2025-09-24@08:35:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14
«faɗar albarkacin baki»:
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da hana su faɗar albarkacin baki. A cikin wata wasiƙar da suka aike wa shugaban ƙasa ranar 20 ga Satumba, 2025, SERAP da Amnesty sun bayyana cewa ƙarar da DSS ta shigar bisa zargin saƙonnin da ake cewa sun na adawa da Tinubu ya zama wani SLAPP (ƙarar da ake amfani da ita don toshe bakin masu suka). Sun ce irin waɗannan suna haifar da tsoro...
tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce hare-haren da aka kai kan masu gudanar da taro a jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi a matsayin abubuwan da ke da haɗarin “jefa Najeriya cikin tsarin kama-karya a karkashin gwamnatin Bola Tinubu.” A karshen makon da ya gabata ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari tare da tayar da tarzoma a wani wurin taron yayan jam’iyyar hadaka ta ADC a birnin Kaduna. Cikin mahalarta taron har da jiga-jigan jam’iyyar ta ADC, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma shugaban jam’iyyar na Arewa maso yamma. Daga baya, a jiya Alhamis rundunar yansandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta aika da takardar gayyata ga jam’iyyar ta...
Wasu mutum biyu da ake zargin ɗaliban jami’a ne a Jihar Bayelsa sun mutu bayan wata mota ƙirar tifa ta murƙushe su lokacin da suke kan babur mai ƙafa uku a kan hanyar Tombia zuwa Ammassoma. Daily Trust ta samu rahoton cewa haɗarin wanda ya afku a ranar Talata, ya kuma sa wasu fasinjojin da ke cikin babur ɗin sun samu munanan raunuka. Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun A cewar wasu mazauna yankin, haɗarin ya afku ne a kusa da wani lanƙwasa mai haɗarin gaske a kan babbar hanyar, sakamakon rashin kyan hanyar da kuma gudun wuce ƙima. Sun ce babbar motar...
A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari. Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa da kasuwar Ɗan Magaji saman gadar da ke kan hanyar Zariya zuwa Kaduna. Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Awaki kusan sama da 100 suka mutu da kuma kaji kusan ɗari 500 ne aka ƙeyasta sun mutu. Sai dai ba a sami asarar rai ko ɗaya...
Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani. A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa. Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga...
Kimanin mutum 16 sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka, babban birnin kasar. Haɗarin jirgin saman yaƙin ya kuma yi sanadin jikkatar gommai, wanda ya kasance guda daga cikin haɗɗura masu muni da ƙasar ta gani a baya-bayan nan a fannin jiragen sama. Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a Wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wurin ya ce ya ga jami’an kashe gobara suna kwasar daliban da suka jikkata yayin da sojoji ke taimakawa wajen zakulo mutane daga cikin baraguzan...
A ɗaya ɓangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; waxanda labarai a kansu babu daxin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, waxanda galibi labaransu marasa daxi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; waxannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma haxari duk da ke xauke cikin wannan labari. Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna fuskantar...
Wani haɗarin mota da ya faru a yau Lahadi a hanyar Lokoja-Obajana ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 8 suka jikkata. Sakataren FRSC na jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa haɗarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima. Mota bas da wata babbar mota sun yi karo da juna a Gada biyu, inda yara 5 suka ƙone har lahira. Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC Kashi 25 Kawai Na Motocin Da Ke Nijeriya Suke Da Inshora – FRSC “Mutane 27 ne haɗarin haɗarin ya rutsa da su, 8 kacal suka tsira,” in ji Tsukwam. An kai wadanda suka tsira asibitin Fisayo a Obajana don samun kulawa. FRSC ta yi...
Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna. Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda ya bayyana cewa al’ummar Kirista ta yi hasarar babban jarumi. “Evangelist Azzaman ya kasance mai himmar wa’azi, mai kare addinin Kirista, kuma mai fafutukar kare hakkin masu ƙaramin ƙarfi. Rayuwarsa ta kasance cikin jarumtaka da ƙwarin gwuiwa ga gaskiya da adalci,” in ji Hayab. CAN ta yi wa iyalansa, da ‘yan cocinsa, da duk wanda rayuwarsa ta shafa ta’aziyya, tare da addu’ar Allah ya ba...
A wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina, mutane tara sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata. Hatsarin dai ya shafi wata babbar motar bas da ke ɗauke da fasinjoji 20. Aliyu Ma’aji, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa gaggawar tuki ne ya haifar da hatsarin, inda direban ya rasa ikon sarrafa motar. An Gabatar Da Motar Asibiti Ta Farko Mai ISO Na Matsayin Kasa Da Kasa A Hukumance Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC Haɗarin ya yi sanadin mutuwar mutane...
Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa uku daga cikin matan da suka rasu ’yan gida ɗaya ne. Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB Sai dai wasu fasinjoji uku da suka haɗa da mata biyu da direban motar sun tsallake rijiya da baya, inda a yanzu suke samun kulawa a Babban Asibitin Lapai. Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne...
Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya. “Rufewar jami’ar ya biyo...
Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48. Mummunan haɗarin wanda ya faru a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, a Hotoro. Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano A cewar Hukumar FRSC, haɗarin ya rutsa da wata motar tirela ƙirar DAF ɗauke da kayayyaki da fasinjoji. Bincike na farko ya nuna cewa direban ya yi tuƙin ganganci saboda gudu wanda hakan ya sa motar ta kauce hanya ta afka ƙarƙashin gadar. Rahotanni sun...
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci a kan lamarin. Har ila yau, ya yi kira ga hukumar makarantar da ma Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), da su girke tudu-tudu na rage gudu a kusa da makarantar domin kaucewa irin hatsarin nan gaba.