2025-11-04@18:38:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7544
«Najeriya da ke»:
Dan wasan gaban Paris Saint-Germain (PSG) ɗan asalin ƙasar Faransa, Ousmane Dembele, zai kasance cikin tawagar da za ta fafata da Bayern Munich a wasan Champions League da za a buga yau Talata. Dembele, wanda ya zura ƙwallo a wasan da PSG ta doke Bayern Munich da ci 2–0 a gasar Club World Cup zagaye na kwata-final a watan Yuli, bayan mako guda ya fice daga wasa sakamakon jin ciwo a cinyarsa ta dama a fafatawar da suka yi da Lorient. ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Kocin PSG, Luis Enrique, ya tabbatar da cewa dan wasan ya murmure daga raunin kuma zai iya buga...
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran...
Ya ce, “Wannan ba yana nufin ba a kashe Kiristoci ba ne.” Abin da muke faɗa shi ne, ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba – ana kashe Musulmai ma,” “Addinan biyu sun tabbatar da hakan, akwai kashe-kashen rayuka da yawa da ke faruwa a Nijeriya tsawon shekaru 16 da suka gabata da kuma fiye da haka daga rikicin Boko Haram a 2009. Babu wanda zai iya musanta hakan. “Amma a ce kawai ana kai wa Kiristoci hari ya dogara ne da inda abin ya faru. Idan ya faru a yankin da Kiristoci suka mamaye, a zahiri Kiristoci ne za su kasance waɗanda abin ya shafa kamar yadda yake a yanzu a Benuwe da Filato. “Idan ya faru...
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba. Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November...
Ƙasar China ta soki abin da ta kira yunƙurin Shugaban Amurka Donald Trump na yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a matsayin martani kan barazanar Shugaba Trump ta tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yaƙi da abin da ya kira kisan kiyashi ga Kiristoci. Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Trump, wanda ya yi ikirarin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya, ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da yin biris da zarge-zargen, yana...
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE Daga Abdullahi Shettima. Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara kanana (RUTF) wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yakar karancin abinci mai gina jiki tsakanin yara. Da take jawabi yayin wani taron hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da...
Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Dick Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Cheney shi ne mataimakin shugaban ƙasa na 46, wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa, George W. Bush a wa’adin mulki biyu daga shekarar 2001 zuwa 2009. An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri A cewar iyalansa, marigayin ya rasu bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita sakamakon ciwon huhu da na zuciya da jijiyoyin jini. Dick Cheney, wanda aka san shi da tsananin ra’ayin mazan jiya, yana daga cikin mataimakan shugabanni mafi tasiri a tarihin Amurka. Ya taka muhimmiyar rawa wajen...
Matsayar da China ta ɗauka na nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu a lokacin da ƙasashen Yammacin duniya, musamman Amurka, ke matsa lamba kan batutuwan haƙƙin ɗan adam da tsaron cikin gida a Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran. Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya. Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare...
Kasashen Musulmi bakwai, da suka yi taro a Istanbul a ranar Litinin don tattauna makomar Gaza, sun dage kan cewa Falasdinawa ne kawai ke da hakkin mulkin kansu, inda sukayi fatali da sabon tsarin kafa wata wani kwamitin gudanarwa na kasa da kasa a yankin bayan makonni biyu na tsagaita wutar da akayi wacce ke tangal-tangal. “Dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa, kuma Falasdinawa dole ne su tabbatar da tsaron kansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ga manema labarai bayan ganawa da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Pakistan, da Indonesia. “Akwai bukatar sake gina Gaza, kuma mutanenta suna bukatar komawa gida inji shi. Ya bayyana fatansa na “sulhu tsakanin Falasdinawa” cikin sauri tsakanin Hamas...
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025
A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar. An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.% na kuri’un da aka kada. Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar. Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara. Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar. Gwamnati ta yi...
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.” “Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar. A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa. A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a...
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa na ƙasa. Shugaban sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya...
Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya da Amurka na da kyakkyawar alaƙa tun da daɗewa, don haka bai kamata wannan sabuwar dambarwa ta lalata dangantakar ƙasashen biyu ba. Obi ya ce dole ne a yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen shawo kan matsalar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump November 4, 2025
Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya tare da tallafin We Are Not Weapons of War (WWoW) a karshen makon da ya gabata a Maiduguri. Taron ya haɗa mutane fiye da 500, ciki har da waɗanda suka tsira daga fyade da cin zarafi a lokacin rikici, sarakunan gargajiya, lauyoyi, jami’an gwamnati da abokan ci gaban ƙasa, domin tattauna hanyoyin magance wannan matsala. “’Yan mata kanana na sayar da jikinsu, suna kuma zubar...
Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi. NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Wadansu dalilai ne ke kara kawo rashin...
Bayan shafe lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta. Duk da haka, Natasha ta ci gaba da nuna ɓacin ranta. “Da ban yi bidiyon kai-tsaye ba, da ba za su dawo da min fasfo ba.” A halin da ake ciki, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025
Gwamnatin Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Nijeriya nan take, tana mai cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilan tsaro, bayan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai harin Soji a yankin Yammacin Afrika. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar damuwa a yankin Sahel. Majiyoyin Soji a N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya bayar da umarnin kulle iyakar kasar da Nijeriya, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda daga arewacin Nijeriya na shirin tserewa zuwa cikin Chadi. An ce umarnin ya shafi manyan hanyoyin shiga da fita, musamman ta yankin tafkin Chadi. Rahotanni sun ce an sanya rundunar Sojin...
Ya ce matsalolin Nijeriya suna buƙatar yin nazari, ba kalaman da za su ɓata lamarin ba. Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma a Kudu maso Gabas da su haɗa kai domin samun zaman lafiya da sulhu. A cewarsa, tattaunawa, adalci da kyakkyawan shugabanci su ne hanyoyin da za su kawo ƙarshen tashin hankali da dawo da amincewa tsakanin jama’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
Prime ministan kasar sudan Kamil idris yayi gargadin cewa aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen waje a kasar Sudan zai kara ruruta wutar rikicin ne da kuma keta yancin kasar, kuma kalaman nasa suna cewa ne bayan rahoton da aka fitar game da cin zarafin dan Adam da aka yi a El-fasher dake arewacin Darfur. Sudan ta dade tana cikin rikci wanda ya haddasa yunkurin juyin mulki sau 20 a kasar da kuma yakin basasa guda biyu, lamarin ya kara taazzara ne bayan rikicin da ya barke a baya bayan nan, wanda ke barazanar ga zaman lafiya yankin , sai dai har yanzu kasashen duniya basu cimma matsaya ba kan yadda zaa samar da zaman lafiya mai...
rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump. Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi. A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji...
Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba. Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025 Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar a yau Litinin cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, sarkin Spaniya Felipe VI, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, daga ranar 10 zuwa 13 ga watan nan na Nuwamba. (Mai fassara Bilkisu Xin) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce November 3, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025
Jami’ar ta kara da cewa, matakin gaggawa da ya dace Sin da Amurka su runguma, shi ne aiwatar da muhimmiyar matsaya da aka cimma, yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a Busan na kasar Koriya ta Kudu, da ingiza karin daidaito cikin harkokin raya tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayyar Sin da Amurka, da ma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin dukkan ƙananan hukumomin jihar da su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin ƙarfafa zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma. A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayar su a tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance matsalolin da ke addabar yankuna. Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotannin hare-haren ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka November 3, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 3, 2025
Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open. ’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian Open a Melbourne a ranar 18 ga Janairu. Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano Kafin hakan dai ’yan wasan biyu, wadanda suka hadu a wasanni uku daga cikin hudu na Grand Slam a shekarar 2025, sun lashe kofuna tara cikin manyan gasa 10 da suka...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
Tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Najeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi abin damuwa ne da ke da ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar. Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa na X. Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Obi ya bayyana cewa, barazanar turo sojojin Amurka su yaƙi ta’addanci da ma sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurkan take da damuwa da su, lamari ne da dole dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar ya ja masa hankali. “Babu shakka...
Ko da yake ƙungiyar ta yaba da sakin biliyan ₦10.6 ga asusun gidauniyar likitoci masu neman ƙwarewa (Medical Residency Training Fund) (MRTF) na 2025, ta ce biyan ya kamata ya zama na yau da kullum, a buɗe, kuma ya dace da hauhawar farashi. NARD ta kuma yi tir da dawo da wasu daga cikin likitocin da aka kora a Asibitin Koyarwa na Lokoja (FTH Lokoja), tana mai cewa dole ne a dawo da dukkan su ba tare da sharaɗi ba. Sauran matsalolin da ta jero sun haɗa da bashin albashi da ba a biya ba a BSUTH, da FMC Owo, da OAUTHC Ile-Ife, rashin aiwatar da tsarin one-for-one replacement, da kuma matsalar amfani da likitoci ƴan kwangila a asibitoci da...
Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi. An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Shugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na aikin al’umma da gidan rediyon ke yi, kuma suna da burin faɗaɗa shi zuwa dukkanin ƙananan hukumomin jihar 44. Ya ce, “Mu gidan rediyon al’umma ne da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya? November 2, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan. Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan motsinsu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse. ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya A sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar, sojojin sun gaggauta kai samame yankin bayan samun rahoto, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar. “A yayin arangamar, an hallaka ’yan bindiga 19, kuma...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sake fuskantar wani mummunan sakamako inda ta koma matsayi na 20, wato ƙarshen teburin gasar Firimiyar Nijeriya ta NPFL. Wannan koma baya na zuwa ne bayan ta sha kashi a hannun Enyimba United a wasan mako na 11, wanda aka buga a filin wasa na Enyimba International Stadium da ke birnin Aba a Jihar Abia. An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a Tanzaniya An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Ɗan wasan Enyimba, Bassey John, ne ya fara zura ƙwallo a ragar Pillars a minti na 27, kafin Edidiong ya ƙara ta biyu mintuna kaɗan kafin a tafi hutun rabin lokaci, lamarin da ya nuna...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
Sojojin haɗin gwuiwa ta Operation MESA ƙarƙashin Birgediya ta 3 sun kashe ƴan bindiga 19 a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wata musayar wuta mai tsanani da ta faru a yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar. Wannan sumame ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin wasu ƴan ta’adda da suka shiga yankin daga maƙwabtan dazuka. A cewar sanarwar Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Birgediya ta 3, Sojojin tare da jami’an tsaro sun fatattaki ƴan ta’addan bayan musayar wuta, inda aka kashe ƴan bindiga 19, yayin da wasu suka gudu da raunin harbi. Ya ce an ƙwato babura da dama da kuma wayoyi...
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36. Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024. BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon...
Sojoji sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan. Bayanai sun ce sojojin sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na shirin ɗaukar matakan soja da ka iya haɗawa da hare-haren ƙasa da na sama a Nijeriya. Trump ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda yake amsa tambayar yanayin yadda hare-haren za su kasance ta sama ko ta ƙasa. NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Tsagin Damagum da Anyanwu sun shirya mamaye hedikwatar PDP a yau A cewarsa, “komai na iya faruwa, abubuwa da dama za su faru. Ina nufin abubuwa masu yawa,” in ji shi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito. Shugaban ya ƙara da cewa, “Suna kashe Kiristoci, kuma suna kashe su da yawa. Ba...
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar. A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da ke da matukar damuwa,” wanda kuma ya yi zargin ikirarin “kisan kare dangi ga Kiristoci.” Kwankwaso, ya yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Nijeriya da tallafin fasaha da leƙen asiri maimakon barazana, sannan ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta zurfafa hulɗar diflomasiyya ta hanyar naɗa wakilai na musamman domin tattaunawa. “Ga ‘yan uwana ‘yan ƙasa,...
Shugaba Bola Tinubu ya ce “ya riga ya yi nisa da wasan da aka tsara a Amurka,” in ji fadar shugaban Najeriya a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci a Najeriya kwanan nan. A cewar Bayo Onanuga, mai ba Tinubu shawara kan bayanai da dabaru, shugaban ya riga ya dauki matakai na dabarun yaki da rashin tsaro a Najeriya tun kafin Trump ya bayyana damuwarsa. Onanuga ya kuma tabbatar da cewa zargin Trump na cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi wani abu ba don kare Kiristoci daga hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai ba daidai ba ne. Mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana cewa Tinubu ya gana...
Daga Aliyu Muraki Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin. Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira. A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa, inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa. Haka zalika su ma likitocin ...
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi. NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar. A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin...
Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro. Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara. Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka. Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don...
Shugaba Donald Trump, ya jaddada cewa Amurka na iya tura sojoji ko ƙaddamar da hare-hare a kan Najeriya idan har kashe-kashen da ya ce ana yi wa Kiristoci suka ci gaba. A yayin tattaunawa da manema labarai da kuma saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Trump ya ce ba zai zauna yana kallo ba. “Ana kashe Kiristoci da dama a Najeriya; ba zan bari a ci gaba ba,” in ji shi. A sakon da ya wallafa a dandamalin Truth a ranar Asabar, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji domin “kakkaɓe” abin da ya kira ƙungiyoyin ƴan ta’adda masu kishin addinin Islama. Haka kuma ya yi barazanar dakatar da duk wani taimakon Amurka...
Sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP yayin da ɓangarori biyu da ke taƙaddamar — na Umar Iliya Damagum, muƙaddashin shugaban jam’iyyar, da na Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na ƙasa — ke shirin mamaye hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja yau Litinin. A ranar Asabar, yayin da Damagum da wasu mambobin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) suka gudanar da taro a Legacy House da ke unguwar Maitama, bangaren Anyanwu kuwa ya gudanar da wani taro daban a ofishinsa da ke Wuye, Abuja. Majiyoyi sun shaida mana cewa bangarorin biyu sun shirya komawa Wadata Plaza, wato hedikwatar jam’iyyar PDP, domin gudanar da ayyuka daga wurin — lamarin da ya tayar da hankalin ma’aikatan hedikwatar. Wani babban jami’in jam’iyyar ya ce, “Abin...
An kama wata matar aure a garin Kuta, hedikwatar Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bisa zargin yankar wuyan mijinta, Salisu Suleiman, da wukar girki. Majiyoyi sun ce matar ta kuma soka wa mijin wuka a idonsa na hagu, lamarin da ya lalata idon gaba ɗaya. Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana wa wakilinmu cewa ma’auratan sun samu saɓani ne, inda matar ta jira har sai da mijin ya kwanta barci kafin ta kai masa hari da wuƙa. Kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarinya auku ne da safiyar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025. A cewarsa, “A ranar 1 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 2:30 na asuba, wani Salisu Suleiman na garin...
Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita cewa dubban yara a falasdinu suna kwana da yunwa kusan kowanne dare, kuma akalla yara 650,000 ba su koma makaranta ba duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimamma a baya –bayan nan tsakanin bangarori biyu, Har ila yau ta bayyana batun dakatar da bude wuta a matsayin labari mai kyau, da ya kawo karshen ci gaba da lugudan wuta da israila ke...
Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun RSF sun kwace iko da El Fasher kuma sun yi kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa. A cikin sanarwar da ta fitar Salma Ishaq, Ishaq ta ce abin da ya faru a El Fasher “ya yi kama da abin da ya faru a El Jeneina a shekarar 2023, amma ba a bankado da kuma yada laifukan...
Daga Yusuf Zubairu Kauru Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu. A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa. Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin. Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda...
Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi. A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai. “Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe. Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar. Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka A cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa. DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da...
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya. Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa. “Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne...
A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare. Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata. Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni. A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kada kuri’ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta’addanci. Majalisar dokokin Ghana ma ta kada kuri’ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023. Wadanne kasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa? Kasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 2, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025
An ture Mataimakin Gwamna Gefe, Tsarin karba-karba Na Goyon Bayan Kwara ta Arewa. Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, zai kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2027, amma babu wata alamar cewa mataimakinsa, Mista Kayode Alabi, zai gaje shi. Yanayin siyasa a jihar na nuna cewa yankin Sanatocin Kwara Arewa ne ake sa ran zai samar da gwamna na gaba; Alabi yana daga Kwara Kudu. Kwara ta Arewa ba ta samar da gwamna da tun daga 1999, yayin da Kwara Kudu ta rike kujerar siyasa ta farko a jihar na tsawon shekaru takwas, kuma zuwa 2027 Kwara Tsakiya za ta kasance ta rike kujerar na shekaru 20. Masu nazarin siyasa guda biyu, Comrade Abdul-Rahoof Bello-Labelabe da Comrade AbdulLateef Ishowo, sun bayar...
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari. Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.” A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa. ...
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
Imam Ali shi ne halifan Annabi Muhammad na hudu a mahangar Ahlussunnan, amma mabiya mazhabar Shi’a na daukar sa a matsayin na farko daga cikin imamansu 12. Wannan ya sanya akasarin mabiya Shi’a na Iraki kan bukaci a binne su a makabartar, kuma sanadiyyar saukin sufuri a zamunnan baya-bayan nan, wasu mabiya Shi’a daga kasashen duniya kan so a binne su a makabartar. Tsarin makabartar ya kasance cakuduwa ce ta gine-ginen hubbarai irin na zamanin baya, da hanyoyi masu tsuku da suka ratsa ta cikinta da kuma wasu wurare da ake yi wa kallon masu tsarki. Me ya sa ake kiran makabartar Wadi al-Salam? Ana kiran makabartar da sunan Wadi al-Salam, wato ‘kwarin aminci’ ne saboda dalilai na tarihi...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama da cutar kansa da kuma cutar koda a Zirin Gaza. Wadannan cututtuka sun kara ta’azzara ne sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza da kuma ci gaba da killace yankin bayan tsagaita bude wuta, gami da hana shigar dq magunguna da kayayyakin ayyukan likitanci masu muhimmanci cikin yankin. Cibiyar ta kuma yi nuni da tsauraran matakan fitar da marasa lafiya zuwa ƙasashen waje don neman...
Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne da rundunar California Army National Guard, mai dakaru sama da 18,000. Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda Aminiya ta tabbatar, Isah ya mayar da martani kan jita-jitar cewa Amurka za ta ɗauki matakin yaƙi a kan Najeriya saboda zargin...
Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda ta yi nasara a kan Arsenal 1-0 a Premier League cikin Agusta da wanda ta ci Burnley 1-0 a cikin watan Satumba a Premier League. Sababbnin ‘Yanwasan da Liberpool ta saya a kakar banamages Giorgi Mamardashbili daga Balencia Jeremie Frimpong daga Bayern Leberkusen, Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen, Milos Kerkez daga Bournemouth, Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt, Aledander Isak daga Newcastle United, Armin Pecsi daga...
Duk da cewa suna da karfi a fannin aikin soja, amma harinsu zai zama tamkar amfani da igwa ne wajen kashe sauro. Duk wani fifikon da suke da shi ba zai dore ba. Saboda haka, a zahiri wannan tambayar da wani mai amfani da yanar gizo ya yi, ta nuna rashin hankali cikin kalaman shugaban Amurka. Sai dai kalaman sun dace da halayya, da salon musamman na shugaba Donald Trump. Wani lokaci, da gangan ya kan yi amfani da kalmomi, da aikace-aikace marasa ma’ana wajen samar da yanayi na rashin tabbas, ta yadda zai samu damar matsawa wani lamba, don tilasta masa ya yi wani aiki. Wannan dabara ce da wasu masanan kasar Amurka ke kira da “ka’idar...
Yawan shafa man kade a wurin ma yana rage ta sosai. Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zarar sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ne babu Kemikal a cikinsa don haka yana daukar lokaci kafin a ga canji kamar, sati biyu idan ba ki ga canji ba sai ki dauki wani kuma. Allah shi ne masani. Allah yasa mu dace. Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba Hanya ta 1: Dankalin Hausa Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antiodidant....
Wasu lauyoyi biyu a Najeriya sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da ta yi taka-tsantsan wajen yin hulɗa da ƙasar Amurka, inda suka ce maganganun Amurka a kan Najeriya abun ruɗarwa ne Babban lauyan nan, Cuf Okoi Obono-Obla, wanda tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ne, ya zargi Amurka da son raba kan ’yan Najeriya da sunan kare Kiristoci. Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya Ya ce iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya ƙarya ne face nufin tayar da hankali da kawo rikici. “Najeriya ba ta taɓa zama barazana ga zaman lafiyar duniya ba,” in ji Obono-Obla. “Idan Amurka, inda ake yawan...
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar. Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya “Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar...
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci. “Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano November 2, 2025 Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da...
Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya cewa babu wani shirin makamin nukiliya domin mun dade muna duba shi. Wannan ya zo ne yayin da Iran ta yi gargadin cewa aiwatar da abin da ake kira “snapback” da sake sanya takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai uku za su soke yarjejeniyar da ta yi da IAEA kan sake fara hadin gwiwa da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a ranar...
Sakataren Ma’aikatar Yaki na Amurka, Pete Hegseth, ya ce ma’aikatarsa na shirin daukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta gaza kawo karshen “kashe-kashen Kiristoci marasa laifi” a kasar. Hegseth, yana mayar da martani ga wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a Truth Social, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci. Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar...
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya. Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan A cewar Daniel Bwala, shugabannin biyu — Tinubu da Trump — sun yi tarayya da juna kan fahimta ta haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama. “A bayan nan Shugaba Trump ya taimaka wajen ba...
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan. Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka. Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Ministan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin. A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen...
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori November 1, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba. A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya. Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla...
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka. Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin da lamura ke kara zafi a yankin bayan yakin da aka yi tsakanin iran da kuma Israila, don haka bayanan na Araqchi wata sanarwa ce dake nuna shirin iran na mayar da martani amma kuma tabar kofar tattaunawar diplomasiya a bude. Har ila yau ministan ya bayyana cewa iran a shirye take ta tunkari duk wani kalu-bale, kuma za ta mayar da martani mai karfi...
Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkabe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa. Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon da Amurka ke bawa Najeriya. Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa. A bayanin da Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba wa ma’aikatar tsaron Amurka damar ta fara...
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum. Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu. Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike “Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu. “An dakatar da shi na tsawon wata guda,...
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace. Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa...
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung November 1, 2025
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini. Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.” PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Trump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su. A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.” A...
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini. Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.” PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Trump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su. A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.” A...
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo. A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa...
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya. Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.” A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Tinibu ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa: Nageria kasa ce ta Demokradiyya,...
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing. Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar. Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin...
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u Sauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin...
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u Sauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin...
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025 Daga Birnin Sin Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu...
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a a ‘Delta state’, na yi makarantar firamare da sakandare a Delta, sannan nayi aure a can. Yara na uku, Allah ya kawo rabuwa tsakani na da mijina. Babana dan ‘Nasarawa State’ ne, Mama ta kuma ‘yar Jihar Kano ce. Shekaruna Talatin da hudu, na tsinci kaina a masana’antar Kannywood ne shekara shida da suka wuce baya. Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Saboda fim yana daya daga cikin abin da ya fara burge ni bayan aure na ya mutu, shi fim abu ne wanda yake kamar wa’azantarwa da kuma tunatarwa. Ya gwagwarmayar farawar ta kasance? Yadda gwagwarmayar ya kasace shi...
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik. Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang) ShareTweetSendShare...
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da fitina a Najeriya. Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u A ranar Juma’a ne, Trump ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta cewar Kiristanci yana cikin hatasri a Najeriya. Ya yi iƙirarin cewa ’yan ta’adda sun kashe dubban Kiristoci, amma ya ce Amurka za ta yi duk mai...