Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara amfani da cikakken tsarin amfani da Komfuta (CBT) ga dukkan jarabawar su nan da shekarar 2026. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin yayin ziyara da kuma duba yadda ake gudanar da gwaje-gwaje na CBT a cibiyoyin Bwari da kuma duba ɗakin gwajin jarrabawa JAMB a kwamfuta.

Alausa ya bayyana cewa, daga watan Mayu ko Yuni na 2026, duka ɓangarorin tambayoyin da aka saba na WAEC da NECO, na rubutu da na gwaje-gwaje, za su kasance a komfuta gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa wannan matakin na daga cikin manufar gwamnatin na magance matsalar satar jarabawa.

Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS WAEC Ta Kwace Lasisin Makarantu 574 Sakamakon Satar Amsa

Ministan ya kuma sanar da cewa an kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Daraktan JAMB, Prof. Ishaq Oloyede, wanda zai duba tsarin jarabawar Nijeriya gaba ɗaya, inda aka ce sakamakon binciken zai fito nan da ƙarshen watan gobe. Alausa ya yaba da ingancin gudanar da jarabawar UTME ta 2025 da JAMB, wanda ya bayyana a matsayin “matsayi na duniya” kuma yana cika ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

A cikin jawabinsa, Oloyede ya bayyana cewa UTME ta 2025 tana ɗaya daga cikin mafi kyawun jarabawar da aka taɓa gudanarwa, inda ya kuma bayyana cewa duk wani zargin rashin dacewar cibiyoyin jarabawa yana buƙatar hujja mai ƙarfi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: WAEC

এছাড়াও পড়ুন:

Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare

Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).

A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.

Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.

A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.

“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.

Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.

Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar