Rasha Ta Fara Aika Isakar Gas Zuwa Kasar Iran Ta Azarbaijan Don Sayarwa A Kasuwannin Duniya
Published: 26th, April 2025 GMT
Kasar Rasha ta fara tura iskar gasa zuwa kasar Iran ta kasar Azarbaijan, wanda daga karshe zai shiga kasuwan ga kasar ta rasah.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar ta na fadar haka a yau Asabar.
Labarin ya kara da cewa tun taron kwamin hadin guiwa na kasuwanci da tattalin arziki na kasashen biyu ya gudanar da taronsa na hadin guiwa karo na 18 a birnin Mosco, Rasha ta bada sanarwan fara tura iskar gas zuwa kasar ta Iran ta kasar Azirbajan, wanda kuma hakan zai zama kasuwa ga kasar Rasha amma a kasar Iran.
.
Kasashen biyu dai sun dade suna kokarin karfafa dangantaka a tsakaninsu, musamman bayan da kasashen yamma suka dora masu takunkuman tattalin arziki masu tsananin, saboda yakin da Rasha take yi a Ukraine da kuma saboda shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
Gwamnatin kasar Faransa ta yi kakkausar suka tare da tofin Allah tsine kan harin ta’addancin da aka kai birnin Zahidan na kasar Iran
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin birnin Zahidan na kasar Iran, tare da jaddada adawar kasarta kan duk wani harin ta’addanci da aka kai kan fararen hula.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, birnin Paris na matukar yin Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a birnin Zahidan na kasar Iran a ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama ciki har da uwa da kuma ‘yarta.
Sanarwar ta kara da cewa, “A yayin da take mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka mutu, suna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a wannan harin ta’addanci.”
Wani abin lura a nan shi ne cewa, a safiyar ranar Asabar 26 ga watan Yuli ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan ginin hukumar shari’a ta cibiyar birnin Zahidan, fadar mulkin lardin Sistan da Baluchestan a kudu maso gabashin kasar Iran, inda suka kashe da kuma jikkata wasu Iraniyawa.