2025-09-18@15:28:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2961

«Sabon Sara»:

    Hukumar bunkasa ilimin gaba da sakandare ta jihar Jigawa ta shirya taron tattaunawa ga jami’an gudanar da shirin koyawa dalibai musamman wadanda suke da nakasu a jarrabawar NECO ko WAEC wato Remedial program don su sami nasarar cin jarrabawar da za ta basu damar ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandare. Da yake...
    A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa...
    Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis. Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar. Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn —...
    A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a  Legas.   A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya...
    Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da...
    Juventus za ta yi kokarin daukar dan wasan tsakiyar Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31 a kyauta idan kwangilarsa da Manchester City ta kare a bazara mai zuwa. (Tuttosport) Ita ma Manchester City tana tunanin zawarcin dan wasan Manchester United Kobbie Mainoo, duk da cewa tana iya fuskantar gogayya daga Newcastle da kuma Chelsea kan...
    Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu. Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu...
    Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar.   Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido...
    Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Gumi kan mumunan al’amuran da suka salwantar da rayukan mazauna kauyen Fas su 19 a makonnin da suka gabata.   Malam Mumini ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da suka kai ziyarar jaje ga al’umma, inda...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024. “Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce...
    Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta ce ma’aikatanta hudu sun mutu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad da ke Legas, a ranar Talata. Aminiya ta rawaito yadda gobara ta mamaye ginin da ke dauke da banki, hukumomi da wasu kamfanoni. Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.   Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar...
    A ƙoƙarinta na  ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa. Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace...
    A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma. Mai kula da...
    Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF). A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa...
      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da...
    Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin...
    Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD. Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan...
    Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025. Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci. Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya...
    Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce...
    Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara...
    Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na...
    A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.   Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai...
    A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi. Kasar Sin ta...
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.  ...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu. A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed...
    “Bayan karbar mukaminsa na sabon kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, kwamared Bala Bodinga ya umurci jami’ansa da su sadaukar da kansu ga muhimmin aiki na tabbatar da amincin muhimman kadarori da ababen more rayuwa na kasa.   “Kwamandan jihar ya ba da umarnin cewa, ba dare ba rana, cikin sa’o’i 24, dole jami’an hukumar...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi...
    Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa  wannan...
    An fara taron hukumar IAEA ta kasa da kashe karo na  69TH  a jiya Litinin, inda a taron ne ake fayyana al-amura masu muhimmanci da ya shafi makamashin Nukliya a duniya, kuma tuni shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Eslami yakejagorantar tawagar Iran a taron. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya...
    Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin. Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe. Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan...
    Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne...
    Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.   Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana,...
    A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara. A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da...
    Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje. Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli....
    Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.” Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar. Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne  ya yi wannan kiran...
    Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin. Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da...