2025-09-24@13:56:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 20
«da labaran karya»:
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya gargadi masu yada labaran karya musamman a kafafen sada zumunta da su daina, domin Musulunci ya haramta hakan. Ya bayyana cewa a Musulunci, yada labaran karya daidai yake da yin karya, kuma addinin Musulunci yana tsananin kin masu karya. UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi Sheikh Khalil ya fadi hakan ne a Kano a ranar Talata yayin wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa malamai da limamai kan yadda za a yaki labaran karya da kuma inganta fahimtar kafofin yada labarai, wanda kungiyar Alkalanci ta shirya, wata kungiya da ke tantance...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa. Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta da ke Jega a Jihar Kebbi. Ya ce, “Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse...
Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Nijeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki. Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki,...
Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa. Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa da ya dada aiwatar da matakan da za su kara karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya. Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da cewa an rage farashin sufurin kayan amfanin gona ba tare da kashe makudan kudade ba. “Shugaban Kasa ya bayar da umarni ga Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa wanda dama yanzu haka yana nan yana kokarin ganin an saukaka hanyoyin sufurin amfanin gona a fadin kasar nan, da su dada...
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin tsaro ya zama babban abin damuwa, ƴan fashi, tada ƙayar baya, da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da wanzuwa a sassan Arewa da dama, inda jihohi kaɗan ne kamar Kaduna da Bauchi suka samu kwanciyar hankali,” in ji shi. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da manufofin siyasa don kawo ƙarshen rikicin. ɗalhatu ya kuma soki manufofin gwamnatin tarayya kan...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA. Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar. Makarantar Yusuf Dantsoho, wacce aka kafa a shekarar 1920, tana tsakiyar Unguwar Rimi GRA, kuma ta samar da fitattun ‘yan Najeriya da dama da suka yi aiki a matakai daban-daban na gwamnati da kuma masu zaman kansu. Alhaji Maman Lagos ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar sayar da wata cibiyar gwamnati, kama daga makarantu zuwa asibitoci. Yace maimakon haka,...
Gwamantin kasar Mauritaniya ta musanta cewa shugabanta ya gana da Netanyahu, ta yi kira ga tashar Al Arabiya da ta tabbatar da sahihancin rahoton kafin watsa shi Ministan al’adu da sadarwa na Mauritaniya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Hussein Ould Maddou ya musanta sahihancin rahotannin ganawar da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya da Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Kamfanin dillancin labaran Jamus ya nakalto ministan na cewa rahoton da tashar Al Arabiya ta watsa game da ganawar da ake zargin shugaba Mohamed Ould Ghazouani da Fira ministan Igwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba shi da tushe balle makama. Ya yi nuni da cewa, labaran ba su da inganci, inda ya yi kira ga tashar Al-Arabiya da ta...
Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe. Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da aka ga gwamnan yana magana da manema labarai kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin tsaro da kuma jin dadin wadanda matsalar tsaro ta shafa. A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin rashin gaskiya da yaudara. Malam Idris Yusuf Gusau ya yi zargin cewa, gwamnatin ta gaza cika wasu...
Shugaban Runkunin Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirinsa na karya farashin shinkafa a Najeriya, yana mai cewa nan gaba kadan wadanda suka saye shinkafar suka boye suna jiya ta yi tsada, za su tafka mummunar asara. Dan kasuwar ya kuma bayyana cewa suna tattunawa da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan hanyoyin da za su bi domin ganin sun daidaita farashin siminti. BUA ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa. “Farashin kayan abinci na saukowa a Najeriya kuma muna yin duk abin da za mu iya na ganin cewa mun mara wa gwamnati baya a kan hakan,”...
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita. Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita. Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi. Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura...
A shekaru 70 da suka wuce, kasashen yamma sun yi wa taron Bandung kallon taro na kasashe matalauta, amma kuma ga irin yadda ya haifar da kyakkyawan sakamako ga mikewar kasashen. A zamanin yau, lokacin da kasar Amurka ke ta kara kakaba harajin kwastam a kan sauran kasashen duniya, muna farin cikin ganin yadda kasashe masu tasowa ke hada kansu, da rike tsaronsu da ci gabansu a hannunsu, suna kuma rungumar akidun zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa don tinkarar yadda kasashe masu karfi ke neman cin zalin kasashe masu karamin karfi da ma rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Yau da muke waiwayen taron Bandung, za mu gano cewa, ko-ba-dade-ko-ba-jima za mu ga bayan nuna...
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata. Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya Hakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasuwannin hatsi a Jihar Neja suna fama da matsalar faduwar farashi amfanin gona, sakamakon shigo da hatsi daga kasashen makwabta kamar Chadi da Ghana da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso. Wannan yanayi ya haifar da yawan kaya, wanda ke shafar manoma da ‘yan kasuwa da masu samar da kayayyaki a yankin. Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi Manoman da suka tara hatsi don cin riba sun shiga damuwa saboda shaguna da kasuwanni sun cika da buhunhunan hatsi, amma babu masaya. Wasu daga cikin manoma da ’yan kasuwa sun bayyana wa wakilinmu cewa, wannan yanayi ya rikitar da harkar kasuwanci, inda suke fama da karancin riba saboda farashin...
Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man fetur daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita a yammacin wannan Asabar.
A kwanakin nan ne wani asibitin kula da dabbobi a kasar Turkiyya ya wallafa wani labari mai ratsa jiki na wata karya da ba ta da masauki ta ɗauki ɗanta da ya suma a bakinta ta ajiye shi a kofar asibitin kamar mai neman taimako. Idan ba don gajeran bidiyon da kyamarorin na’urar CCTV suka ɗauka ba, da alama yawancin mutane za su yi tunanin wannan labarin ba zai iya zama gaskiya ba. ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Wani asibitin dabbobi a Unguwar Adnan Kahveci da ke Beylikduzu, a lardin Istanbul na ƙasar Turkiyya, kwanan ya fitar da rahoton ɗaya daga cikin muhimman harkokin asibitin....
Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar. Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi, jihar Bauchi; Usman Umar Danburam, 35, daga Darazo, Jihar Bauchi; Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 50, daga Mina, Jihar Neja; Aminu Mohammed, 40; da Adamu Abdul’aziz mai shekaru 46 daga jihar Taraba, an kama su ne a ranar 17 ga watan Janairun 2025. An same su dauke da kayayyaki dama da kuma wasu duwatse ake zargin masu daraja ne a wani sansani hakar ma’adinai dake...