Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Published: 28th, April 2025 GMT
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA