Sojoji sun kama ’yan sandan bogi da motoci 2 makare da tabar wiwi a Taraba
Published: 1st, October 2025 GMT
Dakarun sojin Najeriya sun kama wasu mutum biyu da ke sanye da kayan ’yan sanda dauke da motoci biyu kirar Hilux da ke makare da tabar wiwi a jihar Taraba.
Dakarun rundunar sojojin ta shida tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ne suka sami nasarar cafke mutanen bayan samun sahihin bayanan sirri.
An cafke su ne a tashar Takum da ke karamar hukumar Wukari, suna sanye da kayan jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma.
An gano cewa motocin biyu kirar Toyota Hilux da ake tuhuma cike suke da kayan da ake zargin tabar wiwi ce.
Mai rikon mukamin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar soji ta 6 da ke Jalingo, Laftanar Umar Mohammed, ya ce binciken farko ya nuna cewa babu wanda ke cikin motar da ke aiki da rundunar ’yan sanda.
Ya ce an gano cewa motocin sun fito ne daga Akure a jihar Ondo, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Adamawa.
Laftanar Umar ya kara da cewa daya daga cikin wadanda aka kama an gano sunansa da Monday George, tsohon ASP da aka sallama daga aikin dan sanda mai shekaru 71, yayin da dayan kuma sunansa Ezeugo Destiny Uche, mai shekaru 41.
Sai dai mutanen da ke cikin motar Hilux ta biyu sun tsere bayan ganin dakarun sojoji.
“Jimillar buhunan wiwi guda 1,134 aka gano a cikin motoci biyun. An mika wadanda ake zargin da kuma kayan da aka kwato zuwa ofishin NDLEA da ke Wukari domin ci gaba da bincike da gurfanarwa,” in ji shi.
Mai magana da yawun rundunar sojojin ya ce Kwamandan rundunar ta shida, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa dakarun da jami’an NDLEA bisa hadin kai da jajircewa, tare da jaddada kudurin rundunar na tabbatar da cewa jihar Taraba ba za ta zama mafaka ga masu laifi da masu safarar miyagun kwayoyi ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan sandan bogi Tabar wiwi Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso
Sarki Sanusi II, ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da farin ciki kan yawan mata da suka kammala karatu, yana fatan hakan zai ƙara yawan rawar da mata ke takawa a mulki da sauran ɓangarorin rayuwa.
Tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar, ya bayyana cewa cikin ɗalibai 180 da suka kammala karatun 24 sun samu sakamako daraja ta ɗaya (First Class), tare da bayyana cewa wannan bikin yaye ɗaliban shi ne karo na farko da jami’ar ta raba digiri na biyu tun bayan amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), da ta samu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA