Nigeria: Boko Haram Ta Kashe Mutane 12 A Borno
Published: 27th, April 2025 GMT
‘Yan kungiyar ta boko haram sun kashe masu sintiri farafen hula 2 da kuma wasu sana’ar yin sarar itace su 10 a a Bokko Gjide a karamar hukumar Gwoza dake Jahar Borno. Sarkin Gwoza Alhaji Muhammad Shehu Timta ya tabbatar da kisan mutanen da aka fi kira da (Civilian JTF) bayan da aka yi musu kwanton bauna a kan hanyar Kirawa.
Haka nan kuma ya kara da cewa; mutanen sun shiga cikin daji ne domin saro itace, a ranar Asabar, a yayin da masu dauke da makaman su ka yi musu kwanton bauna su ka kashe kashe daga cikinsu, sannan kuma su ka yi wa wasu biyu munanan raunuka.
Sarkin ya kara da cewa; Mun yi jana’izar 10 daga cikinsu sannan kuma mu ka dauke wadanda su ka jikkata zuwa Maiduguri domin samun magani.
Wannan harin na Boko Haram ya afku ne bayan sa’o’i 48 da shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya aike da ministan tsaro Badaru Abubakar, da kuma babban jami’in tsaro na soja Janar Christopher Musa, domin su yi bitar halin tsaro da ake ciki a Jahar ta Borno.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria