Aminiya:
2025-11-18@11:02:29 GMT

Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi

Published: 1st, October 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su.

Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo.

Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba.

Ya ce wannan lamari babban rashi ne, kuma gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Ibaji gaba ɗaya.

Gwamna Ahmed Usman Ododo, ya aike ta’aziyyarsa, inda ya ce gwamnatin jihar na tare da al’ummar Ibaji a wannan lokaci na baƙin ciki.

Ya bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar da sauran hukumomi, umarnin su bai wa waɗanda abin ya shafa tallafi.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiki tare da Hukumomin Tarayya domin ƙara tsaro a harkar sufuri ta ruwa, don guje wa faruwar irin wannan iftila’i a nan gaba.

Haka kuma ya shawarci al’umma da su guji loda mutane da yawa a cikin jirgi, kuma suke amfani da rigar ruwa da sauran hanyoyin kariya idan suna tafiya ta ruwa.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ibaji, Hon. Ugeh Emmanuel, ya bayyana wannan hatsari a matsayin abun takaici.

Ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka radu ba, domin babu wanda zai ya tabbatar da yawansu a lokacin da suka hau jirgin.

A cewarsa, mafi yawan waɗanda suka rasu sun nufi Ilushi ne domin shagalin bikin ranar samun ‘yancin kan Najeriya, wanda ya zama al’ada a garin, kafin aukuwar hatsarin.

Idan za a tuna, a ranar 29 ga watan Nuwamban 2024, wani hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin mutuwar mutum 19 lokacin da jirgin katako ɗauke da fasinjoji 60 daga garin Kupa a Lokoja ya nufi kasuwar Kacha a Jihar Neja ya kife.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnati Hatsarin Jirgin Ruwa ta aziyya

এছাড়াও পড়ুন:

Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Waidu Shuaibu, ya umarni dakarun soji cewa ya zama tilas su nemo sannan su ceto daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Jihar Kebbi.

Janar Waidi Shuaibu ya bayar da umarnin ne a yayin ziyarar aiki da ya kai, Jihar Kebbi, washegarin harin ’yan bindiga suka kai makarantar da ke Karamar Hukumar Danko Wasagu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran
  • PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu