2025-09-17@20:32:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1214

«goyon bayan kafa kasar»:

    A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai. Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu. Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina...
    Gwamnatin  kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI don kwatar kasarsu da ta mamaye. A cikin wani bayanin da ma’aikatar harokokin wajen kasar Iran ta fitar a yau Laraba, Jumhuriyar Musulunci ta Iran, tana kara jaddada goyon bayanta ga al-ummar Falasdina, kuma tana kara jaddada tir da allawai da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza da kuma sauran yankunan falasdinawa da ta mamaye. Kuma tana godewa mutanen kasar Iran...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ilBagaei ya yi tir da samar da duk wata hulda da HKI sannan tana ganin yin haka yana dai-dai da taimaka mata ko halatta mata ayyukan ta’addancin da take aikatawa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran Tasnem na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana fadar haka a yau Laraba, a taron mako-mako da ya saba a ma’aikatsa a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, Iran tana kira ga dukkan kasashen duniya musamman kasashen yankingabas ta tsakiya da su kauracewa Haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ko ta ina. Ya ce kasashen musulmi da dama, har ma da wasu wadandaba musulmi ba sun dade da katse dangantakarsu da haramtacciyar kasar, babu dangantakar diblomasiyya babu na kasuwanci da...
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno. Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin. DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna. “A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki...
      Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu mutum shida sun shiga hannun ’yan sanda kan zargin satar zinari da kuɗinta ya haura Naira miliyan 109.5 a Jihar Kebbi. Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda a jihar Kebbi na tuhumar su da sace sarkoƙin zinare guda biyar sauran kayan zinare daga wani gida a garin Ka’oje, Ƙaramar Hukumar Bagudo. Sauran sun haɗa da zobba huɗu da munduwar hannu tara, da nauyinsu ya kai gram 782.7 — dukkansu mallakar ’ya’ya da ’yan uwar mai gidan. Wanda ake tuhuma ya amsa laifi Bayan samun koken, jami’an suka kama Ibrahim Abubakar Ka’oje, jami’i a Hukumar Gyaran Hali ta Kasa, wanda a yayin bincike, ya amsa laifin. ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote...
    “Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.   Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.   Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin ne dai kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa su ka yi taron gaggawa a birin Doha na kasar Qatar da aka tattauna harin wuce gona da iri da HKI ta kai wa kasar. Bayanin bayan taron ya kunshi bangarori mabanbanta da su ka hada da daukar matakai kwarara domin taka wa HKI birki akan ta’addancin da take yi, da kuma hanyoyin kare kai anan gaba.  Kungiyar kasashen larabawan yankin tekun fasha ta sake jaddada muhimmancin aiki da dokar kafa rundunar hadin gwiwa ta kare kai daga duk wani wuce gona da iri daga waje. Bugu da kari, mahalarta taron sun amince da dukar dukkanin matakan dokoki a fagen duniya domin hukunta jami’an HKI da su ka tafka...
    Ya ƙara da cewa ‘yan’uwa da abokan arziƙi da suka shirya wannan biki na karrama Farfesa Armaya’u Bichi tare da bashi lambar yabo tare da wasu muhimman mutane waɗanda suka taimaimake shi wajen gudanar da shugabanci sun kyauta sannan sun ajiye ƙwarya a gurbinta.   Shima da yake gabatar da jawabinsa, shugaban riƙo na jami’ar gwamnatin Tarayya dake Katsina (FUDMA), Farfesa Aminu Ado ya ce Bichi mutum ne mai jin tausayin al’umma musamman mutanen dake ƙarƙashinsa.   Farfesa Ado ya ce har ƙasa ta naɗe ba zai mance da irin gagarumin ci gaban da Farfesa Arma’yau ya kawo ma jami’ar FUDMA ba.   Haka kuma a yayin bikin an ƙaddamar da littafin waƙoƙin da wasu mawaƙa suka yi wa tsohon...
    Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin. Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta. Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO Hilda Baci dai ta dafa shinkafa dafa-duka mafi yawa a tarihi tare da sauran kayan haɗi da sunadaran ɗanɗano wadda nauyinta ya kai kilo 8,780 a yankin Victoria Island da ke Legas. A shekarar 2023 Hilda mai shekaru 28 ta shiga Kundin Bajinta na Guiness World Record bayan shafe...
      Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.   A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi. A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025. KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja Ya bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso. Wani mutum mai suna Mahamadou Noura...
    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona. Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar. Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka...
    Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana. Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano inda ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyoyin biyu suka shaidi wasan. Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa Kafin yanzu ƙungiyar, mallakar gwamnatin jihar Kano ta yi rashin nasara biyu sannan ta buga canjaras ɗaya a wasanni uku da ta buga a wannan kakar, wannan nasarar da Sai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16, wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement....
    An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su. A ranar 8...
    “Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana da muhimmiyar ma’ana a fannin warware matsalolin da suka shafi tsarin shugabancin duniya a yanzu. A halin yanzu, sauyin karfi a tsakanin kasashe masu ci gaba da ma kasashe masu tasowa shi ne sauyi mafi girma da aka samu a sabon zamanin da muke ciki a fagen kasa da kasa, inda tarin kasashe masu tasowa suka bunkasa da sauri. To sai dai kuma tsarin duniya...
    Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan  ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba; LIVERPOOL Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan  ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan  wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da...
    Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Kayan da aka bayar sun haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da kuma tufafi, kayan mata da shadda. Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin gaggauta tallafa wa al’ummar...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
    Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi. Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su. Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da...
    A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata. Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba ne masu shirya jerin gwano a birnin Auckland, na kasar suka bada labarin cewa wannan shi ne tattaki mafi girma wanda aka gudanar a cikin kasar don goyon bayan al-ummar Falasdinu tun lokacin da aka fara yakin kimani shekaru biyu da suka gabata. Wadanda suka shirya zanga zangar sun bayyana cewa mutane kimani 50,000 suka fito wannan tattakin na goyon bayan Falasdinawa a Gaza, da...
    Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci  shawara Ali Vilayati  ya yi allawadi da kasar Azerbaijan kan shirya taron yahudawan turai a kasar a cikin watan Nuwamba mai zuwa, kuma ya bayyana taron a matsayin tsokanace ga musulmi da kuma addinin musulunci, kuma ba zai je ko ina ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Vilayati yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa , wannan shi ne karon farko wanda aka taba gudanar da taron yahudawan duniya a birnin Baku na kasar Azerbaijan, kasa ta musulmi shia. Ya ce, wannan shi ne karon farko wanda aka gudanar da taron yahudawan duniya a kasar musumi shia, kuma kowa ya san cewa, taron tsokanane...
    Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda ka samu kasashe 142 suka kara kuri’ara amincewa yayin da kasashe 10 kuma sun nuna rashin amincewa sai kuma guda 12 da suka kauracewa kada kuria. Wannan daftarin kudurin ya nuna irin yadda duniya ke goyon bayan kafa kasar palasdinu adaidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza, yayin da duniya ke ci gaba da yin tir da cin zarafi da take hakkin dan adam a gazan, Duk da yake cewa wannan daftarin kudurin ba dole ba ne amma ya kara wa matakin kima a siyasance, kuma ya kara jan...
    Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya ce kasarsa na goyon bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Shugaba Vucic ya bayyana haka ne yayin da yake hira da wakilin CMG a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, inda ya ce tsarawa da gabatar da wannan shawara mai ma’ana, ya zama wani abun da ya wajaba, saboda da farko, a zamanin da ake ciki, ana bukatar samar da karin ikon wakilci ga kasahe masu tasowa a fannin kula da al’amuran kasa da kasa. Kana na biyu, yanzu sannu a hankali ana lalata sakamako da nasarorin da dan Adam ya samu ta fuskar dokoki da ka’idoji na kasa da kasa, yanayin dake bukatar...
    Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani matsayin da yawancin mambobin PDP ba sa jin daɗinsa. Kafin yanzu, jam’iyyar ta shiga cikin wata babbar matsala kan matsayin sakatare jam’iyyar na ƙasa, tsakanin Samuel Anyanwu, wanda Wike yake goyo baya, da Sunday Ude-Okoye, wanda yake samun goyon bayan Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah. Mafi yawancin shugabannin jam’iyyar sun yi tunanin cewa idan har Anyanwu ya dawo a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa zai...
    Chef Hilda Baci mai shekara 28 ta kama hanyar kafa sabon tarihin girka shinkafa dafa-duka (Jollof) ’yar Najeriya mafi yawa a duniya. Hilda Baci ta kafa wannan sabon tarihi ne inda ta girka shinkafa basmati buhu 200 a wata katafariyar tukunya a bainar jama’a. Ta yi wannan sabon abin bajinta ce shekara biyu kacal bayan ta shiga kundin tarihi na duniya na Guinness a matsayin wadda ta shafe awanni mafiya yawa tana girke-girke a duniya. A ranar Juma’a ta fara girkin a otel ɗin Eko Hotel & Suites, da ke Legas, kuma sama da mutum 20,000 mashahurai da sauransu sun yi rajista don halarta. An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Abba ya tarbi tagwayen da...
    Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da “Sanarwar New York” da nufin farfado da shawarwarin samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya  wato Isra’ila, da kuma Falasdinu a daya bangare – amma ba tare da kungiyar Hamas ba. Kasashe 142 ne suka amince da shi, yayin da 10 suka nuna adawa da shi (ciki har da Isra’ila da Amurka) sai 12 da suka kaurace kada kuri’ar. . Bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, kasashe da dama sun bayyana aniyarsu ta daukar irin wannan matakin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a bude ranar 22 ga watan Satumba, ana kallon wannan tsari a matsayin karin tursaswa Isra’ila ta kawo karshen yakin da take ci...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa  fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
    Ya ƙara da cewa a faɗin Afirka, bashi ya zama babban ƙalubale ga tattalin arziki, inda ƙasashe da dama ke kashe fiye da kuɗin kiwon lafiya wajen biyan bashin da suka ci. Ya ce kashi 35 cikin 100 na bashin ƙasashen Turai na daga masu ba da rance masu zaman kansu ne, kashi 39 daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa irin su IMF da Bankin Duniya, kashi 13 daga ƙasashen da ke bayar da rance kai tsaye, yayin da kashi 12 daga Ƙasar China. Abbas ya bayyana cewa Nijeriya ta kuduri aniyar jagorantar kafa tsarin duba bashin ƙasashen Yammacin Afirka ƙarƙashin WAAPAC, domin daidaita rahotanni, samar da ƙa’idojin gaskiya da bayyana bayanai, tare da bai wa majalisu damar samun bayanai cikin lokaci...
    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama buhu 150 maƙare da tabar wiwi a yayin da ake tsaka aikin ceto bayan wani hastarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano. Hukumar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne tsakanin wata mota ƙirar Volkswagen Golf da wata babbar mota a yankin Gadar Tamburawa da ke Jihar Kano. Kakakin NDLEA na Jihar Kano, ASN Sadiq Mohammed Maigatari, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin da aka ceto ya yi ƙoƙarin tserewa amma an yi nasarar kama shi. Ya ce a yayin bincike ne aka gano buhuna 150 na tabar wiwin wanda nauyinsu ya kai kilogram 112. Abba ya tarbi tagwayen da aka raba...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja An yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman. Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta...
    Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta raba kayan tallafi ga al’ummar Jalingo-Kamo da ambaliyar ruwa ta shafa a Karamar Hukumar Kaltungo, inda iftila”in ya shafi gidaje kimanin 90. Rabon kayan ya biyo bayan umarnin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya amince da bayar da kayan abinci da na masarufi domin rage raɗaɗin da jama’ar da abin ya shafa suke ciki. NAFDAC ta kama jabun maganin maleriya na ₦1.2bn a Legas Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo Yayin rabon kayan a fadar Hakimin Jalingo-Kamo, Sakataren Hukumar SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna Abdullahi ya ce sun gudanar da cikakken bincike da ƙirga waɗanda abin ya shafa kafin rabon. Abdullahi ya bayyana lamarin...
    A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin.   An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
    Shugaban kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai kan kasar Yemen a ranar Laraba ba ta nuna wata nasara ba, sai dai yana nuna rashin bin dokokin kasa da kasa wajen ci gaba da aikata laifukan yaki. A cikin jawabinsa na mako-mako a wannan Alhamis, yayin da yake magana kan sabbin abubuwan da suka faru dangane da hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma abin da ya biyo bayan hakan,  Sayyed al-Houthi ya bayyana cewa, kasar Yemen, a hukumance da kuma a matsayi na al’ummar kasar, tana a kan matsaya ta gaskiya, tana taka muhimmiyar rawa, kuma tana da cikakkiyar fahimtar abin da take aiwatarwa na sadaukarwa domin al’ummar...
    Gwamnatin jihar ta sha alwashin bayyana sakacin aikin da Kwamishinan ya yi da zarar ta kammala bincike.   Don haka, an umurci  babban jami’i a ma’aikatar da ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatar har zuwa lokacin da za a fitar da wata sabuwar sanarwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban hafsan sojojin kasar Iran ya bayyana goyon bayan sojojin kasar Iran ga kasar Qatar, bayan hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha na kasar a ranar laraba a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar hamas na kasar Falasdinu da ta mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Mousavi yana fadar haka a yau, ya kuma bayyana cewa wannan matakin ya zo dai-dai da akidar kasar na tallafawa duk wanda yake gaba da HKI a yankin ko a wani wuri. Janar Musavi ya kara da cewa, muna son shaidawa gwamnatin kasar Qatar kan cewa, sojoji da gwamnatin JMI suna tare da ita har zuwa karshe. Musavi ya ce: Kowa ya sani, kamar yadda shugaba Pezeshkiyan...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya sabon wa’adin kwana ɗaya domin ta cika buƙatun da take nema. Hakan dai na zuwa ne bayan wa’adin farko na kwanaki 10 da suka bayar, wanda ya ƙare a ranar Talata, 10 ga Satumba. An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Matakin da ƙungiyar ta ɗauka na zuwa ne a ƙarshen wani taron gaggawa da shugabanninta suka gudanar a ranar Laraba, domin nazarin ci gaban da aka samu tun bayan bayar da wa’adin farko. Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a...
    Daruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP ne suka taru a birnin Kalaba na Jihar Kuros Riba, domin tarbar jagoran jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a wata ziyarar sada zumunta da ya kai a jihar. Kwankwaso ya fara irin wannan ziyarar ce daga yankin Kudu maso Gabas, kafin ya wuce zuwa Kudu maso Kudu, inda ya sauka a Kalaba domin ganawa da mambobin jam’iyyar. Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 Trump ya tiso ƙeyar rukunin farko na ’yan Najeriya daga Amurka A yayin da yake jawabi ga taron magoya bayan jam’iyyar a Kalaba, tsohon Gwamnan Kano, ya bayyana cewa wannan ziyara ba ta da alaƙa da yaƙin neman zaɓe. Sai dai ya ce uzuri ne ya kai shi...
    Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Nijeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki. Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki,...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa. Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa da ya dada aiwatar da matakan da za su kara karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya. Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da cewa an rage farashin sufurin kayan amfanin gona ba tare da kashe makudan kudade ba. “Shugaban Kasa ya bayar da umarni ga Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa wanda dama yanzu haka yana nan yana kokarin ganin an saukaka hanyoyin sufurin amfanin gona a fadin kasar nan, da su dada...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa takaitacce hadin kai ta bawa hukumar IAEA a yarjeniyar da ta cimma da Gorris a birnin Alkahira. Ya nuna irin hakurin da JMI ta nuna bayan hare-haren da aka kai mata kan cibiyoyin Nukliyar kasar . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau a shafinsa na X kan cewa, Iran ta amince da takaitaccen aiki da hukumar IAEA ne saboda dole ne ya zamanto ana kula da ayyukan nukliyar kasar ko da takaitacce ne. Sannan ya ce kasar tana son ci gaba da raya yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015. Ya ce, Iran ta amince da wannan takaitaccen yarjeniya ne bayan ta...
    Gwamnatin kasar Iran ta yi tir da hare-haren da HKI ta kai helkwatan kungiyar Hamas a Doga, ta kuma kara da cewa wannan wani sako ne ga kasashen yankin na su yi shirin kare yankin ko kuma zasu ga abinda ya fi haka nan gaba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani yan fadar haka a shafinsa na X. Ya kuma kara da cewa: Hare-haren Qatar gargadi ne na bainda zai zo nan gaba. A na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya rubuta a shafinsa na X kan cewa, abinda HKI ta yi a doha baa bin mamaki bane a waje na’ sannan ya...
    Wata kotu da ke ƙasar Ghana ta yanke wa ’yan Najeriya uku hukuncin ɗaurin shekaru 96, bayan samun su da laifin satar mota a birnin Kumasi na ƙasar. Kotun dai ta samu Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze ne da laifin a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke neman a kori ’yan Najeriya daga kasar saboda aikata laifuka. Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a Gombe Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Mai magana da yawun ’yan sandan yankin Ashanti na ƙasar, Godwin Ahianyo, ne ya bayyana yanke hukuncin a cikin wata sanarwa ranar Talata. Sanarwar ta ce an kama mutanen ne ranar 20 ga watan Yuni bayan an zarge...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta kalubalantar ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hadin kai tsakanin kasashen musulmi Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, yayin da yake tsokaci kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar, ya bayyana cewa, hanya daya tilo da za a bi wajen kalubalantar mummunar dabi’ar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hada kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmi. Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X a yammacin ranar Talata cewa: “Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata wani mugun aiki kan Iran da ba za a iya tunani ba, a halin yanzu kuma ta kai hari ga al’ummar Qatar...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka tabbatar. An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi Makama wanda kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya ne ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne sanye da hijabai da rigunan mata da suka yi basaja da su, inda suka yi awon gaba da...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta gabata, domin jajanta wa al’umma bisa hare-haren da ’yan bindiga ke kai musu. TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen daƙile matsalar ’yan bindiga a faɗin jihar, inda ya buƙaci mazauna ƙauyuka su riƙa tona asirin duk wanda suka sani yana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya sun shiga taraddadin abin da ka iya biyo bayana kudurin Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NPENG) na tsunduma yajin aiki.   Hakan dai ya biyo bayan tashi da aka yi daga zaman da Gwamnatin Tarayya ta kira don sasanta kungiyar, mai samun goyon bayan sauran kungiyoyin kwadago, da rukunin kamfanonin Dangote, ba tare da cimma wata matsaya ba. NAJERIYA A YAU: Yadda Ilimi Ke Ƙara Tsada Yayin Komawar Yara Makaranta DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Ministan Kwadago Muhammadu Dingyadi ne dai ya kira taron, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin NUPENG da NLC da TUC da na Dangote...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
    Ƴan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Wake da ke ƙaramar hukumar Kachia, jihar Kaduna, inda suka kashe mutum takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama. Bayanan farko sun nuna cewa waɗanda suka samu raunuka a harin an garzaya da su Asibitin Katolika na Saint Gerard domin samun kulawar likitoci. Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina Gwamnatin Katsina Za Ta Sayo Babura 700 da Motoci 20 Don Samar Da Tsaro Duk da cewa cikakkun bayanai kan lamarin ba su fito fili ba tukunna, majiyoyi sun tabbatar da faruwar harin. Sai dai duk wani yunƙuri na jin ta bakin jami’an ƙaramar hukumar Kachia bai samu nasara ba, domin sun ce za su...
    Ali Akbar Vilayati mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aya. Khaminae ya bayyana cewa, yenci da kuma zaman lafiya da tsaron JMI yana da matukar muhimmanci ga kasar Iran. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wilayati yana fadar haka a lokacin da yake ganawa da Ammar Hakin shugaban Jam’iyyar Hikma na kasar Iraki wanda yake ziyarar aiki a nan Iran a yau Lahadi. Wilayati ya kara da cewa kasashen Iraki da Iran suna da dangantaka mai muhimmanci tsakaninsu wanda ya hada da na addini da al-adu ga kuma makobtaka. Yace Iran tana jin dadin ganin Iraki tana samun ci gaba da kuma zaman lafiya mai dorewa a karkashin jagorancin malaman addini...
    Alamomin Basir Bayyanar alamomin Basir, ya danganta ga wane irin Basir ne ya bayyana, Basir cikin dubura ko kuma Basir a wajen dubura? Alamomin Basir Cikin Dubura: 1- Zubar jini ba tare da jin ciwo ba, a yayin tsuguno. 2- Basir mai tsiro, wanda ke fitowa wajen dubura; har sai an tura da yatsa, domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da radadi. Alamomin Basir A Wajen Dubura: 1- Ciwo mai radadi 2- Kaikayi 3- Kumburi a kewayen dubura 4- Zubar jini yayin yunkurin tsuguno Abuban da ke kawo Basir: Basir na faruwa ne sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura, har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka: 1- Yawan yunkuri yayin tsuguno 2- Tsawaitar lokacin...
    Hajiya Sa’ah ta kuma bayyana cewa ita wannan ƙidaya da yin rajistar haihuwa, aure da sauran su, abubuwa ne masu muhimmanci da za su taimaka wa gwamnati ta san yawan su, ta yadda za su sami nasarar ci gaba da lasar romon Dimokraɗiyya mai yawa, musamman a bangaren ilmi, lafiya da dai sauran abubuwan more rayuwa.   Daga nan ne ta jinjina wa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da cewar jihar Kaduna ce jiha ta farko da gwamnan ta ya yi yunƙurin gabatar da wayar da kan al’ummar sa game da muhimmancin ƙidaya, kuma lallai yana bayar da cikakken goyon bayan sa a kan haka, inda ya ɗauki nauyin hakan a dukkan Ƙananan Hukumomin jihar.   A nasa jawabin,...
    Game da babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya kin tafarkin murdiya, wanda aka gudanar a ranar 3 ga wannan wata, mutane daga kasa da kasa masu halartar bikin sun ba da ra’ayoyinsu ciki har da kalmomin hadin kai, da yin kokari tare, da sauransu don nuna kyakkyawar fata ga makoma. Bayan shekaru 80 da gama yakin duniya na biyu, an canja burin dan Adam. Zaman lafiya da samun bunkasa sun zama babban jigo na halin yanzu, kasa da kasa suna kokarin samun zamanantarwa. Amma a sa’i daya kuma, ra’ayin mai karfi ya cinye maras karfi ya sake bullowa, an kawo illa ga...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dama sun bayyana bacin ransu kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi na bude “kofofin jahannama” a zirin Gaza. Wannan martanin ya zo ne a ranar Juma’a bayan da Isra’ila Katz ya ayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan na gab da maida yankin jahannama a gabar tekun. Katz, ya bayyana cewa sojojin Isra’ila za su zafafa kai hare-hare har sai kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta sako mutanen da aka kama. A nata bangaren, Hamas ta ayyana barazanar Katz a matsayin “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba ga dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.” Kalaman na Katz na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta riga ta ba da damammaki don ba...
    Ya kuma sanar da ci gaba da bai wa shugabancin Dakta Dantsoho goyon baya, musaman domin kara samar da sauye-sauyen da za su kara bunkasa hada-hadar zirga-zirga, da kuma a bangaren kara bunkasa kasuwancin tatalin azrki na Teku. A nan kuma Kamfanin Rukunonin SIFAD, ya taya Dakta Dantsoho murnar zama Mataimakin Shugaban na kungiyar ta IAPH. Hakan na kunshe ne, a cikin wata wasika da Shugaban Kamfanin Dakta Taiwo Afolabi CON ya fitar ta taya murnar, inda ya danganta zabar Dantsoho kan mukamanin a matsyin abinda ya dace, musamman duba irin salon shugabanci na gari na Dakta Dantsoho, wanda hakan ya sanya ya samar da gagarumar gudunmawa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar. Shugaban sashen samar da bayanai na...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.   “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.   “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC. FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta. 2027: ’Yan adawa na ƙoƙarin sanya APC fara kamfe da wuri — Tinubu Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa Ya ce ya mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya bisa ayyukan ci gaba da ya ke gudanarwa. “Marar kishin Gombe ne kawai ba zai ga nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ke samu ba,” in ji Umar FK. Ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa za su mara...
    Sama da mutane dubu ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a yankin Darfur na kasar Sudan Sama da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta hallaka daukacin wani kauye a yankin Darfur na yammacin Sudan, a wani lamari da aka bayyana a matsayin daya daga cikin bala’o’i mafi muni da aka taba fuskanta a tarihin Sudan a wannan zamani, a cewar kungiyar fafatukar ‘yantar da al’ummar Sudan (SLM) da ke iko da yankin. Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, zabtarewar kasa gaba daya ta lalata kauyen Tarsin da ke gabashin Jebel Marra, kusa da yankin Soni, tare da kashe daukacin al’ummarta, wadanda aka kiyasta sama da maza da mata da yara sama da...
    Domin ya ce wannnan matsala ce da ta shafi ƙasa, kuma ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanin halin da ƙasar ke ciki. A cewarsa wannan babban zargi ne, don haka bai kamata a manta da shi ta hanyar yin jawabi ba tare da wasu gamsassun hujjoji ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, kasar Iran zata dauki matakan maida martani ga matakin da kasashen E3 ko Faransa, Jamus da kuma Burtania, suka dauka na maida dukkan takunkuman tattalin arziki n a MDD kafinn yarjeniyar JCPOA. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a cikin Malisar dokokin kasar a nan Tehran.  Ya jami’an gwamnatin kasar Iran, da kuma kasashen Rasha da Chin duk sun bayyana cewa maida wadannan takunkuman tattalin arziki kan Iran baya bisa ka’ida kuma zalunci ne. Sannan ba tare da shawara da kowa ba kasashen uku suka dauki matakin aikawa MDD wasika wanda na sake farfado da takunkuman. Share 0 0...
    Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya kuma umarci da a maido da babban daraktan yada labarai, Mista Ayo Adewuyi ya kammala wa’adinsa na ragowar shekaru uku, wanda zai kare a shekarar 2027.   Shugaba Tinubu ne ya nada Adewuyi a shekarar 2024. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba. Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.” Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa...
    Hakan yana faruwa ne saboda yawan hormones “progesterone” da yake taruwa a jikinta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”. Shin wasu lokuta ne za ki tsammaci ganin farin ruwa a gabanki; Idan kin gani ba damuwa bane Yawanci mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar al’adarsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danko ya kan sake bullowa wanda zai yi kamar kwana 4 zuwa 5 kafin lokacin fitar kwayar alitta, alama ce ta kwayar alitta sun fara girma, ana kiransa da “follicular phase” that means a lokacin ne “eggs” (for obulation) suke kokarin girma. Idan kuma lokacin fitar ya yi, ruwan sai ya canza daga mai danko zuwa fari...
    Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba. Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum. A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin. Don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon Gwamnatin Tarayya da hukumar NEDC domin...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...
    Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza ya wuce kare kai, don haka dole ne a matsa lamba kanta don kawo karshen yakin da kuma bala’in jin kai. Ya ci gaba da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila na ruguza tsarin samar da kasashe biyu. A nata bangaren, jami’ar kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai, Kaja Kallas ta bayyana cewa: Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun dauki...
    Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan.   Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye.   Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu...
    Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu.   Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba.   Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka. A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya...
    A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a  cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD. Kasashen uku da aka fi sani da E3  sun ce a shirye suke su dage mayar da takunkumin har na tsawon watanni shida idan Tehran ta amince da sake baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga cibiyoyinta na nukiliya, tare da  magance abin da suka kira damuwar da suke da ita game da yawan tataccen sinadarin uranium da ta ke da shi, da kuma shiga tattaunawa da Amurka. Sabanin haka, jakadan...
    An sake samun damuwar kifewar jirgin ruwa a Ƙaramar hukumar Shagari inda jirgin ruwa ya nutse da mutane 12 a Ƙaramar hukumar ta Jihar Sakkwato wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu namiji da mace sauran 10 suka samu raununka. Hatsarin ya faru ne da daren ranar Alhamis a gulbin Shagari inda mutane suka shiga cikin damuwa da kaɗuwa kan jirgin daya nutse da mutane da babur guda biyu da sauran kayan amfani, a wata ɗaya jirgi uku ya nutse a ruwa a Sakkwato. Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa Nasir Umar wanda lamarin ya faru gaban idonsa ya ce, “jirgin...
    Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: Ina kiran mutanen Jamus kan cewa ku ne kuka samar da ikidar Nazi, a yayinda mu a kasar Italia da Spaine muka samar da akidar Fasim a nahiyar turai a baya, wana ya kai kasashen turai ga lalacewa.. Jami’ar ta bayyana haka ne bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro na Jamus suka yi kan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa wadanda kuma suke bukatar HKI ta...
      Haka kuma, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin tana son mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da kulla hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare tare da Amurka, bisa tabbatar da kare muradun ikon mallakar yankunan kasarta, da tsaro da kuma ci gaban kasar.   Ya kara da cewa, a shirye muke mu yi aiki tare da Amurka a kan turba guda, da aiwatar da muhimman yarjejeniyoyi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ci gaba da sadarwa a tsakaninmu, da warware batutuwan da muka sha bamban a kai, da fadada hadin gwiwa, da kuma ci gaba da lalubo hanyar da ta dace manyan kasashen biyu su tafi tare da juna a sabon zamani.   Jami’in ya...
    Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar. Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da ta hada kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni. An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ke kula da harkokin ruwa da su dauki matakin da ya dace kan wadanda lamarin ya shafa. Hakan...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
    A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare. Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen...
