2025-11-02@19:51:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 197

«lalacewar hanyar»:

    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI). Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya ziyarci AEOI a ranar Asabar da yamma, inda ya gana da wasu manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliyar. A yayin taron, Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Abin takaici, farfagandar son zuciya ta sanya ra’ayin “Makamashin nukiliya” ya zama daidai da samar da makaman nukiliya. Ya ce, “Samar da bama-bamai na nukiliya ƙaramin ɓangare ne kawai na sakamakon da ba su dace ba da...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma. Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade. Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su. Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban. A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya...
    Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba. Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi. Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin...
    Rahotanni sun bayyana cewa cewa kasar Pakistan ta bayyana cewa za ta dauki mataken da suka dace wajen kare tsaron alummarta da kasarta bayan kawo karshen yajejeniyar dakatar da bude wata ta kwanaki 4 tsakaninsu da kasar Afghanistan  ba tare da wani ci gaba da aka samu ba, Yarjejeniyar ta waste ne kwana daya kafin cikarta bayan wani mummunan fada da aka tsakanin kasashen biyu da ya jawo dama suka mutu ciki har da fararen hula, Pakistan na zargin Afghanisatan da boye kungiyoyin yan ta’adda dake kai hare-haren ketare iyaka, sai da Kabul ta musanta wannan zargin kuma ta dage akan ikonta, A karshen mako ne minsitan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya yi barazanar barkewar yaki tsakani, idan dai mataken...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
    Wannan shi ne daya daga cikin martanin NASENI da abokan huldarta don samar da CNG, wannan kuma na daga shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daƙile tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da iskar gas mai rahusa. Manufar ita ce a rage dogaro da na’urorin lantarki da ake shigowa da su daga waje, da inganta dogaro da kai a ɓangaren fasaha, da samar da ayyukan yi. NASENI tana ba da ababen more rayuwa da tallafin manufofin, yayin da ɓangaren da ke kula da masana’antu, yana mai da hankali kan haɗin gwiwa, ƙirƙira da kasuwanci don kafa Nijeriya a matsayin cibiyar fasahar Afirka. Wannan dabarar da NASENI ta yi ya tabbatar da cewa ba a bar kasar a baya...
    Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
    Ba wai nasara kawai ba ce; saƙo ne, cewa masu horarwa na Nijeriya na iya kai wa matakan duniya, kuma ƙwarewar gida har yanzu tana da muhimmanci. Hanyar Da Ba A Yawanta Binta Labarin Madugu ba na nasara cikin dare ɗaya ba ne, yana yi ne sannu a hankali da ƙwarewa mai ɗorewa. Daga farkon ayyukansa na horarwa ya fara da Adamawa United da ƙungiyar mini-football ta Nijeriya, zuwa aiki a matsayin mataimakin mai horarwa a gasar WAFCON huɗu (2012, 2014, 2018, 2022), ya gina suna saboda natsuwa, sassaucin dabaru, da basira. Lokacin da ya karɓi cikakken jagorancin Super Falcons a shekarar 2024, da yawa sun yi shakku kan iya cika takardun zama wasu ƙwararrun masu horarwar na ƙetare da...
    A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
    A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce sauran kasashe a wasu muhimman fasahohin zamani. Sa’an nan, dangane da takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba mata, kasar Sin ta yi kokarin inganta karfin jure wahalhalu da tabbatar da kiyaye bangaren masana’antu da samar da kayayyaki, tare da rage tasirin matsalolin da kan taso daga waje yadda ya kamata. Wadannan ingantattun hanyoyin mayar da martani ga matsin lamba daga ketare sun nuna...
    Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi.   Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa.   Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. ShareTweetSendShare...
    Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
    Ana fargabar cewa aƙalla mutum 30 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wata tankar man fetur a ƙauyen Essa da ke hanyar Agaei zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa, akwai kuma kimanin mutum 40 da suka jikkata wadanda suka wawason kwalfar man fetur bayan kifewar tankar. Bayanai sun ce da misalin karfe 11 na safiyar wannan Talatar ce tankar ta kife a titin Essan da aka bayyana cewa lalacewar hanyar ce ta haddasa hatsarin.  
    Zakaran kyautar Ballon d’Or ta bana, Ousmane Dembele, ya shiga cikin sahun ’yan wasan ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da za ta kece raini da Bayer Leverkusen a gasar Champions League, bayan ya shafe makonni shida a jinya. Dembele, wanda ya samu rauni a cinya yayin da yake wakiltar ƙasar Faransa a farkon watan Satumba, ya shafe makonni yana jinya a cibiyar lafiya ta musamman da ke Qatar, kafin komarwarsa atisaye a makon da ya gabata. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, kociyan PSG, Luis Enrique, zai yi farin ciki da dawowar Dembele, la’akari da yadda...
    An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
    Bayan juyin mulkin da aka yiwa Andry Rajolina a kasar Madagaska kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan jingine kasar daga zama mama a cikinta har zuwa abinda hali yayi. \ Tashar talabijin ta Almayadin ta nakalto majiyar kungiyar AU na bada wannan sanarwan, kwana guda bayan da sojoji suka yi juyin mulki wa shugaba Andria  Rajolina juyin mulki a tsibirin Madagaska. Sabon shugaban kasar Madagaska Micheil Rondri Yorinina ya bayyana cewa zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar zuwa lokacinda kasar zata koma cikin hayyacinta. Sannan a san abinda za’a yi. Mutanen kasar Madagaska dai sun dade suna zanga-zangar bukatar Rajolina ya sauka tunda ya kasa kyautata rayuwar mutanen kasar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
      A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata.   Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa  October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025 Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude...
      A halin yanzu, sama da mata da yarinya miliyan 600 a duniya suna cikin rikici da yaki, sannan mata da ‘yan mata biliyan 2 ba su da tabbacin tsaron zamantakewa. Kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana, cewar har yanzu ci gaban mata a duniya yana fuskantar “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba”, kasashe suna bukatar kuduri da hikima don magance matsalolin mata. A lokacin kaka na shekara ta 2025, daga Beijing za a sake samun ci gaba, wato Sin tana fatan ta kara hada kai da sauran bangarori, don hanzarta cikakken ci gaban mata, da kuma ba da gudummawar mata don ciyar da ci gaban bil’adama gaba. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
      Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.   Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su...
    A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.   Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin...
    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka. A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari. Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Ya ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa. Atiku,...
      Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025 Tsaro Bayan Sulhu  Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina September 22, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025
    Ya kuma sanar da cewa an saka wa cibiyar sunan marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, domin girmama jajircewarsa da hangen nesansa a shugabanci.Gwamnan ya ƙara da cewa Bauchi na da ɗimbin albarkatun ƙasa, kuma gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don inganta yanayin kasuwanci domin jawo hankalin ‘yan kasuwa daga cikin gida da wajen ƙasa.Taron, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya samu halartar gwamnonin jihohi, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, jakadu, sarakuna, da masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya. Ga hotunan:ShareTweetSendShareMASU ALAKA HotunaHOTUNA: An Tsaurara Tsaro A Gidan Buhari Da Ke Daura July 15, 2025HotunaHOTUNA: Yadda Bikin Al’adun Gargajiya A Masarautar Kaltungo Ya Gudana December 28, 2024HotunaHOTUNA: Yadda Abba Ya Raba...
    Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza. A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki. Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka...
    Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.” Tags: Aliko DangoteShettima ShareTweetSendShare Abubakar Sulaiman Related Manyan Labarai Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5 4 hours ago Manyan Labarai Uba Sani Ya Amince...
    Kungiyar Jihadul-Islami ta jaddada cewa: Za ta ci gaba da kare kasarsu da kuma neman kai wa ga dukkan hakkokin al’ummarsu Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta tabbatar a yau Litinin din nan cewa: Za ta ci gaba da daukar alkawarin kare al’ummarsu da wurarensu masu tsarki har sai sun kai ga samun ‘yancin kwato kasarsu, tare da cikakken hadin gwiwa da dukkanin dakarun gwagwarmayar Falastinawa karkashin jagorancin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana cika shekaru 38 da gudanar da jihadi da kuma cika shekaru biyu da harin daukan fansa na “Ambaliyar Al-Aqsa”, kungiyar ta ce: Shekaru 38 da kaddamar da Harkar Jihadin Musulunci ta Falastinu ta zo daidai da cikar shekaru biyu na...
    Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya  sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun. An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya  zube a kan titin Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagamu a  daidai  wurin musayar hanyar. Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Kakakin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce lamarin ya janyo tashin gobara. Ya kuma ɗaura laifin haɗarin a kan gudun wuce ƙima...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki....
    Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
      Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata.   Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin.   Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula...
    Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito. Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan. Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a ranar 28 ga watan Agusta, inda ta ce ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile. Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa. Farfesa Abbas Sharaky na jami’ar Cairo, masani a fannin ƙasa da albarkatun ruwa, ya bayyana cewa ƙaruwar matakin ruwa a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi. “Mun ɗauki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun. Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba. Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin...
    Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki. Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama. A cewarta:...
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
    Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna, da tabarmi, da gidajen sauro, da magungunan zazzabin cizon sauro. A cewar ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai, kimanin mutane 273,000 ne ambaliyar ta shafa a gundumomi 12 na jihohin Jonglei da Unity da Upper Nile da Central Equatoria, inda jihohin Jonglei da Unity suka dauki sama da kaso 91 na jimilar mutanen da ambaliyar ta shafa. Martha Remijo Rial, daraktan kula da...
    Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta. Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe “Matar ce ta kwara wa Fatima man girki mai zafi a fuska, wanda ya janyo mata mummunan ƙuna,” in ji majiyar. An bayyana cewa Fatima na tare da mahaifinta a lokacin da suke shirye-shiryen aurenta da ake sa ran yi a nan...
    Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.   A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su.   Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.” Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
    Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta. A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu saboda lalacewar hanyar, abin da ke jawo gajiya da takaici ga fasinjoji da masu tuƙi. An fara gina hanyar Gombe-Dukku-Darazo ne tun a shekarun 1980, aka gyara ta a farkon shekarun 2000. Sai dai daga baya aka yi sakaci da ita duk da kasancewarta hanyar da matafiya daga jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Bauchi da wasu ke bi. “Gyaran motoci na cinye mana kuɗi”...
    “Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa. Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba da su. Limamin da ya jagoranci sallar jana’izar gawar da aka samu a kwarin Dangoma, Mallam Musa Umar Al mishawi ya bayyana cewa; marigayin ya samu rauni a goshinsa. “Marigayin, mazaunin Unguwar Gidan Dangoma ne da ke tudun jukun ta garin Zaria, sannan kuma an yi jana’izarsa kamar yadda a safiyar yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji shi.   Kazalika, har zuwa lokacin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta Duniya IAEA ta amince da sabuwar yarjeniya tsakaninta da Iran ta yadda ma’amala tsakanin bangarorin biyu zata kasance. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Laraba a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia. A lokacinda yake jawabin hadin guiwa ta tokwaransa na kasar ta Tunisia. Kafin haka dai Aragchi ya yada zango a birnin Alkahira na kasar Masar inda ya gana da Rafael Grossi shugaban hukumar IAEA, suka kuma rattaba hannu kan sabuwar yarjeniya da hukumar, ta yadda hulda tsakaninsu zata kasance bayan hare-haren da HKI da Amurka suka kai wa cibiyoyin sarrafa makamashin nukliya na kasar ta...
    A yayin taron rattaba hannun, Farfesa Gwarzo ya bayyana manufar wannan yarjejeniya, inda ya ce hadin gwiwar za ta bai wa dalibai da ma’aikata damar cin moriyar albarkatu da kwarewa daga kasashen waje.   “Wannan hadin gwiwar alama ce ta jajircewarmu wajen hada jami’o’inmu da manyan cibiyoyi na duniya domin bunkasa kirkire-kirkire da bincike a rukunin jami’o’inmu na MAAUN,” in ji shi.   A karkashin wannan yarjejeniyar, cibiyoyin biyu za su rika raba kwarewar su tare da tallafa wa juna don cimma manufofi na bai daya. Muhimman bangarorin hadin gwiwar sun hada da samar da koyarwar harshen Turanci ta yanar gizo ga daliban MAAUN, samar da hanyoyi don ci gaba da karatu a Seneca, da bayar da shawarwari kan harkokin...
    A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da kungiyar SCO ta taka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasa da yin imani da juna da kuma hadin gwiwa a yankin, kana ya yaba wa kungiyar SCO bisa kokarin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da tsarin MDD. Mukaddashin shugaban tawagar dindindin ta Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana yayin da yake bayani game...
    Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
    Watanni biyu da rabi da yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran tare da fadin Donal Trump kan cewa sojojinsa sun lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, amma har yanzun ba’a san halinda cibiyoyin nukliyar kasar suke ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar IAEA tana iya kokarinta don sanin halin da cibiyoyin nukliyar kasar Iran suke don bawa Amurka da HKI damar sanin yadda zasu kaiwa Iran hare-hare a yakin da za’a fafata da su nan gaba. Gwamnatin JMI tana zargin hukumar IAEA da kasancewa yar leken asiri Amurka da HKI a cibiyoyin Nukliyar kasar Iran, don basu damar `lalatasu a yaki na gaba. Bayan yakin kwanaki 12 a cikin watan...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne ta dauki matakai na zahiri, na musamman, da kuma a bayyane kan hanyoyi guda biyu masu kamanceceniya da juna, don samar da duniya mai zaman lafiya, da duniya mai shirin fadada hadin gwiwar tattalin arziki. A yayin taron kolin shugabannin kungiyar hadin gwiwar Shaghai “SCO” karo na 25 a birnin Tianjin na kasar China, shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tsarin karfafa hadin...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...
    Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar. Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi. Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa A cewarsa, Ado ya aikata wannan aika-aika ne tare da wasu masu laifin a ranar Talata. Waɗanda suka haɗa da: Musa Kwalle da Dan Abba da Sule Musa da wani Arrow dukkansu daga ƙauyen Gerawa. Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Agusta da misalin ƙarfe...
    Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta kan rushe kasuwar Alaba Rago mai ɗimbin tarihi a Legas, inda ta bayyana hakan a matsayin babban koma baya ga dubban ’yan kasuwa. A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, ɓarnata kasuwanci da dukiyoyi ya jefa wasu iyalai da dama cikin ƙunci. Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rushe kasuwar mai ɗimbin tarihi ya haifar da asarar kasuwanci da dukiyoyi, tare da kawo cikas ga hanyoyin rayuwar jama’a...
    A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing.   Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar Sarki Sihamoni bikin da za a yi na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban sakataren kungiya Hizbullahi ta kasar Lebanon ya karbi bakwancin Ali Larijani ya kuma godewa Iran bisa goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da ‘yan gwagwarmaya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da tawagarsa a gaban jakadan Iran a Lebanon Mojtaba Amani. A yayin taron, Sheik Qassem ya jaddada godiyarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa ci gaba da goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da kuma ‘yan gwagwarmaya da yakin da suke yi da makiya yahudawan sahayoniyyar Isra’ila da kuma goyon bayan da take baiwa hadin kai da ‘yancin kai na Lebanon da kuma ci gaba...
    Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule ya yaba wa jami’an gidan yari da sauran jami’an tsaro saboda sake kama wasu daga cikin waɗanda suka tsere. Ya kuma roƙi jama’a da su kasance cikin shiri su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani mai kama da wanda ake nema. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Muryoyi daga ko’ina cikin duniya sun nemi a warware matsalar bisa turbar adalci. Shugabannin tarayyar Turai sun yi ta kira ga kasashen Sin da Amurka da su kiyaye bude kasuwanni da gudanar da gasa ta gaskiya. Kasashen kudu maso gabashin Asiya, sun ba da shawarar tabbatar da kwanciyar hankali. Kasashen Afirka da na Latin Amurka sun nuna damuwa da halin da ake ciki saboda barazanar da lamarin yake yi ga damarmakin zuba jari da kasuwancin kasashensu. Gyaruwar dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka za ta iya haifar da wani sabon zamani na hadin gwiwa, da kirkire-kirkire, da ci gaban da ya kunshi kasashen duniya baki daya. A wannan duniyar tamu wadda bukatar hada hannu da juna ke kara bayyana,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. EFCC ta saki Tambuwal Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar. Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar. A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba. Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi? NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya Ta bayyana cewa sun samu tushen faruwar lamarin ne bayan da wani Mista Innocent, ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekaru 16 a ranar 18 ga Yuli, 2025. Mista Innocent ya shaida wa ’yan sandan cewa ’yar tasa ba ta dawo gida ba tun bayan da ta fita domin...
    An nemi wata jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin. Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da...
    An nemi wata jaririya saoi kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin. Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da...
    Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na da nufin inganta lafiyar mata da yara tare da rage mace-macen da za a iya kauce wa ta hanyar samar da dama ga ayyukan kiwon lafiya. Cibiyoyin lafiya a fadin karamar hukumar, ciki har da Asibitin Gwamnati na Gwarzo da Asibitin ‘Yar Kasuwa, sun bayar da rigakafi kyauta, shawarwari kan abinci mai gina jiki, kulawar haihuwa da sauran muhimman ayyuka na kiwon lafiya. Jami’in...
    “daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba. Ya bayyana cewa gwamnati na binciken gyare-gyare da nufin ƙara bayyana gaskiya, ciki har da yiwuwar gudanar da cinikin danyen mai daga ƙasashen waje da na naira. “Yawancin mu’amalar kasuwancinmu ana gudanar da su ne a waje da tashoshi na yau da kullun. Muna aiki kan gyare-gyaren da za su inganta tsarin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi.   A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da lamarin ya shafa. Makabartar Jajeri Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a Maiduguri, ta ce rundunar ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da abin ya shafa.   Ya kuma tabbatar da cewa, “Abin takaici, gine-gine takwas...
    Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin ayyukan raya kasar da take yi a yankin. Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kasa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Talata, Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), ya yi zargin cewa ana nuna wa yankin bambanci a muhimman manufofin gwamnati da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa. ACF ta ce hakan na faruwa ne duk da irin irin tarin gudunmawar da yankin ya ba gwamnatin mai ci a zaben 2023 da ya gabata. DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Remi Tinubu ta...
    Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu. Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo. Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa. Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.   RN  
    ‎Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa. Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara. ‎Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa. Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna...
      Manoma a Jihar Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da yadda iri na TELA Hybrid Maize daga kamfanin EcoBasic Seeds ke samar da amfanin gona ba tare da amfani da maganin kwari ba.   Sun bayyana hakan ne a Jaji, Jihar Kaduna, lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara gonakin gwaji da kamfanin EcoBasic Seeds ya kafa.   Wani daga cikin manoman, Mallam Sabitu Abdullahi, ya bayyana Irin Masara na TELA Hybrid a matsayin masara mai ban mamaki, yana cewa tana bada amfanin gona mai yawa da kuma girbi cikin kwanaki 70 kacal.   “Idan duka manoman Najeriya suka rungumi wannan iri, zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci a kasa,” inji shi.   Ya ce ya shafe shekaru uku yana...
    A wani roko da wata kungiya da aka fi sani da Sokoto Heritage Reloaded Initiative ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alkawarin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar.   An yi wannan roko ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a jihar Sokoto, inda shugaban kungiyar Farfesa Uthman Abdulqadir, ya jaddada muhimmancin girmama abubuwan da Shagari ya bari.   Ya tuna cewa shugaba Buhari ya yi wannan alkawari ne a ziyarar da ya kai Sokoto.   Farfesa Uthman ya bayyana irin rawar da Shehu Shagari yake takawa wajen ciyar da ilimi gaba a Najeriya, inda ya bayyana cewa ya...
    Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.   Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.   A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan...
    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya sanar da dakatar da bayar da tallafin abinci a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka da ke fama da rikici. Hakan dai na zuwa ne a sakamakon rage tallafin da Amurka ke bayarwa na kuɗi ƙarƙashin Hukumar USAID, wanda hakan ke kawo cikas ga ayyukan wannan ƙungiyar. Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci An sanya dokar hana fita a Adamawa Duk da cewa lokaci ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, ana hasashen kayan abinci za su isa zuwa kusan watan Satumba a mafi yawan ƙasashen da abin ya shafa, wanda hakan zai bar miliyoyin mutane masu rauni cikin halin rashin tallafin gaggawa, a cewar WFP. “Muna...
    Albarkacin taron ministocin kasa da kasa na tattauna mu’ammalar wayewar kai ta duniya, CGTN ta hada hannu da jami’ar Renmin ta kasar Sin, domin jin ra’ayin al’ummun kasashe 41 da yawansu ya kai dubu 12. Masu bayyana ra’ayoyin na ganin cewa, mu’ammala, da cudanyar al’adu, da wayewar kai muhimmin karfi ne na ciyar da bunkasar wayewar kan daukacin bil’adama da zaman lafiyar duniya gaba, don haka ne ma darajanta al’adu da magabata suke dora muhimmanci a kanmu, da kirkire-kirkire, na da babbar ma’ana ga zamanantar da al’ummun bil’adama, wanda hakan ya sa shawarar bunkasa al’adun duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta samu karbuwa tsakanin sassan kasashe daban-daban, yayin da suke kokarin tinkarar kalubaloli a duniya. Yayin da aka tabo...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
    Babban sakataren kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya godewa shugabancin JMI, wato Imam Sayyif Aliyul Khaminaei kan goyon bayan da yake bawa kungiyar babu kakkautawa don yakar makiyar kasar HKI. Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon, a karon farko tun bayan shahadr shugaban kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah a shekarar da ta gabata. Babban malamin ya kara da cewa, taimakon da Imam Khaminae yayiwa kungiyar Hizbullah, ya kai matsayinda ba zamu tambaya, ko roka ba. Musamman bayan fara yaki a cikin watan Octoban shekara ta 2023, kuma ta bada wadannan taimakon ba tare da ta shiga yakin kai tsaye ba. Sheikh Qasem ya bayyana cewa, bamu...
    Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin...
    Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.” Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban hukumar tsaron ta fararen hula janar Jalali ya bayyana cewa; saboda aiki da ka’idojin tsaro sun yi nasarar hana fitowar sanadarorin Nukiliya da za su iya cuta da mutane.  Kamfanin dillancin labaru na “Mehr” ya nakalto janar Jalali yana cewa; Amurka ta kai hare-hare akan muhimman cibiyoyinmu da suke dauka cewa yana da girma da tsanani, sai dai mun dauki matakai na kariya da su ka hana fitowar sanadarori na Nukiliya da za su iya zama masu hatsari da cutarwa ga mutane. Janar Jalali ya ce, tun a lokaci mai tsawo ne aka dauki wadannan matakan saboda kaucewa bacin rana.
    Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci a sake komawa teburin tattauna shirin nukiliyar Iran cikin gaggawa, inda take neman hadin kai a tsakanin Tehran da kuma Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya IAEA. Babbar jami’ar diflomasiyyar EU Kaja Kallas ta shaida wa Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Iran, Abbas Aragchi cewar Brussels a shirye take ta shige gaba don ganin an koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran bayan hare-haren Amurka a tashoshin makamashinsu. HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza Bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarho da jami’ar ta yi da Mista Argchi, ta wallafa a shafinta na X cewar ya kamata a koma tattaunawa...
    Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
    Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta Lebanon ya fadawa Jaridar da The National ta kasar Amurka kan cewa a makon da ya gabata an kama wani shugaban yan kungiyar yan ta’adda ta ISIS a cikin kasar, tare da zarginsa da shiri hare-hare masu yawa a kasar Lebanon. Kafin haka dai a cikin watan da ya gabata wani dan ta’ada ya tarwatsa kansa a cikin wani coci a birnin Damascus babban birnin...
    A yanzu haka, fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI na sauya zaman rayuwar dan Adam. Ga misalin, motoci mara matuki na saukaka tafiye-tafiye na dan Adam, samfurin binciken yanayi na iya hasashen hanyar guguwa a cikin dakika 10 kawai… Amma, fasaha ta zama kamar “takobi mai kaifi biyu”, wadda a lokaci daya take kuma kara haifar da matsaloli, kamar su fallasar sirri, yaudara ta hanyar amfani da AI, da hadarin rashin aikin yi. Bisa wannan yanayin da ake ciki na kasancewar alfanu‌ da ‌matsaloli tare, ‌’dan Adam na bukatar hadin gwiwa cikin gaggawa don daidaita ci gaban fasahar AI, da kafa tsarin gudanar da harkokin fasahar AI na duniya, da nemo daidaito tsakanin kirkire-kirkire da tsaro, da nufin tabbatar...
    A ranar 23 ga wata, Kirsty Coventry, wacce ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics ta kasa da kasa kwanan nan, ta yi hira ta musamman da wani shirin gidan talabijin na CCTV mai lakabin “High-End Interview” a birnin Lausanne na kasar Switzerland. Wannan ita ce hira ta farko da ta yi da kafar yada labarai tun bayan da ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics na duniya. Coventry ta ce ya zama wajibi a kiyaye kima da kuzarin wasannin motsa jiki na Olympics, tare da kara kiyaye su da kuma karfafa su. Ta ce, tana fatan yin mu’amala mai zurfi da dukkan masu ruwa da tsaki a watanni masu zuwa, tare da haduwa tare wajen tsara fasalin aiki na...
    Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ta gudanar da bikin murnar cika shekaru biyar da kafawa, da kaddamar da dokar tsaron kasa ta yankin. Yayin bikin da ya gudana a jiya Asabar, Xia Baolong, wanda shi ne shugaban ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a kwamitin kolin JKS, da ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya ce dokar tsaron kasa ta yankin Hong Kong da aka kaddamar a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2020, ta samarwa yankin damar fita daga hargitsi zuwa yanayi na daidaito, tare da shigar da yankin sabon zamani na gudanar da tsarin “kasa daya tsarin mulki biyu”. Xia Baolong, ya ce...
    A watan Afrilun bana, wata farar mota kirar bas mai tsawo mita 12, ta yi tafiya a kan titunan Ashgabat, hedkwatar kasar Turkmenistan. Bas din da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera ta dace da ma’aunin kiyaye muhalli da kasar ta tanada, kuma tana dauke da na’urar ba da jagorancin sufuri mai amfani da tauraron dan Adam, da na’urar biyan kudi ta yanar gizo, matakin da ya bullo da sabuwar hanyar zirga-zirga ga jama’ar wurin. A wannan shekara, Sin za ta samar da irin wannan bas har 700 ga Ashgabat, matakin da zai biya bukatun zirga-zirgar jama’ar kasar da yawansu ya zarce miliyan 1. Tun da aka bude taron koli na Sin da kasashen shiyyar tsakiyar Asiya karon farko...
    An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada. Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare...
    Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da kumbo mai daukar mutane. Wannan ita ce nasara irinta ta biyu da Sin ta samu a wannan bangare, bayan shekaru 27 da suka gabata, da samun nasara ta farko a aikin gwajin da ta gudanar a shekarar 1998. Aikin gwajin tserewar da aka gudanar ya kasance muhimmin mataki na ba da tabbaci ga rayukan ’yan saman jannati, wato idan an gamu da hadari ko matsala...
    Yayin da taro na biyu na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya ke kara matsowa, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, sun nuna gamsuwa da hadin gwiwa bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da kasashen nan biyar na yankin tsakiyar Asiya, a matsayin wata hadaka ta al’umma mai kyakkyawar makomar bil’Adama, wadda ke kara shigar da sabon kuzari, na daidaito cikin yanayin duniya dake kara shiga yanayin tangal-tangal. Tun dai taro na farko na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen biyar ya shiga wani sabon zango na ci gaba. Har ma kuri’un na jin ra’ayin jama’a suka nuna yadda kaso 90.4...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi karin haske game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta a Kazakhstan, yana mai cewa, Sin na da yakininta hanyar taro, ita da sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya biyar, za su zurfafa dunkulewa, da amincewa da juna, da gina matsaya guda ta fuskar hadin gwiwa, da zurfafa daidaiton dabarun ci gaba, da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da kara kuzarin gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya.   Bisa gayyatar da shugaban jamhuriyar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na...
    Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.   Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.   Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki.   “Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya.   “Martabar...
    Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da ke kawo karshen zaman tankiyar da aka soma tsakanin kasashen biyu tun bayan hawan Donald Trump karagar mulki. Kasashen biyu sun cimma matsaya a kan kan cinikin wani rukini na ma’adinai da Chinar ke fitarwa, wadanda ake kira da sunan Terres Rares, wadanda ake yi amfani da shi wajen samar da lantarki da kuma makamashin da ake sabbintawa. An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m A baya a taron kasar Switzerland, Washington ta amince da rage haraji kan kayayyakin kasar China daga kashi 145 zuwa kashi 30 cikin 100, don musanya makamancin wannan mataki da Beijing ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp