2025-09-20@08:58:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11
«ɓarayin daji su»:
A ɓangaren al’umma an samu halartar shugaban ƙaramar hukumar Faskari Hon. Surajo Aliyu Daudawa da Ɗan Majalisa dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Faskari injiniya Sama’ila Mu’azu Bawa. Sauran sun haɗa da Hakimin Faskari da kuma na Mai Ruwa da wakilan al’umma da masu riƙe da masarautar gargajiya da sauran al’umma. Sai kuma ɓangaren ɓarayin daji inda aka samu halartar manyan jiga-jigan da suka kwarai wajen tada zaune tsaye a yankin Funtua baƙi ɗaya. Mutane iri su Ado Aleiro Ƴan Kuza da Kachalla Hassan Sarkin Fulani Mai Taru da Kachalla Isiya Akwashi Garwa da Kachalla Sari da kuma Alhaji Abdullahi da sauran dakarun daji duk sun halarci wannan zaman sulhu. Rahotanni sun bayyana cewa an cimma wasu sharuɗa kafin a kulla...
Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara. Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa da ake zargin su da satar mota a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa. Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya A cewar majiyar an kama sojan bogin mai suna Kabiru Musa da abokan aikinsa Umar Ali da Sabi’u Bashir, dukkansu ‘yan asalin Jihar Kano. A cewar kakakin rundunar waɗannan...
Dakarun runduna ta 3 da rundunar haɗin gwiwa – Operation Enduring Peace (JTF OPEP) masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun kama wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne a ƙauyen Kogul da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. A cewar rundunar, kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan ƙoƙarin da sojojin suka yi ne don daƙile barazanar satar shanu, “wanda ke haifar da rikici a yankin da Rundunar haɗin gwiwa ta ke.” 2027: Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a Kano An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Da yake yi a wa manema labarai bayan ikan nasarar da rundunar ta samu a Jos, a ranar Alhamis, kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce a...
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne. “Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,”...
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne. “Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,”...
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi. Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a garin Agatu da wasu sassan Ƙaramar hukumar Guma da ke Jihar Benuwe. Galma ya kuma yi zargin cewa, ɓarayin shanu da ke afkawa jama’a a Ƙaramar hukumar Agatu sun faɗaɗa hare-harensu zuwa sassan Jihar Kogi. “A ranar 19 ga Yuli, 2025...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta cafke mutane biyu da ake zargi da satar babura wadanda ta ƙwato babura biyu a hannunsu hadi da wani wanda aka tsinta a lokacin sintiri. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an gudanar da samamen ne bisa bayanan sirrin da aka samu daga wani mai kishin ƙasa, wanda ya kai jami’an Operation Hattara har zuwa wata maɓoyar ɓata gari a Tudun Hayin Kwarin-Misau, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akko An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a Nijeriya An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi Rundunar ta ce an kama Misba’u Adamu mai shekaru 25 dan asalin garin Alkaleri na Jihar Bauchi da Adamu Ibrahim mai shekaru 28, daga Karamar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta samu nasarar kama wasu ɓarayin daji da suka addabi garin Bajoga da ke Ƙaramar Hukumar Funakaye. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen yaƙar masu aikata laifuka a faɗin jihar. Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? A wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa an kama mutum huɗu da ake zargi da kai wa wani matashi mai suna Muhammed Ahmed hari, wanda ke zaune a Unguwar Matasa, Bajoga. An ce ɓarayin sun kai masa hari da makami cikin dare, inda suka tsoratar da shi da...
Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina. Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar. An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje “Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza ayyukan ’yan bindigar da ke addabar garuruwa da ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan. Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin...
Bari ma in yi waiwaye. In yi bi-ta-da-ƙulli. Da jihohin Arewa na musulmi suke yin hutun lahadi ba su zuwa aiki to don su je gidan uban wane ne? A Katsina dai wannan ba zagi ne ba. A maye gurbinsa da hutun Juma’a ranar zuwa sallar Juma’a. Ranar Idi ce. Da ake yin hutu lokacin kirsimati ko wata Ista shi kuma hutun menene ne? Har yanzu Turawan na nan ne? Idan aka ce a yi hutu lokacin da yara ke taya iyayensu aiki a gona za su gane hikimar wannan tunda abinci zai zo gida. Lokaci ya yi da musulmi za su nuna wa duk wani mai shishshigi da takalar faɗa yatsa. Tsarin dimokuraɗiyya tsari ne na masu rinjaye a...
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago. Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato Sai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata. SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin...