HausaTv:
2025-05-21@21:01:02 GMT

 Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Kudancin Lebanon

Published: 17th, April 2025 GMT

Sojojin HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankunan kudancin Lebanon da ya zama ruwan dare a cikin kwanakin bayan nan.

A jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gari “Aytas-sha’ab. Haka nan kuma tankokin yakin ‘yan mamayar sun kai wasu hari a kan wasu gidaje a garin na Aytas-sha’ab.

Haka nan kuma sojojin mamayar sun gina wata Katanga da ta raba tsakanin Ayta da Khillatul-wardi.

Har yanzu sojojin na HKI suna ci gaba da zama a cikin wasu wurare biyar da ta ki ficewa daga cikinsu bayan zuwa karshen wa’adin kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki.

Kamfanin dillancin labarun Lebanon ya bayyana cewa; Jirgin yakin HKI maras matuki ya kai hari akan gidajen tafi da gidanka da wadanda aka rushewa gidaje suke ciki a kusa da garin Shaihin. Sai dai babu wani rahoto akan rashin rai,ko jikkatar mutane, sai dai gidaje da dama sun rushe.

Wadannan hare-haren suna a matsayin sabon bude wuce gona da iri na HKI a kudancin Lebanon.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon din ta sha yin kira ga gwamnati da ta yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta na tilasata wa ‘yan mamaya janyewa daga wuraren da suke ciki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wasu Yan Siyasa A Burtaniya Suna Matsaya Gwamnatin Kasar Ta Amince Da Kasar Falasdinu
  • Sojojin Sudan Sun Gama Tsarkaka Birnin Khartoum Daga ‘Yan Tawayen Rapid Support Forces
  • Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar
  • Falasdinawa 94 sun yi shahada a Hare-haren Isra’ila a rana guda
  • Gaza : Birtaniya ta dakatar da tattaunawar cinikayya da Isra’ila
  •  Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kashe Falasdinawa ‘Yan Gudun Hijira A Lokacin Da Suke Bacci
  • Hare-Haren Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
  • Iyalan Sarkin Da Aka Kama Suna Neman Taimakon Kudin Fanso Shi Miliyan ₦50
  • Isra’ila Ta Kai Hari Ga Rumbun Magungunna A Kudancin Gaza
  • Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5