Darajar cinikayyar ba da hidima ta kasar Sin ta karu sosai, inda ta kai yuan triliyan 1.97 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 270 a rubu’in farko na bana, karuwar kashi 8.7 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Darajar jimillar hidimar fice ta kai yuan biliyan 835.15, karuwar kashi 12.

2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, yayin da darajar hidimar shige ta kai yuan triliyan 1.139, wanda ta nuna karuwar kashi 6.2 cikin dari.

Hidimomin tafiye-tafiye sun nuna karuwa mafi sauri na kashi 21.8 cikin dari. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin

Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba.

Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya.

Kama su ta biyo bayan sanarwar da aka yi a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda sojojin suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkan cibiyoyin gwamnati.

Jami’an da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa, sun ce sun karɓe mulki, sun rufe iyakokin ƙasar tare da dakatar da jam’iyyun siyasa.

Sai dai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma dakarun da suka tsaya kan gaskiya na dawo da doka da oda.

Gwamnati ta bayyana lamarin a matsayin aikin “tsiraru  mutane” da ba su da tasiri.

“Wasu ’yan tsiraru ne kawai da ya mamaye talabijin. Rundunar sojan ƙasa na sake karɓar iko. Birnin da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro,” in ji sanarwar fadar shugaban ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta 
  • Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki
  •  Kasashen Iran Da Turkiya Za Su Bunkasa Alakarsu A Fagen Ilimi Da Musayar Fasaha
  • An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”
  • MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya
  • Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
  • An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166
  • Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa