HKI Tana Amfani Yunwa A Matsayin Makamin Yaki A Kan Falasdinawa A Gaza
Published: 29th, April 2025 GMT
Wakilin falasdinawa a kutun kasa da kasa ta ICJ da ke birnin Haque na kasar Nerthelands yace HKI tana amfani da hana kayakin agaji daga ciki har da abinci shiga gaza a matsayin makami kan Falasdinawa don kashesu.
Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ammar Hijazi jakadan kasar Faladinu a cibiyoyin MDD a kasashen Turai yana fadar haka a gaban alkalai a kotun ta ICJ a jiya litinin.
Ya ce HKI tana kisa ta sama da makamai, sannan tana kisa ta kasa da yunwa banda haka tana ci gaba da korar Falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan tun fiye da watanni 3 da sua habata.
Kutun ta bude wannan zaman ne bisa bukatar MDD ta shekara ta 2024 na bincike don tabbatar da cewa HKI tana amfani yunwaa a matsayin makami a Gaza. Ammar Hijazi ya kara da cewa banda wannan babban kotun HKI tana goyon bayan amfani da yunwa a matsayin makami a gaza tun fiye da watanni 2 da suka gabata.
Wasu lauyoyi daga kasashe daban–daban wadanda suka hada da Nerthlands da Afirka ta kudu duk sun yi magana sun kuma yi allawadai da HKI kan abinda take aikatawa a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza
Ministan wajen na Sin, ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan manufar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa, ciki har da Switzerland, ta yadda za a kai ga cimma nasarar aiwatar da sahihan matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA