Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe.

Shirin da shugaban kasar Donal Trump ya bayyana shi ne karshe dai, ya bukaci gwamnatin shugaba Volodimir Zelesky ta amince da yankin Cremea da kuma sauran yankunan hudu wadanda Rasha ta mamaye da karfi shekaru uku da suka gabata su zama mallakin kasar Rasha har’ abada.

Sannan ta amince a daukewa kasar Rasha takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata tun bayan fara yakin. Sannan daga karshe ta amince ba zata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba.

Shawara bata yi maganar wani abu banada wadannan hudu ba, duk da cewa Ukraine tana da wasu bukatu a yarjeniyar tsagaita wuta da kuma samar da sulhu mai dorewa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Moscow ta bukaci a tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu don samun damar tattaunawa amma gwamnatin Kiev ta ki amincewa.

Masana suna ganin wadannan al-amura suna da nauyi ga kasar ta Ukraine, amma kuma bata da zabi tunda Amurka ce ta biya mafi yawan kudaden da Ukraine ta kashe a yankin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Nsukka ta ce Gwamnatin Tarayya na lalata makomar ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar 2009.

A taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi.

Ya yi magana ne a madadin jami’o’i takwas da ke yankin.

Opata, ya ce an tattauna tare da ƙumla yarjejeniyoyi da dama tsakanin ASUU da gwamnati tsawon shekaru, amma babu wani ci gaba da aka samu.

Ya zargi jami’an gwamnati da yin lƙawarin ƙarya da gangan.

Ya ce ASUU ta dakatar da yajin gargaɗin da ta yi kwanan nan saboda ɗalibai, iyaye, da ƙungiyoyin ƙwadago, amma har yanzu gwamnati ba ta ɗauki aniyar warware matsalar ba.

Opata, ya gargaɗi gwamnati cewa idan ba ta kammala tattaunawar cikin wata ɗaya ba, jami’o’i na iya sake tsunduma yajin aiki.

ASUU, ta kuma zargi wasu jami’an gwamnati da yaɗa bayanan ƙarya game da tattaunawar, musamman batun biyan bashin albashi da wasu kuɗaɗen da aka riƙe musu.

Kungiyar ta ce Najeriya na da isasshen kuɗi, amma gwamnati ce ba ta yi niyyar saka hannun jari a ilimi.

Sun roƙi sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin ƙwadago, ɗalibai, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su matsa wa gwamnati lamba don ganin an daidaita abubuwa.

ASUU ta ce malamai na cikin tsaka mai wuya saboda ƙarancin albashi, kuma ba ya isarsu wajen al’amuransu na yau da kullum.

Ƙungiyar ta sake jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta cika alƙawarun da ta ɗauka a baya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba
  • Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana
  • Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin zaman lafiya na Trump
  • AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro
  • Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
  • Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
  • Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya
  • Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin
  • Rasha Ta yi Gargadin Cewa Za ta Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka
  • Wata Gidauniya Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mata A Nasarawa