Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa
Published: 29th, April 2025 GMT
Wata koutun soja ta yanke wa wani jami’inta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa.
Kotun da ta zauna a Hedikwatar Runduna ta 82 da ke Enugu, ta yanke wa Private Adamu Mohammed hukuncin kisa kan laifin budurwar taas mai suna Hauwa Ali.
Da yake sanar da hukuncin, Shugaban kotun, Birgediya Sadisu Buhari, ya ce, “Kotun Soja ta Kasa ta yanke hukuncin cewa sojan da ake tuhuma, mai lamba 21NA/80/6365 Private Adamu Mohammed, an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa tuhumar kisan kai.
Mukaddashin kakakin Rundunar, Jonah Unuakhalu, ya ce kwamitin kotun ya cimma matsaya ɗaya bayan nazari mai zurfi na shaidu, tarihin aikin wanda ake tuhuma, da kuma roƙon sassauci daga lauyansa.
Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kano: Galadima biyu a masarauta ɗaya Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a BornoYa shaida wa manema labarai a Abuja cewa kotun sojan, ta kuma yanke wa wani Soja mai suna Private Abubakar Yusuf hukuncin ɗaurin shekaru 10 a kurkuku saboda samun sa da laifin fashi da makami a wani shahararren kantin sayayya a Enugu.
Ya kara da cewa an yanke wa waɗannan mutane biyu hukuncin ne bayan kammala shari’o’insu kan laifukan kisan kai da fashi da makami.
Babban Kwamandan Runduna ta 82, Manjo-Janar Oluyemi Olatoye, ne ya kaddamar da kotun sojin a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, domin yanke hukunci kan shari’o’in da suka shafi ma’aikatan da suka yi kuskure a cikin Rundunar.
A cewarsa, waɗannan hukunce-hukuncen sai sun samu tabbatarwa daga hukumomin soji da suka dace, wanda ya nuna ƙarshen shari’o’in sojojin.
Ya sake jaddada ƙudurin Sojojin Najeriya na tabbatar da ɗa’a da kuma kiyaye mafi girman ƙa’idoji na ɗabi’u da ƙwarewa.
“Kuskuren ayyukan wasu kaɗan ba su nuna ƙimar ƙungiyar ba. A koyaushe ana ɗaukar matakai masu sauri da kuma ƙarfi don tabbatar da riƙon amana da adalci,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: budurwa
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Ilimi ta Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 18 a 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta ce za ta kashe fiye da naira miliyan dubu 18 domin gudanar da harkokinta a sabuwar shekara.
Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Lawal Yunusa Danzomo ne ya bayyana haka lokacin da yake kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Dr. Lawan Yunusa Danzomo ya ce zasu mayar da hankali ga aikin gina ajujuwa da gyaran wadanda suka lalace.
Za kuma a samar da littatafan darussa da tebura da kujeru domin inganta harkokin koyo da koyarwa.
Hakazalika za a gina bandakuna da samar da ruwan sha da wutar lantarki da tsaro.
Danzomo, ya ce aiwatar da haka zai yi matukar tabbatar da kyakkyawar da’irar ilimi da ta kunshi samar da ilimi cikin sauki ta hanyar shiga makaranta har a kammmala karatu.
Dr. Lawan Danzomo ya kara da cewar za a dauki malaman wucin gadi har su 4000 a karkashin shirin J-Teach.
Ya kuma yi nuni da cewar, za a shirya jarrabawa ga kason farko na malaman J-Teach su 1,450 na gwamnatin da ta gabata domin daukar su aiki na dindindin.
A nasa jawabin shugaban kwamatin ilimi matakin farkio na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Fagam, Alhaji Yahaya Zakari Kwarko ya bada tabbacin hadin kai da goyon baya domin samun nasarar da ake bukataa sabuwar shekara.