Leadership News Hausa:
2025-11-03@07:46:34 GMT

An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace A Kaduna

Published: 25th, April 2025 GMT

An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace A Kaduna

Farfesa Ibrahim Amos, wani Malamin cocin Katolika, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Kaduna, bayan an sace shi a ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025, daga gidansa a St. Gerald Quasi Parish, Kurmin Risga, ƙaramar hukumar Kauru.

Wani shugaba a ɗariƙar dake Kafanchan, Rev. Fr. Jacob Shanet, ya tabbatar da sakin farfesan a cikin wata sanarwa da aka mikawa manema labarai.

Ya bayyana cewa Farfesa Amos ya dawo lafiya jiya Alhamis ɗin da aka sace shi, amma bai bayyana yadda aka sake shi ba ko sun biya kuɗin fansa ba.

Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna

Rev. Fr. Shanet ya gode wa jama’ar alheri, da ƙungiyoyin addini, da jami’an tsaro, da sauran masu ƙoƙarin ganin an sake shi. Ya jaddada cewa, goyon bayan da aka samu daga kowanne ɓangare ya tabbatar da cewa ba su kaɗai ke ƙoƙarin tabbatar da darajar rayuwar dan Adam ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka

Daga Yusuf Zubairu Kauru 

Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.

Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.

A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.

Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.

Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.

“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.

Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba
  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC