Ɗan sanda ya harbe kansa da bindiga bisa kuskure a Kano
Published: 29th, September 2025 GMT
Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro.
Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro.
Limami ya rasu a hannun ’yan sanda a Kano 2027: APC za ta ƙwace Kano ba tare da taimakon Kwankwaso ba – Jigon APCRahotanni sun nuna cewa jami’in, wanda yake aiki a ofishin ’yan sanda na Hotoro, ya shiga bayan gida ne lokacin da abin ya faru.
Wata majiya ta ce, yayin da bindigarsa ƙirar AK-47 ke rataye a wuyansa, sai ya matsa kunamar bindigar bisa kuskure.
“An samu bindigar, mai lambar rajista GT 4177, tare da harsashi ɗaya da aka harba. An lissafa harsashi 29 daga cikin 30 da aka ba shi,” in ji majiyar.
An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
An ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin domin yin bincike.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa har yanzu ana bincike kan lamarin, kuma za su bayyana sakamakon nan gaba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA