2025-11-02@19:45:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2597

«kan naira miliyan»:

    Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya. Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa. “Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama da cutar kansa da kuma cutar koda a Zirin Gaza. Wadannan cututtuka sun kara ta’azzara ne sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza da kuma ci gaba da killace yankin bayan tsagaita bude wuta, gami da hana shigar dq magunguna da kayayyakin ayyukan likitanci masu muhimmanci cikin yankin. Cibiyar ta kuma yi nuni da tsauraran matakan fitar da marasa lafiya zuwa ƙasashen waje don neman...
     Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya cewa babu wani shirin makamin nukiliya domin mun dade muna duba shi. Wannan ya zo ne yayin da Iran ta yi gargadin cewa aiwatar da abin da ake kira “snapback” da sake sanya takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai uku za su soke yarjejeniyar da ta yi da IAEA kan sake fara hadin gwiwa da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a ranar...
    Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin  tattaunawa da kasar Amurka. Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin da lamura ke kara zafi a yankin  bayan yakin da aka yi tsakanin iran da kuma Israila,  don haka bayanan na Araqchi wata sanarwa ce dake nuna shirin iran na mayar da martani amma kuma tabar kofar tattaunawar diplomasiya  a bude. Har ila yau ministan ya bayyana cewa iran a shirye take ta tunkari duk wani kalu-bale, kuma za ta mayar da martani mai karfi...
    Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.” A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi,...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher.     Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka.   Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waray tarho da takwaransa na Sudan Mohiuddin Salem a ranar Juma’a. Na farko ya nuna damuwa musamman game da hare-hare da kisan gillar da aka yi wa fararen hula a birnin El Fasher da ke kudu maso yammacin Sudan. Duniya ta damu matuka a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar tashin...
    “Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.” Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.” Ya kara da cewa,...
    Wani gidan shan kofi a birnin Dubai ya fara sayar da kofi guda na haɗaɗɗen kofi a kan kusan Dala 1,000, wato kimanin Naira miliyan 1.5, wanda da haka ya zama mafi tsada a duniya. Gidan shan kofin mai suna Julith Café — da ke cikin unguwar masana’antu da ya zama sabuwar cibiyar masu son kofi, shi ne ya ƙaddamar da wannan sabon nau’in abin sha mai daraja. Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai. Wani daga cikin masu mallakar gidan, Serkan Sagsoz, ya ce sun zaɓi Dubai ne saboda “birni ne da  ya...
    Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025
    Gwamnatin kasar Iran  ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa . Tsibiran guda 3 da ake takaddama akansu Abu musa da tunbu babba da karami  suna yankin tekun fasha ne tsakanin mailand na iran da kuma hadaddiyar daular larabawa, tsibbiran wani bangare ne na kasar iran tun karnoni da suka gabata da ke cike da abubuwa da suka safi doka da tarihi  a iran da kuma kasa da kasa. Iran ta jaddada cewa dukkan wadannan tsibirai guda 3 wani bangare na kasarta...
    Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko mukami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda da ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II. Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan. A yanzu “za a rika kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor,” in ji sanarwar. Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo karshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata wadanda ake alakantawa da masarautar. Yanzu an tube shi karfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su. Share 0 0 votes...
    A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.   Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.   Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga...
    Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League. Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4. Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa  Real Madrid ta ce, wannan hukuncin ya tabbatar da cewa UEFA ta karya dokokin gasa, kuma ƙungiyyoyi sun rasa maƙuden kuɗaɗe tun daga lokacin da aka dakatar da gasar. Gasar wacce aka shirya farawa a shekarar 2021 tare da manyan ƙungiyoyin Turai, an yi hasashen zata samar...
    Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa. A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Pulling Out Parade ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta. Wannan biki na nuni da kammala aikin Soja a matakin ƙoli, kuma yana ɗaya daga cikin manyan al’adun da ake yi wa manyan jami’an da suka yi aiki da ƙwarewa da sadaukarwa. Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa. Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar  suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i. Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.   An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa. A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin. “Harkokin da suka shafi jami’anmu da...
    Za a gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 32 a Koriya ta Kudu. Eduardo Pedrosa, babban daraktan sakatariyar APEC, ya bayyana cewa tun bayan shigarta APEC, Sin ta kasance mamba mai himma da kwazo. Kuma a halin yanzu, tana taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagoranci a karkashin tsarin APEC, haka kuma tana mai da hankali kan yadda za a inganta samar da manyan ci gaba a yankin da kuma duniya baki daya. Eduardo Pedrosa ya bayyana haka ne kwanan nan yayin wata hira da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a birnin Gyeongju dake Koriya ta Kudu. Ya kuma yaba da nasarorin da Sin ta samu a tafarkinta na zamanantar da kanta.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU...
    Bugu da kari, shaidu na zahiri sun tabbatar da cewa alakar ci gaban kirkire-kirkiren fasahohin Sin da sauran sassan duniya, ya kunshi kafa tushe na samar da karin daidaito a fannoni da dama, ciki har da hada-hadar cinikayya ta dijital, da ilimi da jagoranci.   Ta hanyar rage gibin dake akwai tsakanin mabanbantan sassan duniya, sashen kirkire-kirkiren fasahohin Sin na kara fadada damar raya masana’antun duniya, da samar da guraben ayyukan yi, musamman a yankunan duniya da aka jima da yin watsi da su, wanda hakan zai yi matukar amfanar da tsarin kasuwancin duniya.   A fannin raya fasahohin cin gajiyar makamashi marar dumama yanayi ma kasar Sin na kara taka rawar gani, inda alal misali Sin ke bayar da...
    Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye wani mai suna Stephen Adamu mai shekara 34 bisa laifin kashe ɗan uwansa. An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye a ranar 31 ga watan Junairu, 2025, kan tuhumar kashe wani David Adamu, a sashi na 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti 2021. Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Domin tabbatar da ƙarar sa, mai gabatar da ƙara Funmi Bello, ya kira shaidu shida da waɗanda ake ƙara da su gabatar da jawabi, da fom ɗin shaida da kuma wuƙa a matsayin nunin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Ana ci gaba da bin hanyar diflomasiyya ko da a ƙarƙashin fada ce amma ba za a yi tattaunawa a ƙarƙashin umarni ba Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar a ranar Laraba cewa: Hanyar diflomasiyya za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga Iran, ko da a lokutan mawuyacin hali. Duk da haka, ya jaddada cewa Iran ba za ta yi tattauna da wani maƙiyi mai wuce gona da iri da mai daukar matakin ƙarfi ba, ta hanyar nuna tashin hankali da barazana ba. Jawabin Araqchi ya zo ne a lokacin da ya halarci zaman taron kan tattaunawar kasa ta Azerbaijan, mai taken “Diflomasiyya ita ce Ingancin Hanyar da...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Amurka ta ɗaga tutar zaman lafiya yayin da muggan makamanta suke ci gaba da kai hare-hare kan al’ummun duniya Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya tabbatar da cewa: Taken zaman lafiya da Amurka ke gabatarwa a yanzu karya ne, yana mai cewa: Yayin da Amurka ke ba da shawarar zaman lafiya da tattaunawa a lokacin yakin da ya gabata, jiragen yakinta B-2 suna shirin kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran a lokaci guda. A lokacin da ya ziyarci lardin Khorasan ta Arewa da ke arewa maso gabashin Iran, Qalibaf ya yi jawabi a wani taro na tunawa da shahidan lardin a ranar Laraba da yamma, yana mai cewa:...
    Wani matashi mai shekaru 20, Jibrin Saidu Lamido, ya rasa ransa bayan wani rikici a kan soyayya da ya auku  ƙauyen Gurdadi da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari a Jihar Yobe. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da Jibrin ya je zance wajen budurwarsa Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri. Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35 Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati Wata majiya ta ce wani mutum da ba a san ko waye ba ya zo wajensu, tare da tafiya da budurwar sannan ya ƙalubalanci Jibrin da ya biyo su idan shi “namijin gaske ne.”...
    Majalisar Tarayya, ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓo rancen dala biliyan 2.35 domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025. Dukkanin Mjalisun sun amince da buƙatar ne a ranar Laraba, bayan sun duba rahoton kwamitin karɓar basussuka na cikin gida da na waje. Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu baya Haka kuma, majalisar ta amince da buƙatar Tinubu na fitar da dala miliyan 500 domin samar da muhimman ayyuka kamar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi ga ƙasar nan. A cikin wasiƙar da ya aike wa majalisar tun a farkon watan nan, Shugaba Tinubu, ya bayyana cewa neman rancen ya zama dole domin aiwatar...
      Dr. Alausa ya ce, za a fitar da kudaden ne ta Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), wanda hakan ke nuna kudirin Shugaba Bola Tinubu na biyan basussukan da ya gada domin karfafa kwarin gwiwar ma’aikata a manyan makarantu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro October 29, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya October 29, 2025 Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025
    CIBIYAR yin nazarin yankuna dake islam abada ta gudanar da wani taron tattaunawa mai take takunkumin snapback kan iran da kuma faduwar yanki,  ya kunshi jami’an diplomsiya , malamai da kwararru kan manufofi da siyasa da tsarin doka, sun bayyana damuwar da ake da ita na sake kakabawa iran takunkumi karkashin tattaunawar JCPOA. Kwararrun sun yi  barazanar cewa sake kakabawa iran takunkumi zai iya haifar da mummunan sakamako ba wai ga tattalin arzikin kasar iran ba kawai, ga ma harkokin kasuwanci a yankin, tsaro da makamashi zai iya zarcewa zuwa inda ba’a yi tammani ba, Tattaunawar ta zo ne adaidai lokacin da kasashen turai ke kokarin rusa yarjejeniyar JCPOA  wanda zai kai ga sake dawo da takunkumin kwamitin tsaro...
    Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Turkiya Rajab dayyib ardogan da ma alummar kasar na farincikin zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, kuma ya jaddada muhimmancin kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Iran da Turkiya suna da alaka mai zurfa ta tarihi aladu da kuma dabarun yaki, a daidai lokacin da ake samun sauyi a yankin , akwai bukatar kasashen biyu sun kara hadin guiwa a fannonin kasuwanci tsaro da kuma diplomasiya, sakon na pezeshkiyan ya nuna aniyar iranta fifita yin hulda tsakanin kasashen biyu Akwai abubuwa da dama da suka yi kama da juna tsakanin kasashen biyu masu abokantaka da yan uwantaka, pezeshekiyan, ya kara da cewa ta...
    Asalin tsarin shari’ar da ake amfani da shi game da kare muradun al’umma ya bai wa masu gabatar da kara damar yin aiki na neman hukunta masu laifi a madadin sauran al’umma a shari’o’in da suka shafi laifukan gurbata muhalli, da rashin kiyaye tsaftar abinci, da kuma rashin da’a ga gwamnati wadanda dukkansu idan aka bar su kara-zube, za su tauye hakkokin galibin jama’a. Amma a halin yanzu, sabon daftarin dokar da ake son kafawa ya fayyace nau’ikan dokoki 16, ciki har da karin wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka shafi al’adun gargajiya da kuma tsaron kasa, wanda ke nuna kara fadada tsarin dokar.   Domin ganin ba a tauye hakkin kowane bangare tsakanin mahukunta da mabiya ba, a...
      Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin. Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin. An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Waɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara...
    Wata gamayyar malaman addinin Musulmai ƙarƙashin inuwar Concerned Ulama of Sunnah ta aika da ƙorafi zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna tana zargin wasu malamai biyu da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Ana zargin malaman ne da yi batancin a cikin wa’azozinsu na kafafen sada zumunta. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Ƙorafin, wanda malamai goma sha shida (16) suka sanya wa hannu, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Umar Shehu Zaria da Malam Muhammad Sani Abubakar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Na’iya, ya bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki. A cewar masu ƙorafin, ayyukan waɗannan malamai biyu “na...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
    Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ɗan kasuwa mai taimakon al’umma, Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa shugaban na da kwarewa da hangen nesa wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar da inganta jin daɗin jama’a. Zaura ya yi wannan kiran ne lokacin da wata tawaga daga Tinubu/Shettima Campaign Group ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, inda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Nijeriya na da matuƙar muhimmanci domin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tabbatar da matsayi irin na ƙasashen da ke...
    Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Ali Larijani (SNSC) ya ce dangantakar da ke tsakanin Tehran da Islamabad tana  habaka, kuma za ta iya kaiwa matsayin babban hadin gwiwa na din-din-din. Ali Larijani, a yayin da yake yin wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan Syed Mohsin Naqvi a wannan Talata a birnin Tehran, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar ƙasashen biyu a fannin tattalin arziki. Ya nuna yarjejeniyar dabarun da aka cimma a cikin kwanakin nan tsakanin Pakistan da Saudiyya, a matsayin mataki mai kyau kuma na hikima, wanda yake da tasiri matuka ga irin barazana da kasashen musulmi sue fuskata daga makiya. Larijani ya ce yanayin yankin a yau yana cike da ƙalubale daga maƙiya, wanda ke...
    Firayim Ministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani ya jaddada cewa wajibi ne a kan al’ummar Iraki kare  ‘yancin kundin tsarin mulkin kasarsu wanda hakan ba zai yiwuwa ba sai hanyar  tsara makomar kasar ta hanyar sahihin zaben ‘yan majalisar dokoki da ke tafe. Al-Sudani ya jaddada cewa babu wani uzuri na kin kauracewa zabe da za a yarda da shi, yana mai bayyana cewa yin hakan “zai share fagen dawowar wadanda suka gaza da kuma wadanda suka ci hanci da rashawa.” Ya ce, “Muna dogaro da shiga cikin harkokin zabe cikin sani da himma a ranar 11 ga Nuwamba, ranar da za mu tsara sabuwar makomar siyasa ta Iraki.” Ya fayyace, “Muna son manufofin hikima da fifita muradun Iraki da al’ummar...
    Sama da Falasdinawa 60, ciki har da yara 22 ne suka yi shahada  a jerin hare-haren jiragen yakin  Isra’ila suka kai a wurare da dama a yankin Gaza A cikin sa’oin da suka gabata, A cewar majiyoyin lafiya. Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a lokaci guda kan gidaje, masallatai, da sansanonin ‘yan gudun hijira. Wakilin Al-Mayadeen ya ruwaito cewa an kai wani harin bam a kan  gidan iyalan Abu Dalal da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, inda aka  kashe mutane 10, ciki har da yara uku. An kuma kai hari gidan iyalan Aql da ke sansanin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar  mutane uku da kuma jikkata da dama, yayin da Isra’ila take ci gaba da kai hari...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci rundunar sojin ƙasar da ta kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, bayan ya zargi ƙungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma. Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar, ta ce: “Bayan tattaunawar tsaro, Firaminista Netanyahu ya umurci rundunar soji da ta gaggauta kai hare-hare masu ƙarfi a Zirin Gaza.” Juventus ta kori kocinta Igor Tudor An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Sanarwar na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas ta karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanakin baya domin ba da damar kai agaji ga fararen hula da ke yankin. Tun da farko dai Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani...
      “Bayan gano alamun karkatar da kudaden tallafin a matakin farko, mun gabatar da matakai don tabbatar da cewa kudin ya isa ga wadanda aka yi niyya,” in ji shi.   Wasu daga cikin matakan da aka dauka sun hada da kafa kwamitin mambobi 20 a kowace karamar hukuma, wanda ya kunshi sarakunan gargajiya, shugaban karamar hukuma, shugaban jam’iyya, da sauran mambobi.   Ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kudaden ta hanyar kafa kananan kasuwancin kashin kansu domin inganta yanayin samun kudinsu da zamantakewarsu domin habaka tattalin arzikinsu da kuma na iyalansu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28,...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
    Jakadan China a Iran ya ce kasarsa za ta dauki mataki idan takunkumin da aka sanya wa Iran ya shafi muradun ta. A wani taron manema labarai da aka gudanar a Tehran jami’in diflomasiyyar naChina ya ce Beijing “ba za ta yi jinkirin daukar mataki ba” idan sabbin takunkumin suka shafi cinikayyarta da Iran. Wadannan kalamai sun zo ne a matsayin martani ga tambayoyi game da matsayin China kan takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da aka sake kakaba wa Iran, wanda aka sake kakabawa a karshen watan Satumba bayan da kasashen Turai da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka zargi Tehran da gaza cika wajibcin da ke kanta a karkashin yarjejeniyar. Jakadan Chinar ya kuma nuna cewa Beijing...
    Rundunar ’yan sandan Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’ai 59 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin ɗawainiyar da rundunar ‘yan sandan ke yi wajen kula da jin daɗin jami’anta da iyalansu. Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jigawa, CP Dahiru Muhammad ne ya wakilci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, wajen raba tallafin a ƙarƙashin shirin nan na tallafa wa iyalan...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Haɗin kai a tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ba zaɓi ba ne, amma dole ne Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Hadin kai da hadin gwiwar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya a cikin tsarin Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki (ECO) ba wani zaɓi ne na siyasa ba, a’a, wani muhimmin abu ne don cimma ci gaba, tsaro, da kwanciyar hankali a yankin. A lokacin jawabinsa a taron Ministocin harkokin cikin gida na kasashe membobin ECO na hudu, Pezeshkian ya lura cewa: Kiran wannan taron bayan dogon hutu yana nuna sha’awar kasashen membobinta na inganta hadin kai da hadin gwiwa a muhimman fannoni da ke shafar dangantakar yankuna. Ya bayyana cewa ma’aikatun...
    Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan Harkokin Siyasa na Iran ya bayyana cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya amma ta yi watsi da duk wata tattaunawar dole da aka tilasta mata Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Harkokin Siyasa na Iran ya jaddada cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya, amma ta yi watsi da duk wata tattaunawa da aka tilasta mata bin duk wani ra’ayin wani bangare guda. Ya jaddada cewa: Warware takaddama cikin lumana zai yiwu ne kawai idan bangarorin biyu suna kan daidaito kuma babu wanda ke neman sanya sharuddansa. A lokacin taron kasa da kasa na hudu na nazarin Iran na zamani, a wani zama mai taken “Iran da Duniya Bayan Yakin Kwanaki 12,” Mataimakin Ministan Harkokin...
    Iran, a matsayinta na ƙasa mai wayewa da wayewa, ta kasance mai himma wajen haɓaka zaman lafiya da tsaro a duniya, in ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Esmail Baqaei a ranar Litinin a gefen wani biki na cika shekaru 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya a Tehran. A cewar Pars Today, Baqaei ya ƙara da cewa a cikin ‘yan shekarun nan, an sami manyan keta ƙa’idodi da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, waɗanda suka yaɗu a duk duniya. Ya yi gargaɗin cewa rashin kula da manufofin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya zaman lafiya da tsaro a duniya cikin haɗari mai girma. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake jaddada buƙatar...
    Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasar kasa da kasa Dr.  Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai kasashe uku a cikin Asiya wadanda suke da ‘yanci da su ne Iran, China da Rasha, kuma suna taka rawa domin samar da sabon tsarin tafiyar da duniya. Dr. Wilayati ya bayyana hakan ne dai a yayin ganawarsa da jakadan China a Iran “Zong Bi Wuu” yana mai kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade da kuma zurfi.  Har ila yau Wilayati ya ce alakar kasashen biyu ta ginu ne akan maslaha da kuma girmama juna da kuma cin gashin kai na siyasa, da hakan ya mayar da su, tare da kasar Rasha zama...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce hadin kai tsakanin kasashen Musulmi yana da matukar muhimmanci wajen kare muradunsu da tsaronsu, daga duk wani cin zarafi daga kasashen waje. Mista Pezeshkian ya yi wannan furuci ne a wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Oman Sayyid Hamoud bin Faisal al-Busaidi a Tehran yau Litinin. Da yake nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Oman, wacce ya ce ta kasance bisa girmama juna da kuma kyautatawa. Shugaban ya ce kasashen biyu ko yaushe suna goyon bayan junansu ta hanyar ci gaban yankin. Ya yaba da rawar da Oman ta taka a ci gaban yankin, musamman a fannin sulhu da kuma karbar bakuncin tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Iran...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar.   Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta. Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata. Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga...
    Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman majalisa a Tehran a ranar Lahadi, mako guda bayan da kasashen uku suka mika wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Kwamitin  Tsaro wasikarsu, inda suka tabbatar da kawo karshen aikin kuduri mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 wadda Amurka ta yi watsi da ita. “A cikin ‘yan kwanakin nan, mun shaida...
    Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke. Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki, tabbas  za su fuskanci Isra’ilawa da dukkanin karfinsu, kuma ba za su bar Isra’ila ta mamaye kudancin Lebanon ba,ko da kuwa hakan zai kai ga shahadarsu ne baki daya. Ya yi ishara da irin ayyukan wuce gona da iri da isr’ila ke yi akullum rana ta allaha  kan kasar Lebanon a kan idanun duniya, wanda hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar dakatar dayaki da...
    Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu. Wanda aka kashe mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi ne da ke shekara ta uku a sashen hada-hadar kuɗaɗen banki. Dangote na shirin faɗaɗa matatarsa don zama mafi girma a duniya Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki Ana zargin Nanpon Timnan da ke ajin shekara ta biyu daga sashen karatun harkar noma, da kashe shi sannan ya binne shi a rami. Rahotanni sun bayyana cewar ɗaliban abokan juna ne sosai. An ruwaito sun fita ƙwallon ƙafa, daga nan suka wuce wani waje sannan suka dawo gida. “Da suka dawo...
    Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu. Wanda aka kashe mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi ne da ke shekara ta uku a sashen hada-hadar kuɗaɗen banki. Dangote na shirin faɗaɗa matatarsa don zama mafi girma a duniya Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki Ana zargin Nanpon Timnan da ke ajin shekara ta biyu daga sashen karatun harkar noma, da kashe shi sannan ya binne shi a rami. Rahotanni sun bayyana cewar ɗaliban abokan juna ne sosai. An ruwaito sun fita ƙwallon ƙafa, daga nan suka wuce wani waje sannan suka dawo gida. “Da suka dawo...
    Kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa ba za ta bari Isra’ila ta samu wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba. Khalil al-Hayyah jigo a kungiyar ta Hamas, ya nuna gazawar gwamnatin Isra’ila na cimma burinta a Gaza kuma ya bayyana cewa kungiyar tana mutunta dukkan alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ba kuma ba za ta bari makiya su sami hujjar ci gaba da yakin ba. al-Hayyah, shugaban ofishin siyasa na Hamas a Gaza, ya bayyana a wata hira da tashar Al Jazeera cewa gwamnatin Isra’ila ta gaza cimma duk wani burinta a lokacin yakin kuma Hamas za ta yi duk mai yiwuwa don hana sake barkewar yaki. Da...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya  Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.  Gwamna Raɗɗa...
    Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.   Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin  gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa! A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya furta sun isa su zame a matsayinsa mayar da martani. Ya zo cikin Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa: Alfaharin Shugaban Amurka cewa: “Hakika sun yi luguden wuta kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran tare da ruguza su, tabbas wannan da’awa ce kawai, amma Amurkawa su ci gaba da rayuwa cikin wannan ruɗunsu!” Martani mai ƙarfi...
    Wani rahoto na kafar watsa labarun Birtaniya ya bayyana cewa; Da akwai fiye da fursunoni 90 da suke yajin cin abinci a gidan kurkukun kasar Bahrain suna neman a sake su. Rahoton ya kuma ce, mafi yawancin fursunonin da suke yajin cin abincin suna babban gidan yarin kasar ne, kuma an kama su da yi musu hukunci ne bisa dalilai na siyasa. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da fursunoni a kasar Bahrain suke yajin cin abinci bisa nema a kyautata yanayin rayuwarsu a inda ake tsare da su, ko kuma neman a sake su ba tare da wani sharadi ba. Wani sauti na daya daga cikin fursunonin da aka dano daga cikin gidan kurkuku, ya bayyana cewa;...
    Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran  Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya. Ali Larijani ya kara da cewa; Sun kashe al’ummar Falasdinu, sun hana shi abinci da ruwa, yanzu kuma suna son bayyana kawukansu a matsayin masu ceto da Falasdinawa, don haka wannan taron ba komai ba ne sai wasan kwaikwaiyo. Taron da aka yi a Sherm-Sheikh na Masar an yi shi ne a karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump wanda kasarsa ce ta kasance a gaba wajen bayar da makamai ga...
    Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU,  ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar. A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta bayyana cewa labaran da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama. Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam “Mun lura da wani faifan bidiyo da na’urar AI ta ƙirƙira, wanda wasu ke yaɗawa suna iƙirarin cewa ABU na ƙera makamin nukiliya a ɓoye. Wannan ƙarya ce babu gaskiya a cikinta,” in ji...
    Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta karyata wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na da hannu wajen wani shiri na sirri kan hada makamin nukiliya a Nijeriya. A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya fitar a ranar Asabar, jami’ar ta bayyana cewa wannan faifan bidiyon da aka samar ta hanyar na’urar kirkirar bidiyo, karya ne kuma an shirya shi ne don rikita jama’a da bata hakikanin manufar kasar wajen amfani da makamashin nukiliya. Umar ya jaddada cewa dukkan aiyukan nukiliyar Nijeriya ana gudanar da su ne bisa tsarin lumana da kuma bin ka’idodin kasa da kasa kamar yarjejeniyar NPT da Pelindaba Treaty, wadda ta...
    Ta hanyar aikinsa, Adeyemi yana nuna cewa ƙirƙira tana da ƙarfi sosai lokacin da take bauta wa bil’adama. Manhajarsa, wacce yanzu ake gwadawa a makiɗa da dama na manyan makarantu, ba kawai tana ba da damar samun ilimi bace, har ma da haɗa ɗalibai cikin zamantakewa, tana taimaka wa aiki ga ɗalibai masu rauni a gani bane kawai, su yi hulɗa da ƙwarin gwiwa a cikin ajujuwa da muhallin dijital. A wannan ma’anar, gudummawarsa ta kasance fasaha da ɗan’Adam: tana cike giɓi, faɗaɗa dama, kuma tana ƙalubalantar tunanin da aka saba game da naƙasa da ƙwarewa. Tafiyar Adeyemi tana nuna haɗin kai tsakanin ƙwarewar fasaha da shugabanci mai manufa. Bayan ya yi horo a Kimiyyar Kwamfuta a Coɓenant Uniɓersity, ya...
    Ya ƙara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta  jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba. A cewarsa, “ABU tana ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta kimiyya da fasaha don ci gaban ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta hanya mai amfani da jama’a.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 ...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Bai kamata a yi mummunan amfani da kwamitin tsaron ba ko kuma a yi amfani da shi don dalilai na siyasa Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya bayyana cewa: An gwada Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sosai ta hanyar ayyukan ta’addanci da kuma amfani da dabarunta na siyasa. Ya ce: “Dole ne kwamitin tsaro ya cika nauyin da ke kansa da mutunci, inganci, kuma ba tare da son kai ba. Babu wani memba, komai karfi da zai iya amfani da wannan cibiyar ba bisa ka’ida ba ko kuma ya yi amfani da shi don dalilai na siyasa ko na bangare guda.” A jawabinsa a Majalisar...
    Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora wa Iran, ba wai kawai bai cimma komai ga Isra’ila ba ne, har ma ya canza daidaiton dabarun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila gaba ɗaya. A lokacin taron tattaunawa na 31 na ƙungiyar Jaruman Musulunci a Qom, Hussein Ta’ib ya ce: “Dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Iran sun kalubalanci masu girman kai inda suka kai wani mataki cikin saurin na zarce lissafin...
    Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), ya rasu a hatsarin mota. Gwamnatin Jihar Gombe ce, ta sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Watsa Labarai, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Juma’a. Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri Sanarwar ta ruwaito cewa Bello ya rasu a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe, bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota. “Gwamnatin Jihar Gombe na cikin jimamin sanar da rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), sakamakon a hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Malam Sidi...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa 774, inda ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta yalwar abinci a fadin jihar. An gudanar da kaddamarwar ne yayin ziyarar Mrs. Uju Rochas-Anwuka, mai bai wa Shugaban Kasa shawara ta musamman kan lafiya ( Karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), wacce ta je Jigawa domin kaddamar da shirin Nutrition 774 da ke karkashin shirin sabunta kudurori na Renewed Hope Agenda. Gwamna Namadi ya bayyana cewa Jigawa ta kasance gaba a yaki da matsalar, tare da kafa shiri na musamman da aka yi wa lakabi da Masaki tun a 2020 domin fadakar da al’umma a...
    ‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet” Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da kuma wasu na’urori da suke amfani da su a yaudarar mutane. A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan kasar ta Ghana su ka sanar da kai farmakin a birnin Accra a ranar Laraba 22 ga watan nan na Oktoba. Shekarun mutanen da ake amfani da su wajen yaudarar mutane ta hanyar internet suna a tsakanin 18 zuwa 26,tuni kuma an kai su...
    Kungiyar ‘yan wasan kokawar Iran na gargajiya na matasa ‘yan kasa da shekaru 23, ta lashe kambun duniya bayan da ta samu lambobin yabo mafi yawa. Kungiyar ta Iran ta sami lambobin zinariya 3, da azurfa 1 da kuma tagulla 2. ‘yan wasan da Iran da su ka sami kyautar zinariyar sun hada Iman Muhammadi mai ajin nauyi kilio 72, da Gulam Ridha Farakhi mai ajin nauyi kilo 87 da kuma Fardin Hidayati mai ajin nauyi 130. Wanda ya  sami azurfa kuwa shi ne Sajjad Abbaspur mai ajin nauyi kilo 60, sai kuma wadanda su ka sami tagulla da su ne Ahamd Ridha Muhsin Najad mai ajin nauyi 67,sai Abul Fadal Muhmadim ai ajin nauyi 82. Kungiyar ta Iran ta...
    Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince a rika sauya kuɗaɗe da aka ware wasu wurare zuwa swasu idan can ya fi na farko amfani ga al’umma (virement) na naira biliyan 526 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 12 na bana, Gwamna Ahmad Aliyu, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na da cikakken ƙuduri wajen gina Jihar Sokoto mai ingantaccen tattalin arziki ta hanyar aiwatar da muhimman sauye-sauye da shirye-shiryen ci gaban al’umma. Gwamna Aliyu ya bayyana cewa wannan sauyin kasafi an tsara shi ne domin ƙarfafa zuba jari a fannoni masu muhimmanci kamar gina manyan ayyukan raya kasa, inganta ayyukan jin kai, da haɓaka tasirin gudanar da ayyuka — ba tare da ƙara girman...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci takunkumin maimakon mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin malla. “Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, domin hakan ya yi hannun riga da maslahar Iran. Amurka da kawayenta, wadanda ake kira da E3, sun  ki amincewa da wani daftarin kuduri daga Rasha da China, wanda ya nemi jinkirta aiwatar da tsarin dawo da takunkumai kan Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta  JCPOA. Pezeshkian ya kara da cewa Amurkawa “suna son mu ba su dukkan sinadarin uranium da aka tace, wanda ba za...
    Fitaccen ɗan wasan tamaula, Lionel Messi, ya tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar Inter Miami har zuwa shekarar 2028, kamar yadda kulob ɗin ya sanar a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025. Wannan sabon kwantiragin zai bai wa kulob ɗin da ma gasar MLS ta Amurka damar ci gaba da kasancewa tare da ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan da duniya ta taɓa gani har zuwa ƙarshen kakar wasa ta 2028. An kashe manoma uku da suke girbin amfanin gona a Filato Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe A ƙarshen wannan kakar ce kwataragin ɗan wasan na ƙasar Argentina zai ƙare, inda ya bayyana farin cikin sabunta shi kamar yadda wani saƙo da kulob ɗin ya...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran wanda ya gana da tawagar masu shirya taron tunawa da Alamah Mirzai Na’ini ( R.A), ya ce; muhimman siffofi biyu da malamin ya kebanta da su, su ne kirkira a fagen ilimi da kuma a cikin ilimin siyasa. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana Allamah Na’ini a matsayin daya daga cikin fitattun malamai, masu tarin sani a cikin jami’ar Najaf mai tsohon tarihi; jagoran juyin na Iran ya yi ishara da yadda marigayin malamin ya samar da ka’idojin da aka gina ilimin usulu akansu, wanda ya kai ga sabunta shi. Daga cikin rukunonin tunanin Allamah Na’ini kamar yadda jagoran juyin ya ambata da akwai batun kafa tsarin musulunci akan ginshikin wilaya domin kalubalantar...
    Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira  ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu. Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa...
    Sama da yahudawa 450 daga sassa daban daban na duniya ne suka yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran shuwagabannin kasashen duniya da su kakabawa gwamnatin Isra’ia takunkumin saboda kisan kare dangi da nuna rashin dan adamtaka da ta yi kan alummar gaza. Acikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta sun bayyana cewa ba mu manta da cewa mafi yawancin dokoki da sharudda da kuma yarjeniyoyi da aka kafa an yi su ne don kiyaye da kuma kare rayukan yan adam, kuma don mayar da martani ga kisan yahudawa da aka yi na holocus. Wasikar ta bukaci a girmama hukumcin da kotun kasa da kasa  ta fitar da ta hana aikawa da isra’ila makamai, sanya takunkumi ga duk wanda...
    Aƙalla shugabanni 15 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Zamfara sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).   An gabatar da waɗannan waɗanda suka sauya shekar ne a gaban Ministan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Dr. Bello Mohammed Matawalle, a Abuja ranar Laraba, ta hannun Shugaban APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Umar Danfulani, tare da Sanata Tijjani Yahaya Kaura da Alhaji Lawal M. Liman.   A cewar wata sanarwa da Mai Magana da yawun jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, Minista Matawalle ya tarbi sabbin ’yan jam’iyyar da farin ciki, inda ya tabbatar musu da daidaito da damar ci gaba da aiki a cikin jam’iyyar.   Dr. Matawalle ya bayyana matakin da suka...
    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zabe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba. Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 “Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin...
    Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki.   A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na binciko albarkatun ma’adanai na jihar don haɓaka tattalin arzikin cikin gida mai ɗorewa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025 Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta...
    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin a cikin shekara mai zuwa. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 Ko Alassane Ouattara zai samu wa’adi na 4 a mulkin Ivory Coast? Dangote ya ce wannan mataki kwatankwacin irin yadda aka gudanar sayar da hannun jarin kamfanononin siminta da suga na Dangote ne. “Ba ma son mu riƙe fiye da kashi...
    Kotun kasa da kasa ta ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin kasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasdinawa a Zirin Gaza. Kotun na mai bayyana cewa akwai wajabci kan Isra’ila na bayar da damar shigar da taimako cikin sauki zuwa yankin, sannan ya zama wajibi ta guji yin amfani da yunwa a matsayin makamin yaki. Kotun ta kuma bayyana cewa Isra’ila na da wajabcin hada hannu da kungiyoyin agaji na MDD, musamman Unrwa. Babban zauren MDD ne ya bukaci kotun ta bayyana ra’ayinta kan lamarin bayan da Isra’ila ta haramta ayyukan hukumar bayar da agajin jin kai ta falasdinawa cewa da Unrwa, tana mai zargin hukumar da hada kai da kungiyar Hamas. Share...
    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin tafiya Isra’ila cewa, ” wannan ba wani abu ne da za mu iya ba da goyon baya gare shi ba a wannan lokaci.” Furin nasa na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’a kan samar da wani kudirin mallake Gabar Yamma da Kogin Jordan a matsayin yankin Isra’ila. Kudirin wanda wani dan majalisar Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi ya gabatar na zuwa ne...
    Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar. Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan Oktoba. Kafin nan gwamnatin Kamaru ta haramta taron jama’a a birane da dama daga jiya Laraba, gabanin sanar da sakamakon zaben, biyo bayan da madugun ‘yan adawa na kasar Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Tun a makon da ya gabata ne magoya bayan Issa Tchiroma, wanda bisa ga kidayar tasa, ya ce ya samu kashi 54.8%...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026.   Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ’Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji  zai shafi rayuwar...
    Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba da inganta shi. Wannan fasaha wacce ta kara jaddada matsayin kasar Sin na ci gaba da zama jagora a fagen kere-keren jirgin kasa mafi gudu a duniya, ba kasar Sin kawai za ta amfanar ba har ma da sauran sassan duniya musamman a wannan zamani da kasar ta Sin ke kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma neman cimma burin samar da al’umma mai...
    Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.   Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya...
    Bam din Mark 84 kirar Amurka shi ne ya kashe dubunnan mutane a Gaza a hare-haren kisan kiyashi da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai Bama-bamai na Mark 84 da Amurka ta kera ba su buƙatar karin haske, lallai sun kasance abin da ya fi daukar hankalin duniya a lokacin kazamin yakin da aka yi a zirin Gaza, saboda barnar da suka yi da kuma kashe-kashen jama’a da ba a taba gani ba. Wadannan bama-bamai su ne suka fi yaduwa a fagen yakin Gaza, kuma sun fi barna da halaka a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare kan al’ummar Gaza. Tunawa da su yana da alaƙa da mummunan kisan kiyashi da al’amuran zubar da jini da suka girgiza duniya....
    Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma’adinai a fadin jihar. A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar, ya bayyana cewa wannan muhimmin shiri na gwamnatin yanzu babban mataki ne na gaba wajen cika alkawarin gwamnati na ganowa da kuma amfani da albarkatun kasa masu tarin yawa da ke cikin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan bincike zai samar da bayanai masu muhimmanci game da ma’adinai, da mmn fetur da iskar gas da ke karkashin kasa, wanda zai taimaka wajen yanke shawara mai...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya. Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar kuɗi a Ilori. A cewarta, za a raba Naira Biliyan biyar da miliyan dari shida ga tsoffin ma’aikatan jiha a matsayin giratuti, yayin da aka ware Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyar domin tsoffin ma’aikatan kananan hukumomi. Dakta Nuhu ta jaddada cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da biyan fansho da giratuti a hankali domin tabbatar da cewa sauran ayyukan...
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Shugaban kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya bayyana cewa, ya bayyana cewa Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya zubar da jinin mutanen yankin yammacin Asia da dama, amma wannan bai bashi lamunin cewa haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) zata zauna lafiya a yankin nan gaba ba. Tashar tal;abijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a jiya Talata a wani bikin kaddamar da littafi wanda yake bayyana ra’yin Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaie dangane da wakoki da kidekide. Yace: Duk tare da zubar da jinin mutanen yankin a duk a lokacinda ya ga dama, Netanyahu ba zai ce yana da lamuni na zaman lafiya ga HKI a nan...
    A cikin jawabin da ya gabatar a wannan Talata da aka nuna kai tsaye a taron jana’izar  babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Yemen  Laftanar Janar Mohammed al-Ghamari, Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa, kasar Yemen za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin komowa ga ayyukan soji idan Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta koma kisan kare dangi, da kuma ci gaba da killace yankin zirin Gaza. Sayyed al-Houthi ya yi ishara da irin babban gangami na dubban daruruwan mutane da suka taru a wurin jana’izar shahid al-Ghamari a matsayin abin da ke nuni da tsayin daka na al’ummar Yemen a kan manufofinsu. Sayyed al-Houthi ya kuma yi nuni da cewa al’ummar Yemen sun gamsu da matsayi mai Daraja da suke a...
    Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa. Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin. Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki. “A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar. Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali. Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar...
      “Wadanda aka nada sun bayyana a gaban kwamitin don tantancewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025,” in ji shi. “Kwamitin bai samu koke ko korafe-korafe ba a kansu, sun nuna shiri da cancanta akan ayyukan da aka zabo su”.   Ya bayyana sunayen wadanda aka tantance a matsayin: “Aminu Yusuf (Jihar Neja) – Shugaba, Joseph Haruna Kigbu (Jihar Nasarawa) – Kwamishina, Tonga Betara Bularafa (jihar Yobe) – Kwamishina. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025 Manyan...
    Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu. Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi. Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai...
    Kasashen Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da mai baiwa kasar Iraki shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji sun bukaci kasashen duniya da su dakatar da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza. Al-Araji, wanda ke jagorantar wata tawagar jami’an tsaro a kasar Iran, ya gana da Araghchi a yammacin jiya Litinin, inda suka yi musayar ra’ayi da su kan hanyoyin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma tattauna halin da ake ciki a Gaza da Lebanon. Dukkan jami’an biyu sun bayyana damuwarsu kan yadda Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude...
    Bayanai daga Falasdinu na cewa a kalla Falasdinawa 97 ne sojojin Isra’ila suka kashe tare da jikkata wasu 230 tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga watan Oktoba. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce ‘yan mamayar  sun aikata laifuka 80 tun bayan ayyana tsagaita bude wuta, wanda hakan ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa. Laifukan sun hada da harbin bindiga kai tsaye kan fararen hula da gangan, da kama fararen hula. A cewar sanarwar, sojojin na Isra’ila sun yi amfani da motocin soji, tankunan yaki da aka jibge a gefuna da wuraren zama, da jirage marasa, lamarin da...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a. Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da karfafa harkokin kasuwanci da zamantakewa a yankin. Haka kuma, gwamnan ya bude sabuwar cibiyar kula da lafiya ta farko, da makarantar Tsangaya ta zamani, da kuma rukunin samar da ruwa a yankin. Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin Gwamnati da Jama’a hanya ce ta karfafa gaskiya, bayyana ayyuka da kuma baiwa jama’a damar fadin  ra’ayoyinsu. “Mun zo ne mu nuna abin da muka...
    NLC ta kuma buƙaci gwamnati ta bi shawarar UNESCO wacce ta ke cewa ya kamata a ware aƙalla kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗi na kowace shekara ga ilimi. Ajaero, ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin makonni huɗu, NLC za ta haɗa dukkanin ma’aikata na ƙasa don gudanar da yajin aiki na ƙasa baki ɗaya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025 Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a October 20, 2025
    Wata kotun majistare da ke Kano ta umarci Hukumar Hisbah ta jihar da ta shirya ɗaura aure tsakanin wasu fitattun ’yan TikTok guda biyu — Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda — cikin kwanaki 60. Kotun ta bayar da wannan umarnin ne bayan yaɗuwar bidiyon Mai Wushirwa da ’Yar Guda a kafafen sada zumunta, da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayyana a matsayin “na batsa da rahsin tarbiyya.” Bidiyoyin sun nuna waɗannan ’yan TikTok ɗin suna nuna soyayya a bainar jama’a, abin da hukumomi suka ce ya saɓa da ɗabi’u da koyarwar addini da al’adun mutanen Jihar Kano. A yayin zaman kotun ranar Litinin, Mai Shari’a Halima Wali ta yi gargaɗi cewa idan ba a ɗaura auren...