An kashe sojoji 12 a yankin Tillaberi na yammacin ƙasar mai iyaka da Mali da Burkina Faso, yankin da ke zama tungar masu iƙirarin jihadi da ’yan ina da kisa masu nasaba da ’yan ƙungiyoyin al Qaeda da IS.
Ma’aikatar tsaron Nijar ta sanar da cewa an yi wa dakarunta na bataliyar ko-ta-kwana mai suna Almahao kwanton ɓauna ne a wani kauye da ke kusa da Sakoira na yammacin Tillaberi, inda sojan suka jima suna ɓarin wuta da ’yan ta’adda kafin a kawo musu ɗauki.
Gwamnatin ta bayyana cewa tuni ta cafke mutane biyu da ake zargi da kai harin a barikin sojojin da ke da nisan mil shida daga ƙauyen Sakoira a jihar ta Tillaberi.
A baya gwamnatin ƙasar ta sanar da kashe ’yan ta’adda tara, ta kuma ƙwace makamai daga hannu masu iƙirarin jihadi da suka kai wani harin da ta daƙile a yankin.
A yankin Tahoua mai iyaka da Nijeriya, rundunar tsaron Nijar ɗin ta sanar da ɗauki ba dadi da Lakurawa masu yawan yin kutse kuma suna kai hari ga bututun man fetur ɗinta da ke zuwa gaɓar teku a Benin.
Nijar Mali da kuma Burkina faso sun shafe sama da shekaru 10 ƙarƙashin barazanar ƴan ta‘adda masu iƙirarin jihadi da ke afkawa jami’an tsaro da kuma fararen hula lokaci zuwa lokaci.
To sai dai kuma ƙididdiga ta nuna ƙaruwar kai hare-hare tun bayan da sojojin ƙasashen uku suka yanke shawarar kifar da gwamnatin fararen hula.
Rikicin yankin Sahel da ya samo asali daga ƙasar Mali a 2012, wanda kuma ya faɗaɗa har zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Benin da ya halaka dubban mutane kama daga sojoji har zuwa farar hula.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.
Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla.
“Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.”
Ya ce daga baya ’yan bindiga suka kawo sabon hari da asuba, ranar Alhamis a yayin da ake Sallar Asuba a ƙauyen Magama, suka yi garkuwa da mutane 20.
“Nan ma da ’yan bindiga suka bi su, ashe sun yi kwanton ɓauna, suka kashe ’yan banga 13, suka jikkata wasu da dama.”
Sakataren Yaɗa labaran Shugaban Ƙaramar Hukumar Mashegu, Isah Ibrahim Bokuta, ya tabbatar da hare-haren, tare da jinjina wa ’yan bangar bisa yadda suka sadaukar da ransu domin kare al’umnarsu.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Neja, Wasiu Abiodun, amma ya ce zai tuntuɓe shi daga baya, idan ya bincika.
A gefe guda, mazauna yankin sun shaida mana cewa tun ranar Litinin al’ummomi da dama sun yi gudun hijira zuwa Mashegu, Kawo-Mashegu, Manigi da wasu wurare. Wasu kuma sun fake a gidajen ’yan uwansu a nesa domin tsira.
Majiyoyi sun ce cikin ƙauyukan da aka watse har da Dutsen Magaji, Borin Aiki, Gidan Ruwa da Magama.
Hakazalika har yanzu masu garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ba su sake shi ba, makonni bayan rahoton cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa na Naira miliyan 70.
An yi garkuwa da Niworo ne a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, tare da Kwamishina na Dindindin II na Hukumar Zaɓe ta Jihar Neja (NSIEC), Barrister Ahmad Mohammed, direbobinsu da wasu matafiya a kan titin Mokwa–New Bussa, a Karamar Hukumar Borgu.