Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
Published: 30th, April 2025 GMT
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.
Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai EU ta zartas da matakan mayar da martani kan Amurka a zagaye na farko. Firaministan kasar Japan Ishiba Shigeru kuma ya bayyana a fili cewa, bai shirya mika wuya don cimma yarjejeniya kan harajin kwastam cikin hanzari ba.
Yanayin rudani da Amurka ke ciki cikin kwanaki 100 da suka gabata ya ilmantar da jama’a cewa, babu wanda zai yi danniya bisa ganin dama. Kuma babu wanda zai hana dunkulewar tattalin arzikin duniya. Hadin gwiwa mai kunshe da kowa da samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare, ita ce hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko kusa babu kamshin gaskiya a ciki, don ba a ga Umar a shirin ‘Gidan Sarauta’ zango na 4 ba, wannan ba dalili ne da zai sa a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanina da shi ba, domin kuwa; a duk wani shiri mai dogon zango, akwai lokacin da za a daina ganin jarumi, amma kuma daga baya ya sake bayyana.
Bashir ya kara da cewa, yanzu kamar yadda ake daukar fim din ‘Alakata da Nana Firdausi’, har wasu ma ke tunanin ko akwai maganar aure a tsakaninmu, duk da dai Allah ne ke yi; saboda yanzu haka, matata ’yar fim ce. Don haka, zuwa yanzu dai babu wani batu na aure tsakanina da Nana, kawai dai muna da fahimtar juna tsakaninmu, sannan kuma na yi amanna da yanayin aikinta, saboda duk wani aiki da za mu yi tare da ita; ina yaba aikin nata kwarai da gaske, saboda yadda ta ke mayar da hankali wajen ganin ta yi abin da ya dace, musamman ma aikin kamfanina.
Lokacin da yake amsa tambaya a kan burin da yake da shi a wannan masana’anta, Bashir ya ce; babu wani burin da yake da shi a yanzu da ya wuce a ce watarana ya dauki nauyin fim a wata kasa daban, ba Nijeriya ba; musamman Kasar Indiya.
“Burina yanzu a Masana’antar Kannywood, bai wuce ganin na zama ‘International Furodusa’ ba, wato ya kasance ina yin fina-finai ba a iya nan gida Nijeriya ba, har ma da kasashen duniya; musamman ma Kasar Indiya”, in ji shi.
“Domin kuwa, in dai ana iya yin fim a samu riba a Kasar Indiya, to ni ma ina fatan watarana a ce nayi, hakan ya sa tun a yanzu na fara gayyato wasu daga cikin jaruman da ba Arewacin Nijeriya suke aiki ba, kamar irin su Kanayo O. Kanayo da sauran makamantansu; domin su zo su taya ni aiki. Burin da nake da shi ga wannan masana’anta mai albarka, ba zai fadu ba; domin idan da zan samu dama, zan yi abin da zai sa Kannywood ta shiga duniya kowa da kowa ya santa”.
Ya ci gaba da cewa, harkar fim; ba karamar harka ba ce a idon duniya, kamar yadda wasu ke tunani. Dalili kuwa shi ne, a fim ne za ka samu daukaka, kudi da kuma masoya, sannan kuma a nan ne za ka bugi kirjin cewa; an san fuskarka, haka zalika an san sunanka, har inda ba ka yi tsammani ba, kuma a harkar fim ne kadai za ka taka kafarka inda ba ka taba tsammanin cewa; za ka iya takawa ba, misali a Nijeriya, duk inda gwamna ke tunanin an san shi, haka nan dan fim ma zai yi wannan tunani, domin kuwa ta hanyar fim sunansa ya zaga ko’ina.
A karshe, Bashir Abubakar Maishadda, wanda ake yi wa lakabi da ‘King Of Bod Office’, ya yi kira ga mutane da su daina raina mutum a duk inda suka gan shi, domin kuwa ba su san abin da zai zama a nan gaba ba, har ma ya yi misali da kansa, inda ya ce a farkon lokacin da ya shigo masana’antar, mutane da dama sun sha tsangwamar sa tare da toshe wasu hanyoyin da suke tunanin zai iya koyon wani abu, amma kuma yanzu da Allah ya mayar da shi abin da ya zama, sai suke mamaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp