2025-11-04@07:20:06 GMT
				 
				 إجمالي نتائج البحث: 135
				 
                «a zaɓen fid da gwani»:
	An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
	An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
	An ture Mataimakin Gwamna Gefe, Tsarin karba-karba Na Goyon Bayan Kwara ta Arewa. Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak, zai kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2027, amma babu wata alamar cewa mataimakinsa, Mista Kayode Alabi, zai gaje shi. Yanayin siyasa a jihar na nuna cewa yankin Sanatocin Kwara Arewa ne ake sa ran zai samar da gwamna na gaba; Alabi yana daga Kwara Kudu. Kwara ta Arewa ba ta samar da gwamna da tun daga 1999, yayin da Kwara Kudu ta rike kujerar siyasa ta farko a jihar na tsawon shekaru takwas, kuma zuwa 2027 Kwara Tsakiya za ta kasance ta rike kujerar na shekaru 20. Masu nazarin siyasa guda biyu, Comrade Abdul-Rahoof Bello-Labelabe da Comrade AbdulLateef Ishowo, sun bayar...
	Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani. Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa. Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.
	Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar.   Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28, 2025  Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025  Labarai Tsohon Kwamishina...
	Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara. Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar...
	Rahotonni sun bayyana ɓarkewar zanga-zanga a birnin Douala, cibiyar kasuwancin Kamaru jim kadan bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar. Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a dandalan sada zumunta sun nuna gomman mutane sun fantsama kan titunan birnin, tare da rera waƙoƙin goyon bayan Issa Tchiroma Bakary, jagoran adawar ƙasar. An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru Kamfanin dillancin labaran Kamaru, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda aka lalata wani ginin majalisar birnin, bayan da masu zanga-zangar suka far masa. BBC ya ruwaito cewa, a yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar kan abin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon zaɓen Kamaru, makarantu da...
	Ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya kare abin da ya bayyana “nasara ƙarara” da ya samu. Yayin da al’ummar ƙasar ke ci gaba da dakon sakamakon zaɓen da za a bayyana a ranar Litinin mai zuwa, Bakary, wanda shi ma tsohon jami’in gwamnatin Paul Biya ne, ya ce zai amince ne kawai da sakamako na gaskiya. Wannan kalami nasa dai zai ƙara rura wutar zaman ɗarɗar da ake yi a ƙasar ta yankin tsakiyar Afirka. Tun daga farkon makon nan ne mutane, musamman magoya bayan Bakary suka riƙa fita kan tituna domin yin gangamin kira...
	Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin? Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja  A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci. An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta...
	Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zabe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba. Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026 “Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin...
	Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da ƙasar ta fara warwarewa daga rikicin siyasa kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin yammacin Afirka. Jerin ’yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon Afirka na bana Idan Tinubu ya gaza zai yi wuya a samu shugaban da zai yi nasara — Shehu Sani A ƙarƙashin mulkinsa, Ivory Coast — wacce ita ce babbar mai...
	Kwamitin da Kotun Tsarin Mulki ta Kamaru ta kafa domin sake ƙirga ƙuri’un zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga Oktoba, ya miƙa rahotonsa a wannan Talatar. Sakamakon da kwamitin ya gabatar ya nuna cewa shugaban ƙasa mai ci, Paul Biya, ya samu nasara da kashi 53.66 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Isa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19. Tinubu ya naɗa sabon Minista Yadda Zanga-zangar Kanu ta ja wa ’yan kasuwa da ma’aikata asara Sai dai ɓangaren jam’iyyar adawa, musamman ta Tchiroma, sun yi watsi da wannan sakamako tun kafin a sanar da shi a hukumance. Alƙaluman kwamitin sun nuna cewa jam’iyyar RDPC ta shugaba Biya ta samu ƙuri’u 2,474,179, yayin da...
	Jam’iyyar APC reshen Jihar Borno ta rage wa mata kashi 50 cikin 100 na farashin fom ɗin tsayawa takara, makonni gabanin zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 13 ga Disamba, 2025. Da yake sanar da hakan a Maiduguri, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bello Ayuba, ya ce an ɗauki matakin ne domin magance matsalar ƙarancin kuɗi da ke hana mata shiga siyasa da tsayawa takara. Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni “Wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da muke yi na samar da daidaito ga mata a fagen siyasa. “Muna son ganin mata da yawa suna jagoranci a matakin ƙasa, suna ba da gudummawa...
	An ce wanda ake zargi da kisan, sananne ne a garin Zing saboda yawo a kan tituna, sanye da fararen kaya yana yin kamar yana wa’azi.   Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, ya jefa al’ummar garin Zing da kewaye cikin rudani kan hakikanin yanayin lafiyar wanda ake zargin.   “Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ’yan banga guda biyu, wadanda a baya suka yi kokarin hana wanda ake zargin shiga jama’a saboda irin halayyarsa,” in ji wani ganau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025  Labarai Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC October...
	Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama. Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma. “Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a...
	A cewar su, wannan sabon tsarin zai taimaka wajen gina dimokuraɗiyya mai ƙarfi da ɗorewa a ƙasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Ilimi Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba October 13, 2025  Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025  Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya October 13, 2025
	An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
	Tawagar da ke karkashin jagorancin, Barry Andrews ta kuma ziyarci hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda shugabanta, Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa jinkirin da ‘yan majalisa ke yi wajen gyaran dokar zabe ta 2022 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zabe a 2027.   Wakilan, wadanda suke Nijeriya tun kusan makonni uku domin nazarin matakin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahotonsu na bayan zaben 2023, sun kuma yi tattauna da babbar jam’iyyar adawa ta PDP.   Abbas, a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Leke Bayeiwu, ya shaida wa tawagar EU cewa rahotanninta kan zabukan shekarar 2023 ana la’akari da su a cikin sauye-sauyen gyara dokar zabe da na dimokuradiyya da...
	“Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027.   “Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi.   Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023.   “An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin...
	Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da...
	More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci.   Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya...
	Tsohon mai magana da yawun marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya mayar da martani kan maganar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa naɗa Buhari a matsayin wanda zai shiga tsakanin a tattaunawarsu da Gwamnatin tarayya. A yayin taron ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta, Jonathan ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani domin tattaunawarsu da gwamnati. Jonathan ya ce a lokacin mulkinsa, gwamnatinsa ta kafa kwamitoci daban-daban don tattaunawa da mayaƙan Boko Haram domin samun zaman lafiya. Sai dai a martaninsa bayan labarin ya karaɗe kafofi...
	A lokacin, sun yi wa motar ‘yansanda ruwan harsasai yayin da ɗaya daga cikin jami’an ya ji rauni, amma an garzaya da shi asibiti. Ya ƙara da cewa daga baya ‘yan bindigar sun sake tare wata hanya a gaba, inda suka sace fasinjoji a motoci uku. Abiodun, ya ce an tura ƙarin jami’an ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro da mafarauta don bin sahun ‘yan bindigar, da nufin ceto waɗanda aka sace da kuma cafke masu laifin. A wani samame daban, Abiodun ya bayyana cewa rundunar ‘yansandan tare da mafarauta sun kai farmaki wani dajin da ake zargin maɓoyar masu garkuwa, a cikin dajin Kokolo da ke Ƙaramar Hukumar Magama. A lokacin arangamar da aka yi da ‘yan bindigar, an...
	Jigon jam’iyyar APC a Jihar Kano, Seyi Olorunsola, ya ce jam’iyyar za ta iya samun nasara a jihar a zaɓen 2027 ba tare da taimakon Rabiu Musa Kwankwaso ba. A baya-bayan nan an yi ta raɗe-raɗin cewa Kwankwaso zai fice daga NNPP tare da komawa jam’iyyar APC. Sojoji sun kama mai yi wa Boko Haram safarar man fetur a Borno Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa A taron manema labarai da ya yi a Kano ranar Lahadi, Olorunsola, ya ce Shugaba Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, sun bai wa Kwankwaso kulawa fiye da ƙima. Ya ce APC na da manyan ’yan siyasa a Kano da za su iya tabbatar da nasarar jam’iyyar....
	A cewarsa, rahotannin farko daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sun nuna cewa Jihar Kaduna da Arewa maso Yamma na baya a yawan masu rajista, lamarin da ya jawo hankalin Gwamnatin Tarayya.   Ya bayyana cewa an faɗaɗa taron ne da gangan don haɗa shugabannin ƙananan hukumomi, sarakuna, shugabannin addini, da ‘yan jarida saboda muhimmancin rawar da suke takawa wajen wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban.   “Gwamnati na matuƙar damuwa wajen tabbatar da ƙarin shiga cikin wannan aikin daga al’umma. Wannan ba game da son ɓangare ba ne; yana game da ƙarfafa dukkan ɓangarorin al’umma Kama daga matasa, mata, manya, da kowane rukuni na jinsi su shiga cikin tsarin dimokiradiyya,” in ji Maiyaki.   Kwamishinan...
	Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.” An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri “Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson. Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar...
	Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.” An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri “Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson. Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar...
	Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa muradin Yarbawa za su zama a matsayi mafi girma a cikin manufofin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ya bayyana cewa akwai labari mara tushe ko kuma fargabar cewa, a shugabancinsa idan aka zaɓe shi, “zai maida hankali ne kan Hausa/Fulani fiye da Yarbawa ko wasu ƙabilu.” An gurfanar da malamai kan zargin lalata da ɗalibarsu a Zariya Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri “Yarbawa suna cikin dangina ne kuma surikaina,” Atiku ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Kola Johnson. Tsohon mataimakin shugaban Ƙasar...
	Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985.   A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Ya ƙara da cewa, “Ina fatan hakan ba gaskiya ba ne, domin kuwa idan wannan mutum ya zama shugaban INEC, ko shakka babu; wannan gwamnati kai tsaye na gayyato yaƙin Basasa ne.” Da yake mayar da martani a kan batutuwan da jam’iyyun siyasa suka fara yi na yaƙin neman zaɓe, ya zargi hukumar zaɓe ta ƙasa da gazawa waje aiwatar da dokokin yaƙin neman zaɓe. “Wannan batu na yaƙin neman zaɓe kafin hukumar INEC ta ba shi dama, gwamnatin wancan lokacin ce ta fara yin hakan, wanda kuma hakan ke nuni da cewa; hukumar INEC ba za ta iya yin alƙalanci na gaskiya da adalci ba,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa; jam’iyyun adawa sun “Faɗa tarkon” APC...
	Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba. Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Jonathan, ya yi wannan jawabi ne a taron shekara-shekara na Tattaunawar Gidauniyar Goodluck Jonathan da aka gudanar a Birnin Accra, na Ƙasar Ghana. Ya ce mutanen Afirka na son a yi amfani da ƙuri’unsu don su samu shugabanni da za su inganta ilimi,...
	Idan aka yi ɗan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba ɗaya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne ɗan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027. Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake kira da “Star Boy”, ya kafa kansa a matsayin jagoran PDP a yankin yamma, tafiyarsa zuwa kujerar gwamna ba ta zo masa da sauƙi ba. Kafin shekarar 2019, Makinde ya tsaya takarar kujerar Sanatan Oyo ta Kudu a shekarar 2007, amma ya sha kaye a hannun Kamoru Adedibu. Duk da wannan rashin nasara ta farko, bai karaya ba. A 2010, ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya sake...
	Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
	Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027. Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya. An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja,...
	Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba da fifiko kan hadin kai da karfafa jam’iyyar a fadin jihar. Ya ce, “Ina godiya ga daukacin shugabanni da ‘yan jam’iyyar NNPP na Jihar Kuros Riba, ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode muku da kuka karɓe mu, muna matukar farin ciki da shugabancin jam’iyyar a jihar, ina kara baku kwarin guiwa da ku yi aiki tukuru don ganin an samu...
	“Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.   Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshikin shugabanci na dimokuraɗiyya.   “Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan bukatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna.   “...
	Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli. Ishiba ya sanar da matakin ne a ranar Lahadi, duk da cewa a baya ya yi ƙoƙarin kaucewa matsin lambar ‘yan jam’iyyarsa da ke neman ya sauka sakamakon rashin nasarar zaɓen, inda ya dage cewa yana son tabbatar da yarjejeniyar haraji da ƙasar ta ƙulla da Amurka ta fara aiki yadda ya kamata. ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo ’Yan ta’adda sun kashe mutum 63 a Borno “Tun da Japan ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya, kuma shugaban Amurka ya rattaba hannu a matsayin doka, mun tsallake...
	Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar. Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar. Ya ce sun ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da shugabannin matasa, sannan an ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakokin jihar domin hana miyagu shiga.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Wata mata mai tabin hankali da ba a iya gano danginta ba, ta haihu a bainar jama’a a cikin kasuwar garin Aarinoye a karamar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa matar ta haihu ne da misalin karfe 5:00;na yammacin ranar Laraba, kuma ta haifi jaririnta namiji lami lafiya ba tare da tallafin unguwar-zoma ba. ‘Za a tafka mamakon ruwan saman da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 14’ Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda Majiyar ta ce kafin matar ta haihu an saba ganinta daga safiya zuwa daren kowace rana dauke da juna biyu tana yawon tsintar dagwalon abinci da shan...
	Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, inda ya ce ya shirya yin “alwashi” akan wannan nasara. Wike ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, yana mai ƙaryata hasashen tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya ce Tinubu ba zai yi nasara ba a zaɓen mai zuwa. Wike ya ce, “Ina da tabbacin Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2027. Na ji wani yana cewa zai zo na uku, ban san irin lissafin da ya yi ba. Idan zai zo na uku, to waye zai zama na farko da na biyu?” Wike...
	Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
	Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro. Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra...
	Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar katin zaɓe ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya. Ya yabawa matakin kafa kwamitin tare da kira ga mambobinsa da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin su tafi su karɓi katin zaɓensu. Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba...
	Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano. A ranar Asabar aka gudnar da zaben na cike gurbi a mazabun Majalisar Tarayya da akamaimaita a ranar Asabar a mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike gurbi na Bagwai/Shanono. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da karuwar adadin mutanen daga 288 a ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Kano. A cewarsa, zaben ya fuskanci barazana sakamakon “shigo da ’yan daba da dama daga cikin da wajen jihar” da suka yi yunkurin dagula tsarin zaben, amma an samu nasarar shawo kan lamarin ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro.       ...
	Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ɗan majalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari/Tsanyawa. Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wasu ’yan siyasa sun yi maguɗi. Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki APC ta lashe zaɓen cike gurbi a Zariya Shugaban jam’iyyar na jihar, Kwamared Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya shaida wa ’yan jarida cewa INEC ta “tauye wa jama’a haƙƙinsu” bayan ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Ya ce zaɓen ya kamata a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 10 da kotun ɗaukaka ƙara ta soke. NNPP ta ce INEC ta ƙwace sakamakon da aka...
	Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano. Da yake sanar da sakamakon da misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadin nan, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ya bayyana Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 31,472. Garba Gwarmai ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Yusuf Ali Maigado wanda ya samu ƙuri’u 27,931.
	Jam’iyyar NNPP wato New Nigeria Peoples Party, ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da ke Jihar Kano. Babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Hassan Adamu ne ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 12:36 na daren Asabar wayewar gari Lahadi. Farfesa Hassan Adamu Shitu, ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 16,198, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC —All Progressives Congress — wanda ya samu ƙuri’u 5,347. Dokta Ali Hassan Kiyawa na jam’iyyar NNPP shi ne ya yi nasara a kan Ahmad Muhammad Kadamu na jam’iyyar APC bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar
	Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano. Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana. An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta samu rahotannin da suka tabbatar an samu rikici a Shanono, Bagwai da Ghari. Ta ƙara da cewa masu kaɗa ƙuri’a sun tsere daga rumfunan zaɓe sakamakon tashin hankali, yayin da...
	Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye. Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba. APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Wakilinmu ya zagaya rumfunan zaɓe, inda ya gane wa idonsa yadda aikin zaɓen ke tafiya a hankali saboda matsalar na’urar tantancewa. Malam Halliru Hamza, ya ce shi ma bai samu damar kaɗa ƙuri’a ba saboda na’urar taƙi ta tantance shi. Ya ƙara da cewa mutane da dama ba su fito ba saboda yadda siyasa ke tafiya ba tare da ci gaba ba, sai tsadar rayuwa...
	Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano. Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana. An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta samu rahotannin da suka tabbatar an samu rikici a Shanono, Bagwai da Ghari. Ta ƙara da cewa masu kaɗa ƙuri’a sun tsere daga rumfunan zaɓe sakamakon tashin hankali, yayin da...
	Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen. Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu. Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci...
	Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano. Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro suna aikin tabbatar da zaman lafiya domin a gudanar da zaɓen cikin lafiya. HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna “Dukkanin mutanen da muka gani suna kawo matsala an kama su, kuma zaɓen yana tafiya lafiya. “Na gamsu sosai da yadda komai ke tafiya. Kayan zaɓe sun isa a kan lokaci,...
	Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna. A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke  ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci. A wata sanarwa da kakaki rundunar,...
	Ahmed Maiyaki da Sadiq Mamman Legas a madadin gwamnatin jihar Kaduna sun ce ofishin babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a zai yi nazari kan kalaman da kungiyar hadaka ta ADC ta yi tare da baiwa gwamnatin jihar shawara kan mataki na gaba. Tun da farko a wani taron manema labarai, jam’iyyar African Democratic Congress da hadin gwiwarta sun zargi gwamnatin jihar Kaduna da daukar hayar ‘yan baranda sama da 4000 tare da cire naira miliyan 30 daga asusun kowace karamar hukuma domin kawo cikas ga zaben da ke tafe.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut. A cewarsu, sun aika da koke...
	Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar. A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya ce...
	Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
	Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin al’umma. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin tattaunawarsa da malaman addini da na gargajiya a birnin Kaduna, inda ya jaddada muhimmancin rawar da shugabannin addini ke takawa wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai. Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu “Ina...
	Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ya ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Najeriya sun sauke APC daga kan mulki. “Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya zai lalace. “Ƙasar...
	Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), ƙarancin yawan masu kada ƙuri’a, sayen ƙuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zaɓe, da kuma yaɗuwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ƴan siyasa, canja sheƙa da zaɓaɓɓu ke yi, da dai sauran makamantansu.                                        Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (eɗclusion) na masu gaskiya da riƙon amana, matasa, mata, masu fama da naƙasa, ƴan...
	Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta  Ya kuma ce sai a ranar 25 ga watan Agusta, 2025 za a fara rajistar ƙuri’a a zahiri. “Za a fara rajistar ƙuri’a ta Intanet a faɗin ƙasa daga ranar 18 ga watan Agusta,” in ji Farfesa Yakubu. “Rajistar ƙuri’ar a zahiri kuma za ta fara daga 25 ga watan Agusta, 2025,”...
	Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC. Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya An bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano,...
	A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai.   A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam Hafiz Khalid, ya gabatar da cikakken jadawalin ayyukan zaɓen.  Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gaskiya a kowane mataki, yana mai bayyana zaɓen a matsayin aikin gama gari da ke buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki.   Mahalarta taron sun bayar da shawarwari masu amfani tare da gabatar da muhimman tambayoyi da suka shafi inganta sahihanci da nasarar zaɓen.   Wasu daga...
	Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni mai nazari ne, kuma ina nazarin ra’ayoyi, a jihohin Arewa Peter Obi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP zai doke duk wani ɗan takara, saboda mutanenmu suna da gaskiya.” Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Peter Obi ya fice daga Jam’iyyar PDP a watan Mayun 2022 inda ya jagoranci Jam’iyyar LP a...
	Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal  ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027. Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.” Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki...
	More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
	Olumekun ya ƙara da cewa, katunan zaɓe na rijistar da ta gabata ma za su kasance a shirye don karɓa. Ya ce da saura kwanaki 105 zuwa zaɓe, INEC ta san lokaci ya matse, amma tana tabbatar da cewa sabbin masu rijista a jihar Anambra za su samu damar karɓar katunansu kafin zaɓen.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100 da aka samu a bara. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati  Sanarwar ta ce an yi bitar alkaluman mamatan a bana ne bisa  la’akari adadin waɗanda suka kamu kuma ta yi ajalinsu a shekarar 2024. Hukumumar ta ce alkaluman mamatan ya kai kashi 18.9 cikin 100 na...
	Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya huɗu a Najeriya da aka zaɓa don wannan aikin na tsawon shekaru uku (tare da yiwuwar ƙarin shekaru biyu don sa ido). Sauran su ne Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (Owo) da Babban Asibitin Irrua da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin. Wannan shiri, wanda Gidauniyar Ƙasa da Ƙasa kan Cututtukan Masu Saurin Yaɗuwa a Najeriya (IFAIN) ke gudanarwa tare da haɗin gwiwar...
	Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne, suka yanke hukuncin a ranar Alhamis. Sun yi watsi da ƙarar da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar, kan cewar hujjojin da ya gabatar ba su da inganci. Mai Shari’a Garba, ya ce Ighodalo da jam’iyyarsa PDP ba su kawo hujjoji masu ƙarfi da za...
	“Mun yi watsi da ƙarar saboda babu ingantacciyar hujja a cikinta. Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke,” in ji Mai Shari’a Garba. Wannan hukunci ya tabbatar da cewa Sanata Okpebholo na jam’iyyar APC ne, halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Edo na shekarar 2024. PDP ta zargi cewa an yi maguɗi a zaɓen, inda ta nemi a soke sakamakon. Amma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi watsi da ƙorafinta, wanda ya sa suka kai ƙarar zuwa Kotun Ƙoli. Da wannan hukunci, an rufe duk wata shari’a da ta shafi zaɓen gwamnan Jihar Edo.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
	Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015. Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba. Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe. Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da...
	Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu zai sake lashe zaɓe ba tare da wata tangarɗa ba. Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Ya ce dole ne ’yan adawa su yi aiki da hikima da dabaru idan suna son yin nasara. “Shirina a wannan karon shi ne zan goyi bayan ɗan Arewa a 2027,”...
	ADC ta tunatar da Tinubu cewa da gwamnatin Goodluck Jonathan ba ta jure hamayya ba a baya ba, shi ma ba zai kai matsayin shugaban ƙasa ba, kuma APC ba za ta lashe zaɓe ba. Jam’iyyar ta ce ya kamata shugaban ƙasa ya nuna cewa yana goyon bayan gaskiya da ‘yancin jam’iyyu a tsarin dimokuraɗiyya.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Salim Sani Shehu Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027. Major ya ce jam’iyyar ta riga ta kori Kwankwaso da Galadima bisa zargin aikata laifukan cin amanar jam’iyya, don haka ba su da ikon magana da sunan NNPP, balle su wakilci jam’iyyar a a duk wani sha’anin siyasa. “Tun da dadewa NNPP...
	Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ADC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Sabuwar haɗakar ta haɗa da fitattun ’yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa Sauran sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran shugabannin jam’iyyun adawa. Sun ƙaddamar da sabuwar haɗakarsu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a ranar Laraba. A...
	Majalisar Dokokin Jihar Filato ta zaɓi Nanloong Daniel a matsayin sabon Kakakin Majalisar, bayan da Gabriel Dewan ya yi murabus. Zaɓen sabon kakakin ya gudana ne a wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar ranar Laraba. David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Zaman ya gudana ne a harabar tsohon gidan gwamnatin jihar. Hon. Nanloong Daniel, wanda ke wakiltar mazaɓar Mikang wanda kuma tsohon jagoran masu rinjaye ne a majalisar ta tara, ya samu amincewar dukkanin ’yan majalisar 24 don jagorantar su. Daniel shi ɗan jam’iyyar APC ne. Zaɓen nasa ya biyo bayan wani zaman sirri da aka yi tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang,...
	Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
	2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
	2. Haɗin kai da shugabanni daga ko’ina 3. Rashin ta’asar da ya yi wa kowa Bayannan ƙuri’un INEC na 2023 daga jihohin Arewa maso Gabas sun nuna cewa Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u fiye da Tinubu a dukkan jihohin yankin. Ƙungiyar ta kammala da cewa: “Lokaci ya yi da Shugaba Tinubu ya kamata ya yi la’akari da wannan batu yayin shirye-shiryen zaɓen 2027.”  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula. Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a Najeriya. NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato Hakan dai na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani game da zaɓen. Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne...
	 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Ƙungiya mai rajin kishin APC a Kano mai suna APC Patriotic Volunteers, ta ce shekaru biyun da jam’iyyar NNPP ta shafe tana mulkin jihar nakasu ne da ke nuna tsantsar rashin ƙwarewarta a gwamnatance. A taron da ta gudanar da manema labarai a Kano, ƙungiyar bisa jagorancin shugabanta Alhaji Usman Alhaji (Wazirin Gaya) ta ce nazarin da ta yi wa salon mulkin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar mata da gazawarsa wajen haɓaka ɓangarori masu muhimmanci duk da makudan kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke bata, da kuma kudaden shiga na cikin gida da take samu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya...
	Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su daina gaggawar shige-da-fice wajen neman tazarce a Zaɓen 2027. ACF ta ce zai fi dacewa gwamnatin Tiinubun ta mayar da hankali wajen ganin ta kyautata rayuwar ’yan Nijeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓensa a 2027, lamarin da ƙungiyar cewa hakan ya yi wuri. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba Ɓarawon waya ya kashe babban jami’in soja da wuƙa a Kaduna Wannan kira dai na kunshe cikin wata sanarwar yi wa musulmi barka da Sallah Babba da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar. Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da...
	A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...
	 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa.   “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe  Shiga zaurenmu na WhatsApp
	Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan. Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar. Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Shin ko hakan zai kawo ƙarshen matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan faɗuwa zaɓen 2023? Daga cikin matsalolin da suka kunno kai a cikin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP tun bayan faduwarta zaɓe a 2023 shi ne yin baram-baram a kan yadda za ta dinke barakar da aka samu a lokacin zaben fidda-gwani da rikicin shugabanci a matakai daban-daban da kuma kasa tsayawa da kafarta domin samar...
	Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ko yau aka yi zaɓe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai yi nasara. Oshiomhole wanda shi ne mai wakiltar shiyyar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a safiyar wannan Larabar. DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Majalisar Dattawa ta buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa Borno da Yobe Tsohon gwamnan na Jihar Edo ya faɗi hakan a lokacin da yake tsokaci kan sauya sheƙar da Sanatocin Kebbi uku suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Ya ce, Tinubu ya ɗauki ƙwararan matakai domin daidaita Nijeriya, yana mai cewa kafin gwamnatinsa manoma a wasu sassan ƙasar...
	Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar Babangida a littafinsa mai suna “A Journey in Service” ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe Zaɓen 12 ga watan Yunin 1993. Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’ Alhaji Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to...
	“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
	Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu.   Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar.   Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar.   Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi.   Gwamnan ya yi addu’ar...
	Uwargidan tsohon Shugaban Najeriya Dame Patience Jonathan, ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu za ta marawa baya a Zaɓen 2027. Patience ta nanata cewa ba ta da burin komawa fadar shugaban ƙasa, amma ta ce a shirye take ta taimakawa uwargidan shugaban ƙasa na yanzu, Sanata Oluremi Tinubu wajen yaƙin zaɓen 2027. Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670 Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin Aminiya ta ruwaito Patience na bayyana haka ne a lokacin da take kiran sunan manyan baƙi ciki har da ’yar shugaban ƙasar, Folashade Tinubu-Ojo a wajen taron da aka karrama ta a matsayin jagora ta gari, wanda kamfanin Accolade Dynamics Limited ya shirya...
	A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
	Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis. Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya. Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane Robert Prevost zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV). Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.
	Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar mai mambobi 630. Kafin zama shugaban gwamnati ana buƙatar kuri’u 316 kuma jam’iyyar CDU/CSU da kuma jam’iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake buƙata. Merz zai maye gurbin Olaf Scholz wanda ya faɗi zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu Upon announcing the second vote, the head of the Union bloc in parliament, Jens Spahn, said, “The whole of...
	’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF). Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne...