    Shugaban gamayyar masu goyon bayan Gwagwarmaya a kasar Lebanon suna tare da kungiyar sannan wadanda suke nanata cewa sai an takaita makamai a hannun gwamnati sun aiki ne wa HKI da Amurka . Tashar talabijan ta Al-Manar ta kungiyar ta nakalto shugaban gamayyar Mohammad Ra’ad yana fadar haka ya kuma kara da cewa abinda ya faru a ranar 5 ga watan Augustan mai karewa wani kuskure ne wanda gwamnatin kasar Lebanon bata taba irinsa ba. Kuma yana dai da kamar abinda ya faru a karbala ne, inda wani sojan yazid ya fadawa yan uwansa kan cewa ku shaida mani wanin nYazid kann cewa ni na fara harban kibiya kan Al-Hussain. Abinda gwamnatin kasar Lebanon tayi na neman yardar Amurka da...
      Kazalika, bukatu masu alaka da kayayyakin masarufi na ci gaba da farfadowa, yayin da manufar “maye tsoffin kaya da sabbi” ta haifar da matukar karuwar bukatun kayan lantarki da na’urorin bidiyo da sauti, da kuma kayan sadarwa. (Amina Xu)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan Majalisar Dattawan kasar Mexico sun yi naushe-naushe a ranar Laraba lokacin da muhawara ta yi zafi a zauren majalisar. Rahotanni sun ce an fara ba hammatar iska ne bayan shugabannin ’yan adawa a majalisar sun bukaci sojojin Amurka su shiga kasar su taya su yaki da dillalan miyagun kwayoyi. Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makare Shugaban marasa rinjaye a makalisar, Alejandro Moreno, shi ne dai ya je wajen yin jawabi a fusace bayan kammala zaman majalisar, inda ya tunkari shugaban majalisar, Gerardo Fernandez Norona, saboda hana shi damar yin Magana. A cikin wani bidiyo a kafafen sada zumunta dai, an ga...
    An kai shi asibiti, inda aka kula da shi sannan aka sallame shi domin halartar jana’izar iyalan nasa. Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Bello Garba, ya ce ba su samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma sun shirya gudanar da bincike kan lamarin. An binne mamatan bisa tanadin addinin Musulunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar gwamnati,” in ji shi. “Mun amince kan abubuwa da dama, sai dai shugabanninsu, Ma’aikatar Ilimi da Gwamnatin Tarayya ba su ɗauki mataki kan kowanne ba.” Ya danganta yawan ficewa daga Najeriya da malamai da likitoci ke yi saboda ƙarancin...
    Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja, bayan ya kammala ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce jirgin shugaban ƙasa ya tashi daga filin jirgin sama na Brasília a ƙasar Brazil da ƙarfe 12:57 na rana a ranar Laraba. A cewarsa ya iso Abuja da safiyar ranar Alhamis. Ga hotunan yadda wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbi shugaban:
    Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi Ruftawar katanga ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 2 a Zariya El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke...
      Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a.   Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya...
    Musiba da auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci. Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u da Aina’u Nuhu. Wani ɗan sanda ya harbe soja a Bauchi A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC Sai dai mijinta, wanda shi ma ya samu rauni a sakamakon faruwar lamarin, tuni an sallamo shi bayan duba lafiyarsa a asibiti. Wani maƙwabcinsu, Malam Ahmed, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asubahi,...
    Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar tun shekara ta 2023 da ta gabata Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar a ranar Talata, tun bayan barkewar yaki a kasar a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023. Kamfanin dillancin labaran Sudan ya bayar da rahoton cewa, “Gwamnatin bege” karkashin jagorancin fira ministan kasar Kamil Idris, “ta tattauna, a zamanta na farko na hukuma a birnin Khartoum bayan kafuwarta, game da tsare-tsaren ma’aikatun na wannan shekara, inda suka mai da hankali kan ayyukan jama’a da rayuwar jama’a, tsaro na ‘yan kasa, sake gina kasa, da tabbatar da dawowar ‘yan kasar da suka yi gudun hijira bisa radin kansu....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi. A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori wajen inganta hadin-gwiwar kasashensu a fannoni daban-daban. A yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka yi a watan Satumban bara a Beijing, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan daga matsayin huldar kasashensu, zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, al’amarin da ya kafa alkibla ga ci gaban dangantakarsu. Firaminista Li ya ce yana fatan...
    Kalli hotuna da bidiyo da sauran bayanai kai tsaye daga shafin Aminiya kamar kana wurin da ake gudanar da gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya ta 2025.