An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji
Published: 26th, April 2025 GMT
Iyalan wata dattijuwa da suka nema suka rasa sun shiga fargaba bayan gano gawarta a cikin wani maciji.
Lamarin na zuwa ne bayan kumburin ciki ya bayyana sosai a kasurgumin maciji — kafin dangin tsohuwar su gano cewa maciji ya haɗiye kakarsu a cikinsa.
Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a NejaIyalan matar da ta ɓace sun bi sawun macijin zuwa wani mai yawan ciyayi a kudancin Sulawesi na kasar Indonesia.
’Yan yankin sun tsorata matuka lokacin da suka ga maciji mai tsawon kafa 26 ya yi nauyi da wani babban kumburi a cikinsa.
A lokacin da suka farka cikin macijin, sun gano gawar matar mai suna Hasia mai shekara 66, wadda ta bata a lokacin da take komawa gida daga wurin aikinta a wata gonar roba.
Ana kyautata zaton macijin ya fito ne daga dogayen ciyayin ya sari kafarta, wanda hakan ya sa ta faɗi.
Ɗan matar mai suna Nurdin, ya ce danginsa da ke cikin damuwa, sun kaddamar da bincike lokacin da dare ya yi, bayan da suka lura tsohuwar ba ta dawo gida ba.
Sun yi cigiya kafin su far wa macijin da misalin ƙarfe 9 na dare.
Sai suka sari macijin, suka buɗe cikinsa, inda suka tarar da gawar Hasia a cikinsa.
Nurdin ya razana, inda ya ce: ‘Wannan abu ne mai ban tsoro.
“Na san mutuwa ce mai raɗaɗi ga mahaifiyata, kodayake macijin ya mutu.
“Ba zai taɓa dawo da ita ba. Yanzu muna addu’ar Allah Ya jikan ta da rahama.
Ipda Zakaria, Shugaban ‘yan sandan PituRiase, ya ce: ‘Yanzu haka, ana shirin yi wa matar jana’iza.’
“Saboda haka, muna kira ga mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan wajen tafiya, domin an san cewa akwai manyan macizai a dajin.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An fara shigar da kayan agaji a Gaza
An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji.
DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu.
Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo An kashe ’yan ta’adda 45 a NejaSakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da mai sanyaya zuciya bayan damuwa da bala’in da mazauna Gaza suka tsinci kansu a ciki, yana mai fatar gaggauta shigar da kayayyakin agajin da kuma dorewarsa.
A yayin taron tattaunawa kan matsalolin da suke shafar ayyukan samar da abinci a Afrika ne Guterres ya faɗi cewa yunwa ba za ta taɓa zama makamin da za a yi amfani da ita wajen yaƙi a duniya ba.
Babban jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher ya yi maraba da matakin, yana mai cewa yanzu haka yana tuntubar kungiyoyi wadanda za su yi duk mai yiwuwa don isa ga mutane da dama da ke fama da yunwa a wannan lokaci.
Tuni dai kungiyoyin agaji suka gabatar da wasu korafe-korafe tun ba a yi nisa ba, don yi wa tufkar hanci muddin ana son kwalliya ta biya kudin sabulu a ayyukan agajin da aka fara bayan fiye da watanni uku da dakatar da su.
Ahmad Nadir, na kungiyar lafiya ta duniya WHO, ya ce tsame hannun Isra’ila daga batun karba da rabon kayan agaji ne kadai zai bai wa kwarraru kan ayyukan agaji damar gudanar da ayyukan da za a samu nasara.
A bayan nan ne Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce kashi uku na al’ummar Gaza ba su ci abinci na kwanaki ba, kuma mutane 470,000 suna cikin yanayi na juriyar tsananin yunwa wanda tuni ya kai ga mutuwar wasu.
Isra’ila dai na ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya, kan amfani da yunwa a matsayin makamin yaki kan al’ummar Falasdinu, lamarin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da shi.
Akwai yunwa ta gaske a Gaza —TrumpKo a wannan ɗin Litinin Shugaban Amurka Donald Trump ya ce “akwai yunwa ta gaske” a Gaza.
Shugaban na Amurka ya faɗi hakan ne bayan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nace kan cewa babu yunwa a yankin.
Da aka tambaye shi ko ya yarda da abin da Netanyahu ya fada cewar “ƙarya ce tsagwaronta” idan aka ce Isra’ila na ta’azzara yunwa a Gaza, shugaban na Amurka ya ce: “Ban sani ba…amma yaran nan da ka gan su, suna cikin yunwa…wannan yunwa ce ta gaske.”
Kalaman Trump na zuwa ne bayan shugaban hukumar kai agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana buƙatar abinci mai “ɗimbin yawa” domin magance halin yunwa da yankin ke ciki.