Aminiya:
2025-10-13@15:50:24 GMT

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Bi Ba Don Magance Taƙaddamarsu

Published: 29th, September 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Ɗangote don a sasanta a yau.

Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan ƙwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Ɗangote ta salami ma’aikata fiye da 800.

Sai dai wasu masana suna ganin tun farko bai kamata lamarin ya kai ga haka ba, da an bi wasu hanyoyi.

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata

Waɗannan hanyoyi shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai binciko.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno.

Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram.

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi 

Ko da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a.

Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin.

A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da roka, jirage marasa matuƙa, da bama-bamai wajen kai harin.

Sai dai sojojin sun mayar da martani, inda suka kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan.

Ya ƙara da cewa wasu motocin yaƙi na sojojin sun lalace, amma duk da haka dakarun sun yi tsayin daka wajen yaƙar maharan.

Bayan harin, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin hana bin hanyar Ngamdu zuwa Damaturu, wanda hakan ya tilasta rufe hanyar na ɗan lokaci.

Daga baya,sojoji sun cire bama-bamai guda uku, sannan suka sake buɗe hanyar ga matafiya.

Laftanar Kanar Uba, ya ce an ƙara wa dakarun kayan yaƙi da harsasai domin ci gaba da fafatawa.

Rahotanni sun nuna cewa gawarwakin ’yan ta’adda kusan 15 aka samu a kusa da ƙauyen Bula Wura.

Rundunar Sojin Najeriya ta yaba wa jarumtar dakarun, tare da tabbatar wa jama’a cewa zaman lafiya ya samu a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno
  • Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
  • Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
  • Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza
  • CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
  • ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali – Likita