Collins Daga BUK Na Dab Da Shiga Kundin ‘Guinness World Record’ Tare Da Goyon Bayan Indomie
Published: 2nd, October 2025 GMT
Collins mutum ne mai jajircewa da azama. Bayan gaza cin nasara da ya yi a ƙoƙarinsa na kafa tarihi a shekarar 2024, ya ɗauki tsawon shekara guda yana ɗaukar horo da shiri sosai domin wannan rana. Ya ce, “Na koyi darussa da dama daga ƙoƙarina na farko. Yanzu na shirya sosai. Tare da goyon bayan Indomie, domin mu kafa tarihi.
A wajen Collins, fentin fuska ba nishaɗi ba ne kaɗai ba, fasaha ce da ke bayyana fikira da ƙirƙira. Ƙoƙarinsa ya haskaka wa duniya irin baiwar da matasa ’yan Nijeriya suke da ita a idon duniya.
Kamfanin Indomie, ya jima yana bayar da gudummawa da goyon baya a fannin ƙirƙira da ilimi a tsakanin matasa, kamfanin ya bayyana farincikinsa da alfaharinsa na ɗaukar nauyin Collins.
Collins ya bayyana cewa, “Ina son na zama sanadin sanya Kano da Nijeriya a idon duniya, domin mu nuna muna da ƙwararrun mutane da za su iya karya fito da fasahar su a idon duniya. Yau na yi fentin fuska 17 a cikin minti 2 da sakan 40, wanda ya zarta abin da aka ba ni na yin fentin fuskar mutane 13. Ina gode wa Indomie da iyalina da abokaina da masu yi min fatan alheri.”
Daga cikin waɗanda suka halarci taron, wani ɗalibin BUK, Sulaiman Haruna, ya ce: “Ina addu’ar Collins ya yi nasara saboda ya nuna bajinta sosai.” Wani shaidar gani da ido a taron, Jimoh Momoh, ya yaba da ƙoƙarinsa yana mai cewa Collins zai iya kafa tarihin. Wata ɗaliba mai suna Aisha ma ta nuna mamakinta kan lamarin Collins ta kuma bayyana goyon bayanta da fatan ganin Collins ya samu nasara.
A yanzu da dai bayan kammala wannan taron kallo ya koma sama, kowa na jiran mataki na gaba daga Guinness World Records. Da zarar mahukunta sun kammala tantance ƙoƙarin Collins, suka tabbatar da nasararsa, zai shiga cikin jerin masu rike kambun duniya, lamarin da zai ƙara wa matasan Nijeriya ƙwarin guiwa da ƙarfafa fasaha a ƙasa baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ɗalibi
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA