2025-09-17@20:29:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 197

«yayin tsuguno»:

      A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.   Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan. Masoud Pezeshkian shugaban kasar Iran a jiya litinin kafin ya tashi zuwa kasar Qatar domin halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa birnin Doha, ya bayyana cewa: “Gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta amince da wani iyaka ga kanta ba, kuma tare da goyon bayan Amurka, ta...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
    Ministan harkokin wajen Tunisiya Mohamed Ali Nafti ya ce kasarsa da Iran sun amince da karfafa hadin gwiwa tare da shirya taron komitin hadin gwiwa, yayin da yake maraba da sabuwar yarjejeniyar da Tehran ta kulla da hukumar IAEA. A cikin rubuce-rubuce uku na X a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Tunisia ya bayyana cewa, an cimma yarjejeniyar fadada huldar dake tsakanin kasashen Tunusiya da Iran a yayin ganawarsa da takwaransa na Iran Abbas Araghchi a birnin Tunis. Nafti ya ce, “Ina mai farin cikin maraba da takwarana Araghchi, ministan harkokin wajen Iran, a ziyarar aiki da ya kai kasar Tunisiya, mun gudanar da tattaunawa mai zurfi don tantancewa da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, domin samun...
    Aƙalla mutum 12; ciki har da yara huɗu ne suka rasu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Owerri zuwa Onitsha da ke Jihar Imo. Hatsarin ya auku ne lokacin da wata tankar gas mai lamba T 16716 LA, mai ɗauke da rubutun NUPENG, ta ƙwace daga kan hannunta ta afka wa wata motar fasinja. Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki  Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Motar na ɗauke da mambobin Ikklisin Jehovah’s Witness daga Jihar Anambra zuwa ƙauyen Agwa da ke Jihar Imo. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da mutuwar manyan mutane takwas da wasu yara huɗu, yayin da wasu...
    Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru a kotu a yau Alhamis. Za a gurfanar da su ne a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja. Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Mutanen da za a gurfanar su ne Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da mataimakinsa Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Mahmud Al-Nigeri ko Mallam Mamuda. Za su fuskanci tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta’addanci. Tuhuma ta farko ta ce, mutanen sun taimaka wajen tsara da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru tsakanin 2013 zuwa 2015. An haramta ayyukan Ansaru a Najeriya kuma tana da...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu. Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa. NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da ke sa ilimi ƙara tsada yayin da yara ke komawa makaranta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Alamomin Basir Bayyanar alamomin Basir, ya danganta ga wane irin Basir ne ya bayyana, Basir cikin dubura ko kuma Basir a wajen dubura? Alamomin Basir Cikin Dubura: 1- Zubar jini ba tare da jin ciwo ba, a yayin tsuguno. 2- Basir mai tsiro, wanda ke fitowa wajen dubura; har sai an tura da yatsa, domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da radadi. Alamomin Basir A Wajen Dubura: 1- Ciwo mai radadi 2- Kaikayi 3- Kumburi a kewayen dubura 4- Zubar jini yayin yunkurin tsuguno Abuban da ke kawo Basir: Basir na faruwa ne sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura, har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka: 1- Yawan yunkuri yayin tsuguno 2- Tsawaitar lokacin...
    Game da babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya kin tafarkin murdiya, wanda aka gudanar a ranar 3 ga wannan wata, mutane daga kasa da kasa masu halartar bikin sun ba da ra’ayoyinsu ciki har da kalmomin hadin kai, da yin kokari tare, da sauransu don nuna kyakkyawar fata ga makoma. Bayan shekaru 80 da gama yakin duniya na biyu, an canja burin dan Adam. Zaman lafiya da samun bunkasa sun zama babban jigo na halin yanzu, kasa da kasa suna kokarin samun zamanantarwa. Amma a sa’i daya kuma, ra’ayin mai karfi ya cinye maras karfi ya sake bullowa, an kawo illa ga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iyayen ɗalibai a sassan arewacin Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ta ƙara kuɗin makaranta da kuma tsadar littattafai a kowace shekara, da sauran hanyoyin da suka ce makarantu ke tatsar kuɗi a hannunsu. Wasu makarantu masu zaman kansu kan tilasta wa iyaye sayen littattafai daga wurinsu kawai, alhali a kasuwa ana samun su a farashi mafi sauƙi. Wannan matsala ta fi shafar iyaye a zangon farko na shekara, inda buƙatun makaranta sukan yi yawa. Ƙarin kuɗi duk shekara Malama Halima Mu’azu, mazauniyar Hayin Malam Bello a Kaduna, wadda ke da yara a makarantar kuɗi, ta ce: “A wannan zangon makarantar ’ya’yana sun ƙara kuɗi sosai. Babbar ’yata da ke aji ɗaya na sakandare yanzu za ta shiga aji...
    Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta haramta wa makarantu a jihar tilasta iyayen ɗalibai sayen sabbin littattafai duk shekara. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da Hon. Joseph Bukar, ɗan majalisa mai wakiltar Shendam ya gabatar, tare da goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus daga Mangu ta Kudu. Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana Gwamnatin Sakkwato ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kuɗi da shinkafa Bukar, ya ce bai dace ba a ci gaba da tilasta wa iyaye siyan sabbin littattafai duk shekara, inda ya ce hakan cin zarafi ne. ’Yan majalisar sun ce wannan mataki zai rage wa iyaye nauyin kashe kudi. Sun bayyana cewa ana iya sake amfani da littattafai, har ma a raba wa...
    Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta haramta wa makarantu a jihar tilasta iyayen ɗalibai sayen sabbin littattafai duk shekara. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da Hon. Joseph Bukar, ɗan majalisa mai wakiltar Shendam ya gabatar, tare da goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus daga Mangu ta Kudu. Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana Gwamnatin Sakkwato ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kuɗi da shinkafa Bukar, ya ce bai dace ba a ci gaba da tilasta wa iyaye siyan sabbin littattafai duk shekara, inda ya ce hakan cin zarafi ne. ’Yan majalisar sun ce wannan mataki zai rage wa iyaye nauyin kashe kudi. Sun bayyana cewa ana iya sake amfani da littattafai, har ma a raba wa...
    Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi na’am da shawarar inganta jagorancin duniya ko GGI, da kasar Sin ta gabatar a farkon makon nan, yayin taron koli na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko (SCO Plus). Kakakinsa Stephane Dujarric ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, inda ya ce mista Guterres ya bayyana shawarar a matsayin muhimmin mataki na kare tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa karkashin MDD, dake zama jigon cimma nasarar hakan. Kakakin ya ce mista Guterres ya yi tsokacin ne yayin da ya halarci taron koli na SCO a birnin Tianjin a arewacin kasar Sin a ranar Litinin, yana mai bayyana shawarar...
    A ranar 3 ga watan Satumba, Sin ta gudanar da babban bikin faretin soja a birnin Beijing, don tunawa da cika shekaru 80 da yakin da Sinawa suka yi da mamayar Japan kana yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan bikin faretin soja ya nuna sabbin makamai na zamani na Sin, wadanda suka nuna ci gaban fasahohin tsaron kasar. Bikin da kuma kayayyakin aikin soja na zamani sun sa wasu mutane shakku: Shin Sin za ta kama hanyar nuna fin karfi? Amsar ita ce, a’a. Kamar yadda wani soja da ya halarci bikin ya ce: “Ba karfi muke nuna ba, sai dai niyyarmu ta kare adalci.” A wannan bikin faretin soja, rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya, ya ja hankalin al’umma...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da ake gudanar da bukukuwan Mauludi a sassa daban-daban a garuruwan Najeriya, wasu yankunan na gudanar da nasu bukukuwar na daban. Ko yaya ake gudanar da bikin Sallar Gani? NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan yadda ake gudanar da bikin sallar a wasu garuruwan kasar Hausa. Domin sauke shirin, latsa nan
          Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi. Abin da ya yi matukar ba shi mamaki shi ne yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye labarun abubuwan...
    Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar  Shanghai (SCO) a kasar China. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran ta yi amfani da tsarin diflomasiyya a bangarori daban-daban a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekara-shekara a kasar Sin. Gharibabadi  ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shafin Twitter a jiya Talata, inda ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi taron, wanda shugaba Masoud Pezeshkian, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin ya aiwatar da su. A cewar jami’in diflomasiyyar, halartar babban jami’in gudanarwa na kasar Iran a taron ya...
    Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike Harin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Birnin Magaji, inda ’yan bindiga suka kai wa ƙauyuka biyu hari. Mutane da dama ne suka tsere zuwa bakin kogi, inda suka riski jirgin ruwa guda ɗaya kacal. Hakan ya sa aka jirgin da mutane sosai, lamarin da ya sa ya nutse a cikin ruwa. “Babban yayana...
    Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas. Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin. HOTUNA: Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki a Japan da Brazil Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasar Shaidu sun ce ƙungiyoyin asirin biyu sun yi artabu da bindigogi, adduna da kwalabe. Ɗan sandan da ya ji rauni an garzaya da shi asibiti, inda yake cikin mawuyacin hali. Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin. Amma ta ce...
    Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.   A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba...
    Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta. An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar. Aminiya ta ruwaito cewa, waɗanda...
      Amma abin takaici, duniya ba ta san laifukan da Japan ta yi wa kasar Sin a lokacin yakin ba sosai. Har yanzu gwamnatin Japan ba ta nemi afuwar Sin da sauran kasashen Asiya da ta jefa cikin ukuba ba. Har ma, ‘yan siyasar Japan masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da gurbata wannan tarihi, a yunkurin gujewa hukunci da al’ummar duniya za su yi musu.   Mace macen da aka samu a yakin duniya na 2, abun bakin ciki ne ga dukan bil’adama. Al’ummomin kasashen duniya suna da makoma da tarihi na bai daya, wanda ba za a iya mantawa da shi ba, balle a gyara shi.   A bana ake cika shekaru 80 da nasarar yakin kin harin...
    Birnin Mashhad na Iran ya karbi bakwancin maziyarta 3,500,000 daga kasashe 20 a yayin taron tunawa da shahadar Imam Rida (a.s) Dubban daruruwan masu Ziyara daga ciki da wajen kasar Iran ne suke gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida (a.s) a birnin Mashhad mai alfarma da ke arewa maso gabashin kasar Iran. Yayin da masu ziyarar suke ci gaba da isowa, ana gudanar da tarukan makoki a hubbaren da kuma titunan da ke kewaye da hubbaren Imam, inda taron jama’a ya kai kololuwa. Dubban al’ummar Iran ne suka ci gaba da gudanar da isa hubbare daga sassa daban daban na kasar, daga tazarar daruruwan kilomita daga garuruwan su zuwa birnin Mashhad, a cikin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa. Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa ya ƙi ba shi kuɗin da ya nema don yin kasuwanci. Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13 Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya A ranar 11 ga watan Agusta, Bello ya shaida wa iyayensa cewa zai tafi Ibadan, amma maimakon haka ya ɓoye kansa a Ipele. Daga nan ya riƙa kiran iyayensa da abokansa yana...
    Majalisar Dokokin Jihar Gombe, ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomin ci gaban Ƙananan Hukumomi 13 da Gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar. Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu cikin rana guda. Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Kakakin majalisar, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya bayyana hakan ne yayin zaman sauraron ra’ayin jama’a a kan ƙudirin, wanda aka gabatar wa majalisar kwanaki uku da suka gabata. Ya ce majalisar ta yi gaggawar karanta ƙudirin saboda muhimmancinsa, domin zai taimaka wajen kusantar da gwamnati ga jama’a. Hakazalika ya ce zai kawo ci gaba a ƙauyuka, da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jihar ta...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen. Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu. Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci...
    A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya. A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa. Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa....
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya soki lamirin kasar Amurka, dangane da yadda ta wanke Japan daga laifukan da ta tafka, yayin yakin duniya na biyu. Jiang Bin, wanda ya yi sukan a Juma’ar nan, ya kira hakan a matsayin mummunan karan-tsaye ga ainihin abun da ya auku a tarihi, kana tozarta damuwar wadanda mamayar dakarun Japan ta cutar. Jami’in ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, inda ta ce, bana shekaru 80 ke nan, bayan da Amurka da Japan suka kawo karshen yaki a yankin tekun Pacific. To sai dai kuma a ta bakin Jiang Bin, yayin yakin duniya na biyu, dakarun Japan ‘yan mamaya sun aikata muggan...
    Miliyoyin musulmi daga ko ina sun taru a hubbaren Imam Hussain (a) da ke birnin Karbaka na kudancin kasar Iraki, don girmama limami na 3 daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wanda ya zama a bin buga misali a duk tsawon tarihin musulunci na nuna turjiya da kuma fada da azzalumai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Iran ta bayyana cewa miliyoyin musul daga cikin kasar Iraki da kuma wajensa ne suke tattaki da kafa daga ko ko ta ina a cikin kasar zuwa hubbaren Imam Hussain (a). Sannan a kan hanyarsu ta zuwa Karbala akwai dubban mutane masu sa kai, suna raba ruwa da abinci da samarda wuraren hutawa da kuma magani ga wadanda suke bukata....
    Cikin shekaru 20 da suka gabata kawo yanzu, kasar Sin ta himmatu wajen gina tsarin tattalin arziki mai kiyaye muhallin halittu, da ingiza sabon karfi da fifikon bunkasa kai, karkashin tsarin kare muhalli bisa matsayin koli. Wani rahoton hadin gwiwa na cibiyar kwararru ta Xinhua dake karkashin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, da cibiyar bincike game da tunanin shugaba Xi Jinping dangane da wayewar kai ta fuskar kare muhallin halittu ne ya bayyana hakan. Rahoton da aka fitar a yau Lahadi, mai taken “Kyakkyawan ruwa, da tsaunuka masu ban sha’awa, da Sin da duniya masu kayatarwa: Yanayin wayewar kan Sin ta fuskar kare muhallin halittu, da ayyukan da kasar ke gudanarwa a fannin, da yadda take zaburar da...
    A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu. Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma...
    A dai dai lokacinda ake shirin juya yin 40 na shahadar Imam Hussain (a) jikan manzon All..(s) Iraniyawa fiye da miliyon 1.2 suka shiga kasar Iraki daga Iran don halattar wannan makokin. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana ncewa hotunan bidiyo na jami’ann tsaro sun bayyana cewa a lardin Ilam wacce ta mutane kimani 20,000 an ga mutanen Iran suna tafiya ta hanyar Karbala don halattar juyayin  fiye da mako guda da ranar ta 40 wacce zata fado a ranar 14 ga watan augustan wannan shekarar. . Wani hasashe ya bayyana cewa mutanen daga kasashen duniya kimani miliyon 25 zasu halarci Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to...
    Birnin Hiroshima na kasar Japan ya yi juyayin cika shekaru 80 da harin makamin nukiliyar Amurka Birnin na Hiroshima ya gudanar da bikin juyayin cika shekaru 80 da kai harin makamin nukiliyar Amurka ta yi a yau Laraba tare da halartar kasashe fiye da 100, inda mahalarta taron suka yi shiru na dan wani lokaci. Kafin a fara yin shiru, a daidai lokacin da bam din nukiliyar Amurka ya fado a kudancin kasar Japan, da dama daga cikin mahalarta taron sun ajiye furanni a wurin taron tunawa da wadanda harin ya rutsa da su. A wajen bikin juyayin, Hiroshima ta sake yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su dauki matakin kawar da makaman kare dangi. Wakilai daga kasashe da...
    Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun riga mu gidan gaskiya a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya janyo ruftawar ginin gidansu a ƙauyen Dankama da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na dare a ranar Litinin yayin da waɗanda ajalin ya katsewa hanzari ke tsaka da barci. Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri Bayanai sun ce wasu mutum huɗu waɗanda su ma lamarin ya rutsa da su an gaggauta miƙa su asibiti domin samun kulawa. Magidancin da aka yi wa wannan babban rashi, Muhammad Sani Garba, yayin ganawa...
    Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake zargin masu ƙwacen fili ne suka zo ƙauyen tare da ‘yan sanda daga ofishin Byazhin, suna ƙoƙarin ƙwace wani fili a ƙauyen. Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa Dangana, ya ce lokacin da mazauna ƙauyen suka gan su, sai suka taru suka toshe hanya don hana su zuwa wajen filin....
    Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da  Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
    Jami’an tsaro sun tabbatar da kuɓutar wasu ɗalibai shida na Makarantar Horon Ilimin Shari’a ta Najeriya da aka sace. Rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a. ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Kakakin ’yan sandan, Udeme Edet, ya ce ɗaliban sun taso ne daga Jihar Anambra, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makarantar horon ilimin shari’a da ke Yola, a Jihar Adamawa. ’Yan bindiga ne suka tare su a iyakar Binuwai da Taraba. “An ceto ɗalibai shida da aka sace a ranar 26 ga watan Yuli, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Anambra zuwa Adamawa. “An...
    Sai dai girma, kima da ɗaukakar da matasa ke da ita ga al’umma ta ja baya ƙasa sosai a bisa ga yadda rayuwarsu ke iyo da ninƙaya a kogin  zubar da mutunci ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke da alamar ayar tambaya. Matasa da dama a yau ba su ganin kowa da gashi, ba su girmama kowa, ba su ganin mutuncin kowa, ba su daraja kowa ballantana har a tsawata masu ko a ba su shawara da ɗora su kan hanyar yadda za su daidaita rayuwar su daga gurɓatacciyar hanya zuwa madaidaiciyar hanya. Abin takaici ne da matuƙar damuwa yadda matasa suka gurɓata rayuwarsu mamakon amfani da lokaci da damar da suke da ita amma sai suka zaɓi biyewa...
    Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023. Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ta riga ta shiga sabon mataki na neman samun ci gaba mai inganci, wanda ke bukatar gaggauta kiyaye muhallin halittu da rage yawan iskar Carbon da ake fitarwa. Aikin kiyaye muhallin halittu na fuskantar matsin lamba. Ya kamata a yi kokarin zamanantar da kasar Sin bisa tushen samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. (Kande Gao) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a kwanan nan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen amfani da tsarin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali. Dangane da batun Falasdinu kuwa, Guo Jiakun ya ce, “manufar kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo ta hakika ta warware matsalar Falasdinu, kuma kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Falasdinu wajen kafa kasa mai cin gashin kanta.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani. A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa. Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga...
    Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) za ta buga wasan ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika yau da ƙasar Moroko a filin wasa na Olympique da ke birnin Rabat na ƙasar Moroko, za a buga wasan da misalin ƙarfe 9 na dare agogon Nijeriya. Wannan ne karo na biyu da ƙasashen biyu za su haɗu a tarihi, sun haɗu a karon farko a shekarar 2022 a wasan kusa da na ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika na mata, inda Moroko ta fitar da Nijeriya bayan bugun Fenarati, a wannan karon duka ƙasashen biyu na daga cikin waɗanda ake hasashen za su iya lashe kofin, duba da cewa babu kanwar lasa a cikinsu. Kano Pillars: Yaushe Kungiyoyin Kwallon...
    Wasu matasa uku daga ƙauyen Durum sun rasu yayin da suke wanka a wani rafi a ƙauyen Jinkiri, cikin gundumar Tirwun a Ƙaramar Hukumar Bauchi. Matasan su ne; Habibu Mohammed mai shekaru 16, Abubakar Mohammed mai shekaru 16, da kuma Zailani Sule mai shekaru 14. 2027: Obi zai iya takara ba tare da ni ba — Datti Baba-Ahmed NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana wa manema labarai faruwar lamarin. Duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto su, matasan sun rasu kafin a kai su asibiti. Wakil, ya ce bincike ya nuna cewa matasan sun yi aikin haƙar ma’adinai, wanda daga bisani...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin...
    Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya jinjinawa gudunmuwar kasar Sin ga ci gaban kasarsa. Da yake jawabi jiya a fadar shugaban kasar yayin da yake bitar ziyara ta baya-bayan nan da ya kai Amurka, shugaba Embalo ya ce kasar Sin abokiyar hulda ce ta hakika, kuma sahihi yayin da take bayar da taimako. Ya ce babu wanda ke gindaya sharudi a hadin gwiwarsu da Sin, yana mai nanata cewa Guinea Bissau kasa ce mai cikakken ‘yanci kuma ‘yar ba ruwanmu. A cewarsa, kasar Sin ta kasance abokiyar kasar tun farko kuma ba ta taba watsi da su ba. Yana mai bayyana ta da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin mai matukar inganci. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)...
    Eh, wasu mata suna daukar lambar motar duk wanda ya yi musu kyau ko ya zo da motar alfarma, su kai wa malami ko boka domin a janyo hankalinsa ya zo neman aurensu. Hakan kuskure ne babba, ba daidai ba ne a nemi aure ta hanyar sihiri ko dabara marar tsarki. Duk wata riba da ke tattare da hakan ba ta da karko, kuma tana iya dawo da akasin abin da aka nema, kamar rashin samun auren kwarai da tsayayye, zama da mutumin da ba da gaske yake ba, daukewar albarka daga rayuwa, fushin Allah da rushewar aure cikin lokaci. Shawara ga masu haka; ku dogara da addu’a, tarbiyya da hakuri, idan aure naku ne, zai zo da sauki cikin...
    ’Yan ta’addan Lakurawa sun karbe ’yan sanda uku har lahira a yankin Gozirma da ke Ƙaramar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi. ’Yan sandan sun kwanta dama ne a yayin musayar wuta a yayin da ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin kai hari ga matafiya a kan Babbar hanyar Gozirma zuwa Till. Kakakin ’yan sanda a Jihar Kebbi, ya sanar da cewa a yayin ƙazamin faɗan, “an kashe ’yan ta’adda da dama, amma wasu sun tsere da raunukan harbi a jikinsu. Sai dai kuma an yi rashin sa’a ’yan sanda uku sun kwanta dama a yayin arangamar.” Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M Sani, ya yaba da namijin ƙoƙarin jami’an rundunar da ke yankin Zurmi da suka...
    A gabanin bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD, taron kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD wato UNHRC karo na 59 ya zartas da kudurin da kasar Sin ta gabatar dangane da muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam. Wannan ne karo na farko da aka zartas da kudurin ta hanyar tattaunawa a maimakon kada kuri’a. Kasar Sin ta gabatar da kudurin ne a shekarar 2017. Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland ya yi karin bayani kan kudurin da cewa, kudurin ya sake nanata muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, tare da jaddada yadda ci gaba mai inganci kuma...
    Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ta bayyana kudurinta na kara zurfafa dangantakarta da kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Kano.   Wannan alkawari ya fito ne daga bakin kwamandan sashin, Kwamandan Corps Muhammad Bature, a lokacin da yake karbar sabbin shugabannin majalisar a hedikwatar hukumar FRSC da ke Kano.   Sabbin shugabannin kungiyar masu aiko da rahotanni ta NUJ sun ziyarci hukumar FRSC ta Kano domin taya rundunar murna kan kokarin da take yi na inganta hanyoyin kiyaye hadurra da kuma gano sabbin hanyoyin hadin gwiwa.   Kwamandan sashin ya yi maraba da ziyarar, inda ya bayyana ta a matsayin wata babbar alama ta tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin FRSC da...
    A kasar Iraki,miliyoyin mutane sun cika birnin Karbala domin yin juyayin shahadar  Ahlul Bayti ( a.s) da iyalansa tsarkaka, a tsakanin hubbaren Imam Hussain da dan’uwansa Abul Fadal Abbas ( a.s). Masoya Ahlul Bayti ( a s.) da su ka fito daga cikin kasar ta Iraki da kuma wasu kasashe, sun yi cincirindo a cikin birnin na Karbala a tsakanin hubbaren Imam Hussain da Abul Fadal Abbas ( a.s). Cibiyar da take kula da wuraren masu tsarki a Karbala ta yi tsari na kula a tafiyar da juyayin a cikin tsaro  da kuma gabatar da hidima ga masu Ziyara. An girke jami’an tsaro masu tsaro yawa a cikin birnin na Karbala da zagayen haramin Imam Hussain ( a.s) , haka...
    A yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya halarci bikin bude dandalin tattaunawa kan zaman lafiya na duniya karo na 13, a jami’ar Tsinghua inda kuma ya gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa, Han Zheng ya bayyana cewa, a halin yanzu an samu babban sauyi a duniya, tare da fuskantar batutuwan kasa da kasa da yankuna da dama, don haka ana fuskantar kalubale a sha’anin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaban duniya. Ya ce, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, da kiran samun bunkasar duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kuma kiran kiyaye al’adun duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, sun samar da ra’ayoyin Sin kan daidaita manyan...
    Sojojin Nijeriya sun kashe wani shugaban ‘yan ta’adda Mai Dada a yankin Maru na jihar Zamfara yayin wani farmaki na musamman. Babban hafsan Soja Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa an kama wasu waɗanda ake zargin suna kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki, tare da aika wasu masu basu bayanai a jihohin Borno, Kaduna da Edo. Sojojin DRC: Ƴan Tawayen M23 Sun Kashe Fararen Hula 17 Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga A Borno, Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da ƙwato makamai da harsasai da dama, yayin da aka kama wanda ake zargin jigilar kayayyakin ga ‘yan ta’adda a Monguno. An kuma ƙwato bindigogi da harsasai a jihohin Kaduna da Filato,...
    A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna  juyayi ga jaririn Imam Hussain          ( a.s)  Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala. Iyaye mata dauke da kananan yaransu  masu watanni  6 daga  haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran suna masu mika juyayinsu na shugaban Shahidai Imam Hussain ( A.S). Bugu da kari iyaye matan sun gargadi HKI da Amurka akan fada da Iran, suna masu cewa; Dukkanin ‘ya’yansu da za su girma za su kasance sojojin Imamul Hujja ( a.s) da za su yake su. Baya ga Iran da akwai kwasu kasashe 45 da ake juyayin Ashura a duniya. Taro mafi girma na...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. A yayin harin, wata matar aure ta rasu, yayin da wani manomi ya samu rauni. ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa  Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Harin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025, a ƙauyen Ungwan Sarkin Hausa da ke Rimau. Ana zargin maharan sun gudu da shanun da suka sato daga Ƙaramar Hukumar Kauru. A lokacin harin, sun kashe wata mata mai suna Misis Alheri Danzaria. Sun kuma sace wasu mutum biyu, amma daga...
    Mahaifin ango da ƙanin ango na daga cikin mutanen da aka kashe lokacin da wasu suka kai musu hari a Jihar Filato. Rahotanni sun nuna cewa mutum 31 ne ke cikin wata babbar mota mai ɗaukar fasinja 18 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), yayin da aka kai musu hari. Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000 Mutanen sun fito ne daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Pau da ke Jihar Filato domin ɗaurin aure. Mutum 12 sun rasu a sakamakon harin, yayin da 19 suka jikkata kuma ana kula da su...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kada a kuskura a shiga tsakanin yaƙin da Iran da Isra’ila ke fafatawa ta hanyar amfani da ƙarfin soji.  Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gargadi kan duk wani “shiga tsakani na soji”, a yankin Gabas ta Tsakiya, inda manyan abokan gaba Isra’ila da Iran ke musayar wuta a rana ta shida. Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi Nijeriya za ta fara fitar ta tataccen mai zuwa Asia — Matatar Dangote Ita ma ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci bangarorin biyu, da su kare fararen hula yayin da adadin mace-mace da jikkata ke ci gaba da karuwa. Babbar sakatariyar ƙungiyar ta kasa da kasa, Agnes...
    Iran ta zartar da hukuncin kisa kan jami’an leken asirin Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya “Mossad” a safiyar yau Litinin A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan sahayoniyya, bisa tuhumarsa a matsayin maci amana da gudanar da barna a kan doron kasa. An zartar da hukuncin ne bayan kammala shari’ar laifuka da kuma tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke. A cikin wani hadadden aikin fasaha da leken asiri a cikin kasar, an kama Isma’il Fakri a watan Disamban shekara ta 2023 yayin da yake da alaka da hukumar leken asiri...
    Yayin taron shekara-shekara na tattaunawar CBD na shekarar 2025 da aka rufe a yau Juma’a 13 ga wata, mashawarci kana kwararre a hukumar kasuwancin kasar Sin ta kasar Birtaniya, kuma shugaban cibiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Sin mista John Mclean, ya bayyana yayin da yake hira da wakilin CMG cewa, kasuwar kasar Sin tana cike da damammaki, don haka dole ne ya shiga a dama da shi a cikinta. A ganinsa, yayin da ake tinkarar tashe-tashen hankula da rashin tabbaci a duniya, babbar baiwar da Sin take da ita, da muhalli mai aminci da bude kofa ga kowa, sun samarwa kamfanonin Birtaniya da ma duniya baki daya damammaki. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2000 zuwa yanzu, taron ya kasance...
    Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari. He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin...
    A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Korea ta Kudu da su daukaka dangantakarsu zuwa matsayi na gaba ta yadda al’ummominsu za su kara amfana da ita da kawo tabbaci ga duniya mai cike da rashin tabbas, yayin da yake taya Lee Jae-myung murnar lashe zaben shugabancin kasar. Tabbas kyakkayawar alaka tsakanin Sin da Korea ta kudu ta dace da yanayin da duniya ke ciki da muradun al’ummomin kasashen da ma tabbatuwar zaman lafiya a yankinsu da ma duniya baki daya. A matsayinsu na makwabta, wadanda suka shafe shekaru 33 da kulla huldar diplomasiyya, kyakkyawar hulda tsakaninsu na da matukar muhimmanci musamman a irin wannan lokaci da duniya ke cike da hargitse...
    Miliyoyin musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya suka gudanar da sallar Layyah, wanda yake daga cikin manya-manya bukukuwa a cikin addinin musulunci. Tashar talabijin na Press tv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan sallar wanda maniyya da kuma sauran musulni suke yi ya hada da yanka dabba gwagwadon hali, da kuma raba namansa a tsakanin mabukata musulmi. Don tunawa da annabi Ibrahim a lokacinda ya yi kokarin yanka dansa annabi Isma’ila duk da cewa shi kadai ne yake da shi. Kuma yana sonsa, da yayi haka sai All..T ya fance shi da rago, don haka a mai makon dansa ya yanka rago, Ana son duk musulmi baligi wanda ya ke da lafiya da ikon zuwa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin.   Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin ba a yin su a yanzu. Ko wadanne irin al’adu kenan na bukuwan sallah da dattawa ke ganin anyi watsi dasu. NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah...
    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sake haramta duk wani nau’i na hawan Sallah a yayin bukukuwan Babbar Sallar da ke tafe. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata, ya ce har yanzu haramcin da rundunar ta fitar na nan daram kuma za su tabbatar da an yi aiki da shi a yayin bukukuwan Babbar Sallah ta 2025. Ya ce sun dauki matakin ne bayan wani zama da ilahirin shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka yi, inda ya ce sun gano wani yunkuyi da aka yi wajen yin amfani da hawan wajen yi wa harkokin tsaron jihar zagon kasa, kamar yadda aka samu yayin Karamar Sallar da ta gabata....
    Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi.   Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa.   “Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe ‘yan ta’adda sama da 20.   “Abin takaici, a yayin harin ta sama, ‘yan banga biyu a yankin, an kuskure su yayin da wasu kuma suka samu raunuka,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon. Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga wata. Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da ’ya’yansu suke makarantun kwana da su je da wuri domin daukar yaran a ranar Laraba. Kwamishinan mai kula da ma’aikatar, Ali Makoda, ya kuma bukaci iyaye da su tabbata daliban sun dawo makaranta a kan kari bayan kare hutun Babbar Sallar. An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Uba ya harbe ɗansa har lahira...
    Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da HTC ke jagoranta a lardin Suwayda da ke kudancin kasar. Wannan dai shi ne harin farko da Daesh ta yi ikirarin doka kan sabuwar gwamnatin ta Siriya. Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta bayar da rahoton cewa, a yayin harin, wasu mambobi uku na runduna ta 70 na rundunar HTC sun jikkata, a yayin da suke sintiri yayin...
    Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi. Ya jaddada cewa, “tattaunawa hanya ce ta ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba kayan aiki na tilastawa ko mika wuya ba.” Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan. Ya...
    Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da yin kutse cikin Masallacin Al-Aqsa, yayin da kungiyar Hamas ta yi kira da a kalubalance su Daruruwan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a safiyar yau Alhamis suka kutsa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa, karkashin kariyar da ‘yan sandan gwamnatin mamayar Isra’ila, yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen gudanar da taron gangami da kuma jaddada rashin amincewa da keta hurumin alkiblar musulmi na farko, kuma daya daga cikin Masallatai masu daraja na al’ummar musulmin duniya.  Majiyoyin daga Qudus sun ba da rahoton cewa: Tsagerun yahudawan sahayoniyya mazauna matsugunai da dama sun gudanar da rangadi masu tayar da hankali a harabar Masallacin Al-Aqsa mai albarka, ciki har da gudanar da ibadar Talmud da raye-rayen neman tsokana.
    A wani lamari mai ban al’ajabi, a daren jiya dalibai a jihar Taraba sun zana jarrabawar kammala karatunsu na Ingilishi na WAEC da karfe 8:25 na dare, sama da sa’o’i 12 da fara sa’o’i 8:00 na safe.   Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa jinkirin ya haifar da rudani da damuwa a tsakanin iyaye da masu kula da su, wadanda ke nuna shakku kan dalilan dage jarabawar da ba a taba ganin irinsa ba.   Lamarin dai ya yi matukar tayar da hankali idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin. Ba tare da wani bayani a hukumance daga WAEC ba, dalibai da iyaye suna mamakin abin da ya jawo tsaikon da kuma...
    Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, tun daga rubu’i na hudu na shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da matakai a jere na kula da harkokin tattalin arziki, da kyautata yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma hasashen kwarin gwiwa da ake yi kan kasuwanni cikin kwanciyar hankali. Matakin da kamfanin nazari na Moody’s ya dauka na tabbatar da daidaiton mizanin matsayin kasar Sin, wani lamari ne mai kyau, na kyakkyawan fatan bunkasar tattalin arzikin kasar.   Ma’aikatar kudin ta kasar Sin ta bayyana cewa, a mataki na gaba, wasu tsare-tsare za su gudana tare, kuma za su ci gaba da yin tasiri, da samar da cikakken goyon baya ga bunkasar tattalin arziki...
    Rikici ya ɓarke tsakanin wasu matasa a ƙauyukan Faruruwa da Tarandai da ke Ƙaramar Hukumar Takai a Jihar Kano, inda aka kashe wani matashin har lahira. Rikicin ya faru ne a ranar cin kasuwa kuma ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka ƙone rumfunan kasuwar. Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana mu kayar da Tinubu a 2027 ba — Babachir.Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole Wani masani kan harkar tsaro, Zagazola Makama ne, ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi. Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar 23 ga watan Mayu, 2025, a kasuwar Faruruwa. A cewarsa, rikicin ya...
    Jami’an da aka kashen da suka hada da Kwamandan CWC Mallam Sanusi, rahotanni sun bayyana cewa, suna cikin wani aikin kai dauki ne yayin da wasu ‘yan bindiga kusan ashirin (20) dauke da makamai a babura suka yi musu kwanton bauna a madatsar wani rafi.   A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula ya fitar, maharan wadanda suka boye jikin bishiyar mangwaro, sun kona motar jami’an tsaro kirar Hilux a yayin harin.     Gwamna Radda ya samu rakiyar kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Dr. Nasiru Danmusa; Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Daraktan Ma’aikata na Jihar, Shugaban Ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; da sauran manyan jami’an tsaro.   Shugaban karamar hukumar, Alhaji...
    Mutane 7 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu goma sha daya suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Essa dake kan titin Agaie Badeggi a karamar hukumar Katcha a jihar Neja.   Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Minna.   A cewar Abdullahi Baba Arah, motar na dauke da hatsin gwamnatin tarayya, da kuma wata mota dake dauke da wasu fasinjoji 36, wadanda dukkansu maza ne zasu jihar Kano daga jihar Legas suka yi toho mu gama a lokacin da hatsarin ya afku.   Hatsarin ya afku ne da...
    Wani mutum da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane an kama shi a sansanin alhazai da ke Abuja. Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar wa wakilinmu cewa an kama wanda ake zargin, mai suna Yahaya Zango, yayin da ake tantance takardun maniyyatan da ke shirin tafiya Ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana. ’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa.Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Rahotanni sun bayyana cewar Zango yana zaune ne a unguwar Paikon-Kore da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Jami’an tsaro sun bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo saboda zarginsa da hannu...
    Wani hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 37 a ƙauyen Gbajibo-Mudi da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara. Hatsarin wanda ake fargabar ya auku ne a sanadiyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata. Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi Lamarin na zuwa ne watanni bakwai bayan aukuwar makamancinsa wanda ya janyo asarar fiye da mutum 106 a jihar. A cewar wani mazaunin yankin, kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji kimanin 150 ya kife ne a tsakiyar ruwa. Bayanai sun ce waɗanda lamarin ya rutsa da su na komawa gida ne bayan cin kasuwa a tsallake...
    Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai...
    Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas. Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi. Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba  Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Ma’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar. Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya. Ya...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi.   Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar sakandaren Larabci ta mata ta gwamnati da aka gyara tare da inganta ta a garin Gusau.   Ya bayyana cewa, aikin sauran makarantun da ake gudanarwa a fadin jihar, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na farfado da tsarin makarantun kwana, tare da karfafa tsaro domin kare makarantu da kewayen su.   A cewar Gwamna Lawal, inganta kayan aikin makarantu na da matukar muhimmanci wajen...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar za ta kara inganta kula da duk wani abu mai nasaba da sarrafawa ko samarwa a bangaren ma’adanan kasa masu matukar muhimmanci, don hana fitarwa ba bisa ka’ida ba, da kuma kiyaye tsaron kasa.  Mai magana da yawun ma’aikatar wanda ya bayyana haka a yau Laraba, ya ce, karfafa yadda ake kula da fitar da albarkatun ma’adanai masu muhimmanci zuwa ketare yana da muhimmanci ga tsaron kasa da muradun ci gaba. Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025 A ranar Litinin da ta gabata ne, wani taron kasa da aka...
    Abu ne wanda bai dace ba kuma ya saba ka’ida sai dai mu yi wa irin wadannan iyayan fatan shiriya, munanan kalamai gurbata tarbiyyar ‘ya’ya yake yi sukutum, abun fada shi ne kawai iyaye su kiyaye harsunansu wurin furta munanan kalamai ga yaransu ko sauke takaicinsu a kansu dan hakan kan iya janyo babban matsalar da al’umma za ta yi turrr da halin ‘ya’yan, hakuri za su rika yi su kuma danne zuciyarsu saboda zuciya ba ta da kashi munanan kalamai za su iya fita har wanda kan iya janyo da-na-sani kamar tsinuwa da makanantansu. Illoli masu mugun yawa, ciki dawo wa marasa ji a cikin alumma, kwace, fada ta daba, taurin kunne, yawan musu da rashin ganin manya da...
    Bugu da kari, wasu kwararru a fannin aikin noma, su ma tuni suka gargadi manoman kan kaucewa yin shuka da wuri, inda suka shawarce su da su tabbatar da sun kiyaye da hasashen na hukumar ta NiMet, domin kaucewa tabka asara da kuma yin da-na-sani. Lokacin Da Ya Fi Dacewa Manona Su Yi Shuka: Wata kungiya mai bayar da agajin gaggawa, (Christian Aids) tare da hadaka da wasu abokan hudda, sun samar da wata taswira da ke kunshe da lokacin da ya fi dacewa manoman da ke jihohin kasar 36 ciki har da babban birnin tarayayyar Abuja, su yi shuka. Taswirar wadda ta kasance mai saukin amfanai, sun tsara matakan da suka kamata manoman su bi, na kiyaye lokacin yin...
    Kasashen NIjar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu a bangarori da dama. Bangarorin sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a yayin ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin cikin gida da tsaron jama’a da wata tawagar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar tsaron kasa Birgediya Janar Ahmad Rezaei RADAN. A yayin wannan zama Nijar da Iran sun amince da kafa kwamitin kwararru domin yin musayar ra’ayi lokaci-lokaci da karfafa hadin gwiwa. Nijar da Iran, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a fagen yaki da ta’addanci, da manyan laifuffukan kasa da kasa, tsaron iyakoki, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba.
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, da sanya kwanciyar hankali da kyakkyawan kuzari a duniyar mai fuskantar sauyi da tashe-tashen hankula. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin ziyarar da ya kai kasar ta Rasha. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba mai dorewa, cikin koshin lafiya kuma a babban mataki, sakamakon...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa. Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa...
    Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka. Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka. ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane titi, da kowane yaro, tare da cewa a kowace rana, ana kara gargadin cewa; Lokaci ya fara kurewa don ceton abin da za a iya cetowa. Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sabunta gargadi game da bala’in da ke tafe saboda ci gaba da rufe mashigar yankin da kuma tsaurara matakan hana shigowa da madarar jarirai, da abinci mai gina jiki, da kuma...
    A gaskiya wannan matsalar takan faru ne a tsakanin ma’auratan da basa son juna sosai, hadin gida (auren dangi), ko babbar matsala na karya alkawari tsakaninsu, abu ne kuma wanda bai kamata ana yi wa yara hukuncin da ba laifinsu, wannan a bayyane cin zali ne da shirin maida yaro kangarerre. Ba shi da wani amfani sai illah, dan ya kan maida yaro ya zamo baya tausayin iyayenshi, kullum yana cikin jimamin rayuwarsa a duk sanda iyayensa suka samu sabani to, a kanshi ko a kansu za a huce haushi. Babbar matsala ma, dan zai sanya kokwanto a zuciyar yaransu na cewa iyayen nasu anya suna sonsu kuwa? Ko su kadai Allah ya bawa irin wadannan iyayen?, za su kasance...
    Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara. Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis. Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma. Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga...
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo. Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna. Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci. A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34. Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika...
    Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna. Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna. Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin...
    Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana. A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar. Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar. Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu. Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin...
    Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda. An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su. ‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike. Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya umurci a tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a yankin, tare da umartar Mataimakin Kwamishinan Sashen Binciken Laifuka da ya fara bincike da kuma kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai a Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasa Mai Tsarki. Amirul Hajji na jihar na shekarar 2025 kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a lokacin taron farko da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Birnin Kebbi. Ya kuma yi alkawarin tabbatar da jin daɗin mahajjatan jihar yayin da suke a ƙasa mai tsarki. Amirul Hajjin ya bayyana cewa jimillar mahajjata 3,800 daga jihar ne suka biya kuɗin kujerunsu gaba ɗaya domin aikin hajjin bana, kuma jigilar mahajjatan za ta fara ne ranar 9 ga watan Mayu, inda ya ce da yardar Allah za a ci...
    Gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkanin buƙatun ɗaliban na zana jarabawar, ciki har da abinci da wurin kwana, har na tsawon kwanaki uku. Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Lawal Mohammed Rimin Zayam, ya yaba da wannan mataki na JAMB, yana mai kira ga iyaye da su tura ‘ya’yansu dake da lalura ta musamman makaranta domin samun ilimi. Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma da iyaye su fahimci muhimmancin ilimi, musamman ga yara masu naƙasa, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da wayar da kan iyaye don ganin suna tura ‘ya’yansu makaranta.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya. A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance...