Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
Published: 27th, April 2025 GMT
“Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau.
“Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in ji Sarkin.
Ya yi addu’a Allah ya jiƙan mamatan ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.
Sarkin ya yaba wa gwamnati da sojoji bisa ƙoƙarinsu amma ya buƙaci a ƙara amfani da sabbin fasahohin zamani da kayan yaki masu ƙarfi domin yaƙar ‘yan ta’addan.
Ya yi gargaɗin cewa waɗannan hare-hare na iya tsoratar da manoma wajen komawa gonakinsu yayin da lokacin shuka ke gabatowa.
A wani ɓangare kuma, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sake kira ga rundunar soji da su ɗauki mataki wajen fatattakar ‘yan Boko Haram daga maɓoyarsu.
Gwamna Zulum ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, da sauran manyan hafsoshin soji a gidan gwamnatin jihar da ke Maiduguri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram Hari
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa.
Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025.
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a BornoAn sanar da wannan naɗin ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa da Hukumar CDCFIB, ta fitar, wacce sakatarenta, Abdulmalik Jibrin, ya rattaba wa hannu.
Wannan naɗin na zuwa ne bayan da shugaban hukumar na yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, ke shirin ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60 a duniya.
Olumode Samuel Adeyemi yana da ƙwarewa da gogewa a aikin kashe gobara.
Ya fara aikinsa a Hukumar Kashe Gobara ta Abuja, kafin daga bisani ya koma Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa, inda ya bi matakai har ya kai matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar a sashen kula da ma’aikata.
A tsawon lokacin da ya shafe yana aiki, ya samu horo da ƙwarewar da ake buƙata a cikin gida da kuma waje.
Haka kuma ya riƙe muƙamai daban-daban a hukumar, kuma memba ne a ƙungiyoyi irin su ANAN, Cibiyar Gudanar da Harkokin Kamfanoni ta Ƙasa, Cibiyar Gudanar da Harkokin Jama’a ta Ƙasa, da kuma Cibiyar Kula da Kuɗaɗe ta Ƙasa.
Hukumar ta yaba wa shugaban da zai ritaya, bisa gudunmawar da ya bayar da kuma irin shirye-shiryen da ya jagoranta a lokacin da yake shugabancin hukumar.