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshen halin da ake ciki a Gaza ba, ciki har da tsagaita wuta da kuma tsarin samar da zaman lafiya na din-din-din. Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya A cewarsa, hakan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi. Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu. Ana iya tuna cewa, tun...
    Jamhuriyar Nijar da ƙasar Rasha a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 sun ƙulla yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kuma haƙar yuraniyom. Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce bayan ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashi, Mista Sergei Tsivilev. Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma “Muhimmiyar manufarmu ita ce mu ƙara inganta rayuwar mutanen Nijar da na Rasha,” in ji Sergei, kana ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom. “Mun amince cewa za mu horar da...
    Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya, da na hidimomin al’umma a gundumomin Miyun da Huairou, a kokarin ganin rayuwa ta dawo kamar yadda take a wuraren, an kuma dawo da ayyuka kamar yadda aka saba. Ban da haka kuma, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa ta kasar sun zuba kudin Sin yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 49 don tallafawa biranen Beijing, da Tianjin, da lardunan Hebei, da...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da shahadar wadanda suka yi shahada a yankin. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka halarci tarun iyalan shahidan yakin kwanaki 12 ne da jami’an gwamnati da kuma manya-manyan sojojin kasar da sauran Jama’a. Jagoran ya kara da cewa, HKI da Amurka basu fadawa JMI da yaki don shirin ta makamashin Nukliya ko don take hakkin...
    Ma’aikatar leken asiri na JMI ta bada sanarwan cewa ta gano shirin makiya na kashe manya-manyan Jami’an gwamnati har 35 a kasar kafin yakin da suka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar na fadar haka, ta kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 sun yi kokarin kashe many-manyan Jami’an gwamnati har 35 a cikin yakin. Da kuma wasu 13 watanni kafin yakin, amma saboda matakan da ma’aikatar ta dauka hakan bai faru ba. Labarin ya kara da cewa, hukumar a tsaye take kan makirce-makircen makiya, sannan kuma tana daukar matakan da suka dace don hana  kutsawar su a cikin kasar da kuma cutar da shuwagabanni da kuma mtanen gari. A wani...
    Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da kuma hanasu kudadensu wanda gwamnatin jihar take yi. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa duk tare da kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi don kada likitocin su shiga yajin aiki amma a safiyar jiya litinin likitocin sun dakatar da ayyuka a dukkan asbitocin gwamnatin Jihar. A bangaren kasha na jami’ar koyon aikin likita na Jami’ar Lagos marasa lafiya da dama sun fito don ganin likotocinsu amma sai aka fada masu duk sun shiga ya jin aiki. Wanta marasa lafiya wacce taki fadar sunanta ta fadawa Premium times kan cewa ta zo ganin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi. Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu. Ana iya tuna cewa, tun...
    Ambaliya sanadiyyar wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi ajalin mutane 30 a Arewacin China, lamarin da ya tilasta kwashe mutane fiye da 80,000 zuwa Beijing, babban birnin kasar. Jaridar Beijing Daily ta ruwaito cewa ruwan saman ya haddasa rufe hanyoyi da dama da kuma katsewar lantarki a kauyuka sama da 130 yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto. Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri A jiya Litinin ce Shugaban China, Xi Jinping ya ba da umarnin daukar matakan gaggauwa a yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliya sakamakon mamakon ruwan da ake hasashen za a ci gaba...
    Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen. Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa  na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa. Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama. Dr Shuaibu ya bayyana cewa,...
    2. Asibitin Turai Yar’Adua 3. Asibitin Amadi Rimi 4. Asibitin Jibia 5. Asibitin Funtua Zango, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wanda ke fama da cutar ya samu magani cikin sauƙi ba tare da biyan kuɗi ba. Zazzabin taifod yana yaɗuwa ne musamman a lokacin damina, kuma yana da nasaba da amfani da ruwa mai datti da rashin tsafta. Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, ciwon kai, da gajiyar jiki. Gwamnati ta shawarci jama’a da su riƙa kula da tsafta da kuma hanzarta zuwa asibiti idan sun ga irin waɗannan alamomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...
    Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
    Sannan su ɗaure kayan da iska za iya ɗauka. Ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi kafin tashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani. A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa. Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari  ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Idan aka maimaita ta’asar kai hari kan Iran, za ta mayar da martani ta hanyar da ba za a iya boyewa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani kan barazanar da jami’an Amurka suka yi a baya-bayan nan, inda ya ce idan aka sake kai hari kan Iran, za ta mayar da martani mai tsauri wanda ba zai yiwu a iya boye ba. Araghchi ya kara da cewa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin din nan cewa: Iran, kasar da ke da al’adun gargajiyar da ta shafe shekaru dubu bakwai na wayewar kai, ba za ta taba mika kai ga barazana...
    Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...
    Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.” Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar...
    Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara. Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu. Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar. Ya buƙaci al’umma da su daina suka, su kuma tallafa wa jami’an tsaro da addu’a da fahimta, ganin irin sadaukarwar da suke yi domin kare rayukan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da  Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar. Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar. Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a. Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu. Kwamishinan...
    Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya. Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa. Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba. Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe...
    Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar. A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai...
    Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal  Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada. Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin...
    A yankin sweida na kudancin kasar Siriya mazauna wurin sun bayyana cewa abinci da ruwa da kuma kayakin bukatu nay au da kullum sun fara karanci sosai a yankin saboda yakin makonni uku da suke fafatawa da sojojin sabuwar gwamnati a Damascus. Jaridar The National ta Amurka ta bayyana cewa yankin sweida na kudancin kasar Siriya wanda kuma HKI ta dade tana shigowa yankin ta fita a halin nyanzu yana fama da karancin abinci da ruwansha. Sannan da alamun har yanzun sojojin sabuwar gwamnatin kasar Siriya tana ci gaba da hana shigowar abinci da ruwa yankin duk tare da shelanta tsagaita wuta da aka yi. Labarin ya kara da cewa. an kashe daruruwan mutane a fafatawar da mayakan hTI suka...
    Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON. Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa  a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100. Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.  
    Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa. Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro da bai kai shekaru uku da haihuwa ba. Za a kebe tallafin daga cire harajin kudin shiga kuma ba za a kidaya shi a matsayin kudin shiga na iyalai ko na mutum daya ba a yayin da ake tantance masu karbar taimakon, inda abun zai zama kamar dai irin na wadanda ke karbar alawus na cin abinci ko kuma wadanda ke rayuwa cikin matsananciyar wahala....
    Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar  mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu. A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in. Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu. Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo. Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa. Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.   RN  
    Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da takwarorinsu na rundunar sojin ƙasa sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 45 da ke addabar wasu sassan Jihar Neja. Bayanai sun ce an kashe ’yan ta’addan ne a ƙauyen Iburu da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a ranar Juma’ar da ta gabata bayan jami’an DSS sun tattaro bayanan sirri kan harƙallar miyagun a yankin. Mutum miliyan 1.2 na fama da ciwon hanta a Kano Najeriya ta ba wa Habasha kyautar iri da itatuwan cashew 100,000 Majiyoyin tsaro sun ce DSS ta samu bayanan sirri kan wani hari da ’yan ta’addan ke shirin kaiwa ƙauyen Iburu a kan babura, lamarin da sojojin da ke shirin ko-ta-kwana suka tari hanzarinsa. Ɗaya daga cikin majiyoyin ya shaida cewa...
    Da safiyar yau Litinin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, bisa taken “Cimma burikan da aka tsara domin neman bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al’umma a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025”. A yayin taron, jami’in babbar hukumar buga haraji ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 ya zuwa yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa shirin da aka tsara, kana, bisa hasashen da aka yi. Sakamakon haka, jimillar haraji da kudaden da hukumomin buga haraji sun karba ta zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 155, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari na yawan kudaden shiga na kasar Sin. Cikin adadin, kudin haraji zai kai sama...
    Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan. A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho. Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar. Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan...
    Kasar Sin ta fitar da manyan manhajojin AI har 1,509, matakin da ya sanya ta kaiwa matsayi na daya cikin jerin sassan duniya da suka fitar da jimillar irin wadannan manhajoji 3,755. Masana na ganin bunkasar sashen masana’antun fasahohin AI na kasar Sin zai ingiza sabbin nasarori a fannin. A jiya Lahadi, yayin taron karawa juna sani na kasa da kasa game da AI na shekarar 2025, an gudanar da baje kolin nasarori da aka cimma a fannin masana’antun AI na Sin. Kuma a cewar sashen lura da bayanai na cibiyar bincike game da harkokin sadarwa ta Sin, adadin kamfanonin AI na sassa daban daban na duniya ya kai sama da 35,000, yayin da Sin ke da irin wadannan kamfanoni...
    Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Kano ta sanar da cewa akwai aƙalla fiye da mutum miliyan 1.2 da ke fama da ciwon hanta da ake kira Hepatitis B a faɗin jihar. Kwamishinan Lafiya, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yau Litinin yayin wani taron manema labarai a Cibiyar Tiyata ta Gaggawa da ke Asibitin Nasarawa a birnin Dabo. Najeriya ta ba wa Habasha kyautar iri da itatuwan cashew 100,000 An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja Aminiya ta ruwaito cewa wannan sanarwar na zuwa ne a daidai Ranar Ciwon Hanta ta Duniya ta bana. Kwamishinan ya bayyana ciwon hanta a matsayin matsala babba da ana iya magance ta matuƙar an miƙe tsaye a kai. Ya yi bayanin cewa muddin...
    A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi. Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan. An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka. Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki,...
    Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya.   Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba.   Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin.   Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan. Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance...
    Gwamnatin Najeriya ta ba wa ƙasar Habasha kyautar itatuwan cashew guda 2,000 da kuma irin cashew guda 100,000. Najeriya ta bayar da kyautar irin ne a wani bangare na yunƙurin taimaka wa ƙasashen biyu wajen samar da abinci mai yawa da kuma ƙarfafa dangantakarsu. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da wannan kyauta, da za ta iya shuke ƙasa mai fadin hekta 600. Shettima ya bayar kyautar ce a lokacin da ya isa birnin Adis Ababa, babban birnin kasar, domin halartar Babban Taron Majalisar Xinkin Duniya Kan Tsarin Abinci. Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja Ministan Harkokin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba.  Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli. Wannan matakin na  Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba...
    A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
    Wani jami’in kasar Ukiraniya ya bayyana cewa, a kalla mutane 8 ne su ka jikkata sanadiyyar munanan hare-haren da Rasha ta kai wa birnin Kiev ta hanyar amfani da makamai masu linzami. Shugaban sha’anin tafiyar da Mulki na soja a birnin Kiev Taimur Tikatishinko ya wallafa sanarwa a shafinsa na “Telegram’ cewa; A tsakanin wadanda su ka jikkata din da akwai karamin yaro dan shekaru 3, kuma tuni an dauki mutane 4 zuwa asibiti, daya daga cikinsu yana cikin mummunan hali. Shi kuwa magajin birnin na Kiev Fitali Kikitshiko cewa ya yi, mutanen da su ka jikkata suna zaune ne a cikin gidaje mabanbanta a unguwa daya. Har ila yau ya kara da cea; Harin ya haddasa fashewa mai karfi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal  ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027. Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.” Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na                         kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan. Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar...
    Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran. Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba. A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da...
    Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran. Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba. A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da...
    Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci  ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi. Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen...
    An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar. Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro. Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gwawar mutum 15, amma ana ci gaba neman wasu mutum uku, ko da yake cewa...
    An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar. Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro. Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gwawar mutum 15, amma ana ci gaba neman wasu mutum uku, ko da yake cewa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Domin neman mafita da samar da zaman lafiya mai ɗaurewa, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman da zai hhaɗa ukkanin bɓangarorin da abin ya shafa da jami’an gwamnati domin daddale asalin filayen da aka ware domin noma da ware iyakokin noma da kuma na kiwo domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin kowane ɓangare. Gwamnan ya jaddada cewa dukkanin ɓangarorin biyu na manoma da makiyaya kowa na da rawar da yake takawa wajen ci gaban tattalin arziki, don haka ya nemi a mutunta juna a zauna lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    A dai-dai lokacinda hankalin mutane da dama suka tashi dangane da abinda ke faruwa a Gaza, kasashen Faransa da saudia sun shirya gudanar da gagarumin Taro a birnin New na kasar Amurka a dai-dai lokacinda ake gudanar da babban taron majalisar dinkin duniya na shekara-shekara. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Bin Farhan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, za’a gudanar da taron a ranar 28-29 ga watan Yulin da muke ciki , kuma akwai fatan kasashen duniya zasu tattaunawa wannan batun sosai don kawo karshen rikicin gabas ta tsakiya bayan shekaru fiye da 70 ana gudanar da ita. Ministan ya kara da cewa a wannan taro...
    Allah Ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Farfesa Alhassan Gani, rasuwa a safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 66 a duniya. Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Kafin rasuwarsa, Farfesa Gani yana koyarwa a Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Farfesa Gani, ya yi fice wajen sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi, musamman lokacin da yake jagorantar Jami’ar Kashere. Gwamna Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta’aziyyarsa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana rasuwar Farfesan a matsayin babban rashi ga harkar ilimi da...
    Bisa alkaluman da aka fitar a dandalin shafin intanet, ya zuwa ranar 27 ga watan, jimillar kudin shigar da kasuwar fina-finai ta Sin ta samu a lokacin zafi na bana ya zarce yuan biliyan 5, kuma adadin masu kallon fina-finai a lokacin ya kai miliyan 129. Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da hare-haren sojojin Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya ko kuma yakin duniya na biyu. Daya-bayan-daya zuwa yanzu, ana ci gaba da fitar da wasu fina-finai, da shirye-shirye, da wasannim kwaikwayo, da kide-kide, da raye-raye da kuma ayyukan fasaha dake da jigon tunawa da tarihin yaki da hare-haren na Japan da kuma gadon ruhin yaki da hare-haren. Daga cikinsu, za a fitar...
    Janar majid Khatami Shugaban Bangaren Leken Asiri Na dakarun IRGC masu kare juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa, rundunarsa tana sa ido akan take –taken kasashen Turai dangane da ayyukan sharrin da HKI take gudanarwa a yankin. Ya kuma kara da cewa rundunarsa tana da hanyoyin wadanda zata yi amfani da su , wanda daga karshe turawan ne zasu cutu a goyon bayan da suke bawa HKI. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Janar Majid Khatami yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron addu’a da girmama Ghulam Hussan Ghaiba a nan Tehran. Dangane da marigayin ya bayyana cewa ya kasance cikin wadanda suka je yakin kare kasa na shekaru 8, kuma a cutu da makaman guban da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Afganistan Amir Khan Muttaki a yau Lahadi inda bangarorin biyu suka tattauna dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amuran yankin wadanda suka hada da batun gaza da kuma halin da take ciki. Kamfanin dillancin labaran Tasnima na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana cewa kasar Iran ta kira taron gaggabawa na kungiyar OIC ta kasashen musulmi don tattauna wannan batun. A nashi bangaren muttaki ya bukaci gwamnatin kasar Iran ta maida yan kasar Afganistan wadanda suke zauna a kasar zuwa gida tare da mutuntasu. Kafin haka dai a lokacin yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da Iran jami’an tsaro a kasar...
    Muƙaddashiyar Shugabar Jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce gwamnatin APC ce ta fi jefa ’yan Najeriya cikin talauci sama da kowace gwamnati a tarihin ƙasar nan. Da ta ke zantawa da manema labarai a Jihar Kaduna, Sanatan ta ce jam’iyyar LP ta shirya tsaf don gyara kurakuran da gwamnatin APC ta tafka. Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa Ta roƙi ’yan Najeriya da su bai wa LP goyon baya, inda ta ce jam’iyyar za ta kawo canji na gaskiya. Ta ce halin da ake ciki na wahala a ƙasar nan ya yi muni ƙwarai, kuma ta d6ora alhakin hakan kan gwamnatin APC. Game da sauya...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci zaman sasanci domin kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Nahuta da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Wannan sasanci na zuwa ne bayan makonni uku da aka shafe ana rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu. Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman A taron da aka yi a ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da yadda dukkanin ɓangarorin suka fahimci juna. Gwamna Bala, ya buƙaci jama’a da su guji duk wani abu da zai tayar da hankali, tare da yin kira a bin doka da oda. Ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai domin hana rikici...