An Kammala Jana’izar Paparoma Farancis A Birnin Vatican
Published: 27th, April 2025 GMT
Fafa roma Farancis shugaban cocin catholica ya koma makwancin na din din din a Santa Maria Maggiore Basilica, wanda kuma ake kira St. Mary Major, daya daga cikin fitattun coci-coci guda 4 mafi daraja a birnin Vatican .
Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika News’ ya bayyana cewa Farancis shi ne paparoma na farko daga yankin Laten Amurka, wanda kuma ya kirkiro abubuwa da dama a cocin daga ciki shi ne ya fara zaben inda za’a yi masa kabari.
Tashar talabijin ta CNN ta nakalto cewa fafaroman ya bukaci a yi masa kabari mai sauki a wajen birnin Roma wato Basilica di Santa Maria Maggiore.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata
Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya.
Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji.
Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani.
A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa.
Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga don shiga tsakani amma ya faɗi sumamme a yayin.
Ayuba, wanda aka yi imanin yana cikin koshin lafiya kafin faruwar lamarin, an garzaya da shi asibiti a garin Gawu, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsa.
Sarkin yankin, bayan samun labarin lamarin, ya sanar da ’yan banga tare da ba da umarnin kama ma’auratan, waɗanda daga baya aka mika su ga jami’an tsaro a Gawu.
Ibrahim, daya daga cikin ’yan bangan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Mun fahimci cewa ƙaramar rashin fahimta ce kawai ta kai ga faɗan tsakanin makwabcin mamacin da matarsa.”
Ya ƙara da cewa an kai gawar mamacin kauyensa na Paiko a Jihar Neja don binnewa.
’Yan sanda a yankin Gawu sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce har yanzu ana ci gaba da bincike.