2025-09-17@20:30:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 334
«ɗauke wuta»:
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025. Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci. Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati...
A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696. Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar. A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a...
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ƙaryata zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi masa, dangane da mutuwar wasu marasa lafiya sakamakon katse wutar lantarki da aka ce kamfanin ya yi. Asibitin na AKTH ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi kan abin da ya kira abin takaici yana mai...
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara. An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar...
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da...
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya...
Gwamnatin Belarus ƙarƙashin jagorancin Shugaba Alexander Lukashenko ta saki fursunoni siyasa 52 ciki har da fitaccen ɗan adawa, Mikola Statkevich da kuma ɗan jarida Ihar Losik, a wani yunƙuri da aka danganta da ruwa da tsakin Amurka. Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa: “Mutum 52...
Wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a), ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso. Abu Bara’a wanda Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar a ranar Alhamis, ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ba...
Wata budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba. A cewarsa,...
Hukumar Hana da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta cafke buhuna uku da kuma sinki 150 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 112. Bayanai sun ce an kama kwayoyin ne bayan wani hatsarin mota da ya faru a Gadar Tamburawa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano. Wannan na...
Wata kotu da ke ƙasar Ghana ta yanke wa ’yan Najeriya uku hukuncin ɗaurin shekaru 96, bayan samun su da laifin satar mota a birnin Kumasi na ƙasar. Kotun dai ta samu Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze ne da laifin a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke neman a kori ’yan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar. DSS...
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum. A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa....
Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya...
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari yankin Okpella, da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas, a Jihar Edo, inda suka kashe wasu jami’an tsaro. Sun kashe jami’an Sibil Difens guda takwas sannan suka yi garkuwa da wani ma’aikacin ƙasar China. APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a Jigawa...
Iyayen ɗalibai a sassan arewacin Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ta ƙara kuɗin makaranta da kuma tsadar littattafai a kowace shekara, da sauran hanyoyin da suka ce makarantu ke tatsar kuɗi a hannunsu. Wasu makarantu masu zaman kansu kan tilasta wa iyaye sayen littattafai daga wurinsu kawai, alhali a kasuwa ana samun su...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kogi ta kama wata budurwa mai suna Charity Williams ’yar shekaru 23, wadda aka same ta da kuɗi Naira miliyan 2,047.500 da miyagun ƙwayoyi da kuma bindigar fistol. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’anta da ke aiki da sashin Okene a Ƙaramar hukumar Okene a jihar,...
Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, ta amince za ta biya dukkanin kuɗaɗen jinyar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Nata’ala, wanda ke fama da ciwon daji. Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne, ya bayyana haka lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke Potiskum. Gwamnatin Sakkwato ta ba...
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa...
Wata kotu a Jihar Ekiti, ta tura wani mutum mai suna Ibrahim zuwa gidan yari bisa zargin kashe saurayin ’yarsa. Rahotanni sun ce saurayin ya ziyarci budurwarsa a gidan mahaifinta da ke kusa da Corpers’ Lodge, a kan titin New Iyin, Ado Ekiti. Da ina da iko da cikin mako biyu zan magance matsalar tsaron...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar...
Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko...
’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai...
Manchester United ta amince za ta ɗauki golan tawagar Belgium, Senne Lammens daga Royal Antwerp kan fam miliyan 18.1 har da karin tsarabe-tsarabe. Sasashen wasanni na BBC ya ruwaito cewa hakan ya kawo karshen zawarcin golan Aston Villa, Emiliano Martinez da ta yi. An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe...
Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure...
Wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai rajin ɓallewar ƙasar Biyafara, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa laifukan da suka shafi ta’addanci, zamba da karya doka. Kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya aikata laifuka da suka haɗa da ƙoƙarin hargitsa jama’a da nufin ta’addanci da kuma...
Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United, Alejandro Garnacho, kan kuɗin da ya kai kusan fam miliyan 85 (£85m). Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan na ƙasar Argentina ya rattaba hannu kan kwantiragin zama a Stamford Bridge har zuwa shekarar 2032. Hamas ta tabbatar da mutuwar jagoranta a...
A Arewa maso Yamma, an kama ‘yan ta’adda 35 kuma an kuɓutar da mutane 76. A Arewa ta Tsakiya, an kama mutane 49, an ceto mutane 36, yayin da a Kudu maso Gabas aka kama mambobin IPOB tara. A Kudu maso Kudu, sojoji sun kama mutane 48, sun lalata wuraren tace ɗanyen mai, tare da...
Wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan wata mota mai ɗauke da ma’adinai da ake zargin ta wani kamfanin...
Wata kotu a Ƙasar Amurka, ta yanke wa Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, daga Jihar Osun, hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin zamba a tallafin COVID-19. Alƙalin kotun, Christopher Boyko ne, ya yanke wa Sarkin mai shekara 62 a duniya hukunci a ranar 26 ga watan Agusta,...
Wata kotu a Ƙasar Amurka, ta yanke wa Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, daga Jihar Osun, hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a gidan yari saboda samun sa da laifin zamba a tallafin COVID-19. Alƙalin kotun, Christopher Boyko ne, ya yanke wa Sarkin mai shekara 62 a duniya hukunci a ranar 26 ga watan Agusta,...
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga...
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, ta kama wani matashi mai shekara 29, Sylvester Enemo, bisa zargin kashe matar ɗan uwansa, Misis Esther Enemo, wacce ke ɗauke da juna biyu a Ilorin. An samu gawar Esther mai shekara 39 a yankin Temidire Zone 4, a bayan gidanta cikin daji, an yayyanka jikinta. An haramta bukukuwan aure...
Jam’iyyar NNPP wato New Nigeria Peoples Party, ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da ke Jihar Kano. Babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Hassan Adamu ne ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 12:36 na daren Asabar wayewar gari Lahadi. Farfesa Hassan...
Wasu mutum biyu da ake zargin ɗaliban jami’a ne a Jihar Bayelsa sun mutu bayan wata mota ƙirar tifa ta murƙushe su lokacin da suke kan babur mai ƙafa uku a kan hanyar Tombia zuwa Ammassoma. Daily Trust ta samu rahoton cewa haɗarin wanda ya afku a ranar Talata, ya kuma sa wasu fasinjojin da...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙon kan mutane uku. Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata. Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman...
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar...
Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa...
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata. Ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnati wajen taimaka wa matasa domin rage zaman banza da kuma ba su damar dogaro da kai. Jama’a sun...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekaru 18, Hassan Aminu Sadiq, bisa zargin aikata fashi da makami a lokuta daban-daban, bayan wani samame da aka kai unguwar unguwar Yelwa da ke garin Kwadon a Karamar Hukumar Yemaltu Deba. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama wanda...
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da...
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da...
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna. Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin. Dattijon ya gamu da ajalinsa...