Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano
Published: 1st, October 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa.
Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka gudanar a jihar.
A bisa al’ada dai Gwamna kan jagoranci hukumomin tsaro wajen gudanar da faretin bikin ranar a duk ranar daya ga watan Oktoba. To sai dai a bana, ba a ga Kwamishinan ’Yan Sandan na Kano ba, sannan babu ko dan sanda daya a wajen bikin.
Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sojoji sun kama ’yan sandan bogi da motoci 2 makare da tabar wiwi a TarabaDa yake jawabi a wajen taron da ya gudana a filin was ana Sani Abacha da ke Kano ranar Laraba, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan wannan mataki, yana mai cewa hakan cin mutunci ne ga al’ummar Kano da kuma ruhin haɗin kan ƙasa.
Gwamnan ya ce, “A ƙarshen jawabina, ina kira ga dukkan hukumomin tsaro da su ci gaba da sadaukar da kansu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihohin ƙasar nan, ciki har da Kano. Amma musamman hukumomin tsaro a Kano, bai kamata su tsoma kansu cikin siyasar bangaranci ba, domin hakan ba zai amfani kowa ba a Kano da ma Najeriya ba.
“Ina so in yi amfani da wannan dama a matsayina na ɗan Najeriya, ɗan Kano, kuma Babban jami’in tsaron Jihar Kano, in yi alla-wadai da halin rashin ƙwarewa da nuna bangaranci da Kwamishinan ’Yan Sanda na yanzu ke nunawa,” in ji gwamnan.
Gwamna Yusuf ya ce rashin halartar Kwamishinan da jami’ansa a bikin wani mataki ne da aka yi da gangan, kuma ya ce hakan ya jawo wa jihar kunya a rana mai tarihi.
“Kamar yadda kuke gani, a wannan rana ta tarihi ta bikin ’yancin kai na Najeriya, ya yanke shawarar ya janye daga jerin faretin tare da jami’ansa. Wannan mataki ne da ya shafe shi da mutanensa. A matsayina na Babban Jami’in Tsaro na Kano, a madadin gwamnati, ba mu ji dadin wannan hali da Kwamishinan ’Yan Sanda ya nuna ba,” in ji shi.
Gwamnan ya jaddada cewa Kano na cikin zaman lafiya, kuma al’ummar jihar sun dade suna jiran wannan rana don su taru su yi murnar ’yancin ƙasa tare.
Ya kuma ce matakin na Kwamishinan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana halin Kwamishinan da kalmomin “rashin ƙwarewa,” “rashin da’a,” da “rashin yin biyayya ga kasa.”
A ƙarshe, yayin da yake godewa sauran hukumomin tsaro da suka halarta, Gwamna Yusuf ya tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a Kano da Najeriya baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamishan Yan Sanda hukumomin tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji
Da yake magana da manema labarai, Ahmed ya ce ficewar ba za ta raunana jam’iyyar ba, amma dai, ya yi fatan alheri ga ‘yan jam’iyyar da suka fice.
Ahmed ya ƙara da cewa, NNPP tana da ƙwarin gwiwar riƙe Kano da kuma lasheh kujera a Jigawa, Kaduna, da sauran jihohi. Ya kuma yi ikirarin cewa, an ƙwace nasarar da jam’iyyar ta samu ne a Taraba a zaben da ya gabata wanda ke nuna yiwuwar samun nasara a shekarar 2027.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA