Kotun Sojin Nijeriya Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Soja Da Ya Kashe Ɗan Adaidaita
Published: 19th, September 2025 GMT
Kotun ta kuma samu Musa da mallakar harsashi na musamman har guda 34 mai nauyin (7.62mm) ba bisa ƙa’ida ba.
Ga laifin kisan kai, sashe na 220 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 221, Musa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A laifi na biyu na mallakar harsasai ba bisa ka’ida ba, sashe na 8 (1) na dokar bindigogi, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.
A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar DukkuDarekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.
DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.
Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.
Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.