Jigawa Ta Bude Sabon Babi: Maniyyata Za Su San Masaukansu Tun Daga Gida Najeriya
Published: 25th, April 2025 GMT
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta bullo da tsarin da kowanne maniyyaci zai san masaukinsa a kasa mai tsarki tun daga nan gida najeriya.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shalkwatar hukumar dake Dutse.
Yana mai cewar, wannan shi ne karon farko da hukumar ta bullo da tsarin domin maniyyaci ya san masaukinsa a nan gida kafin zuwa kasa mai tsarki.
Game da batun kudade kuwa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma kaddamar da kwamitin canjin kudaden guzuri na maniyyata domin samun saukin canji yayin aikin Hajjin.
Ya ce an kafa kwamitin ne domin bibiyar maniyyata kan canjin kudin guzuri, kasancewar wasu batagari na damfarar mahajjata a kasa mai tsarki wajen canjin kudade daga Dala zuwa Riyal.
Ya kara da cewar, hukumar ta turawa hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON fiye da naira miliyan dubu shida da miliyan dari uku da talatin da daya (6,331,000,000) a matsayin kudaden maniyyatan aikin hajjin bana.
Ya ce jihar Jigawa ce ta farko wajen biyan kudaden aikin hajjin bana ga hukumar aikin hajji ta kasa.
Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar Gwamnatin jihar ta baiwa hukumar rancen naira miliyan dubu uku da miliyan dari uku da sittin (3,360,000,000) da ta yi amfani da shi wajen sayen kujerun aikin hajjin bana daga hukumar aikin hajji ta kasa.
Umar Labbo, ya ce sun cimma kaso 95 bisa 100 na aikin bada biza ga maniyyata.
Babban Daraktan ya shedawa mahalarta taron cewar hukumar ta kammala duk wani shiri na fara jigilar maniyatan wanda za a fara jigilar alhazan Najeriya a ranar tara ga watan Mayu.
Kazalika, wakilan hukumomin tsaro sun yi bayani akan shirye shiryen da suke yi domin tunkarar aikin hajjin bana
Ya kuma yi kira ga maniyyatan jihar, da su ci gaba da halartar cibiyoyin bita domin samun ilimin da za su gudanar da aikin hajji cikin sauki.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da babura a fadin jihar.
Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya da babura a cikin birnin Kano, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar.
Danladi Karfi ya jaddada cewa dokar da ta haramta zirga-zirgar babura a matsayin sufuri na haya har yanzu tana nan daram, kuma za a aiwatar da ita sosai, inda ya gargadi masu karya doka da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kara da cewa Kano na daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a kasar nan, kuma gwamnati ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya tayar da hankalin jama’a ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a su kasance masu lura da kai rahoton duk wani abin da suke shakku ga hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.