Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
Published: 29th, April 2025 GMT
Ba wannan ne karo na farko da shugaba Trump ya nuna girman kai da rashin sani game da Afirka ba. A watan da ya gabata, lokacin da yake bayani game da dalilin da ya sa gwamnatinsa ke rage gudummawar jin kai da take bayarwa a duniya, ya ce a baya, Amurka ta samar wa kasar Lesotho gudummawar dala miliyan 8, amma “ba wanda ya taba jin sunan wannan kasa”.
Sai dai ban da girman kai da rashin sani, kalaman shugaba Trump ya kuma bayyana matsayin da gwamnatin kasar Amurka ta dade tana dauka a game da kasashen Afirka, wato a maimakon abokan hadin gwiwa na zaman daidaito da martaba juna, tana kallonsu a matsayin abin da take iya amfani da su wajen takara da sauran manyan kasashe, kuma muna iya ganin haka ne daga manufofin da mahukuntan kasar suka dauka cikin ‘yan shekarun baya.
A shekarar 2014, gwamnatin Barack Obama ta shirya taron kolin Amurka da kasashen Afirka karo na farko, inda ta dauki alkawura a gaban kasashen Afirka. Sai dai bayan taron, a maimakon ta kara samar da gudummawa, sai ta rage, har da kudaden da take samarwa a fannin yaki da cutar kanjamau a Afirka. A gun taron, Amurka ta kuma yi alkawarin zurfafa huldarta da kasashen Afirka da ma gudanar da taron a kai a kai, amma ba a sake yin taron ba har sai bayan tsawon shekaru 8. A karshen shekarar 2022, Amurka ta gudanar da taron karo na biyu, inda tsohon shugaban kasar Joe Biden ya yi alkawarin samar da iya abin da kasarsa take iya bayarwa don tabbatar da kyautata makomar Afirka, kuma a cewarsa zai kai ziyara Afirka a shekarar 2023, amma bai cika wannan alkawari ba sai zuwa karshen bara, lokacin da ya kusan sauka daga kujerar shugabanci, kuma ba mu san yaushe za a cika sauran alkawuran da ya dauka ba.
Bayan da gwamnati mai ci ta fara aiki, jerin matakan da ta dauka sun haifar da munanan illoli ga kasashen Afirka. In mun dauki misali da harajin kwastam na ramuwar gayya da ta dauka a baya bayan nan, inda ta sanya haraji mai yawa kan kasashen Afirka 51, ciki har da 50% a kan Lesotho da 47% a kan Madagascar da 40% a kan Mauritius, matakin da ya kasance tamkar yi wa kasashen fashi. Abin lura kuma shi ne, harajin ya dakatar da dokar samar da ci gaba da damammaki a Afirka da aka san ta da AGOA, tun kafin wa’adinta ya cika, lamarin da ya jefa kasashen Afirka da dama cikin mawuyacin hali wajen yin ciniki da Amurka.
Har kullum kasar Sin na ganin cewa, Afirka dandali ne na hadin gwiwar kasa da kasa, a maimakon wajen yin takara tsakanin manyan kasashe. Rashin girmamawa ne ga kasashen Afirka da al’ummarsu yadda Amurka take da rashin sanin nahiyar, kuma rashin sahihancin da take wa hadin gwiwarta da kasashen Afirka ya shaida gazarwata ta daukar kasashen Afirka da muhimmanci. Kasashen Afirka na bukatar kawaye na gaske. Idan gwamnatin Trump tana son samun karbuwa daga kasashen Afirka, dole ne ta gyara matsayinta, kuma ya kamata ta fara da fahimtar kowace kasa da ke nahiyar. (Mai Zane: Mustapha Bulama)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar.
Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci.
Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku.
Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace.
Ya kara da cewa, “Kasancewar manyan jami’an Nijar a taron da kuma kwamitin hadin gwiwa wani mataki ne mai ban sha’awa na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.”
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa, bunkasa alaka da Nijar abu ne mai matukar muhimmanci, “idan aka yi la’akari da matsayinta kan ci gaban yanki da na kasa da kasa da kuma ra’ayi daya kan batutuwan Falasdinu da Lebanon.”
A yayin da yake tsokaci ga kiran da ministan na Nijar ya yi na inganta alaka a fannin noma, man fetur, da makamashi mai dorewa, Aref ya bayyana wadannan fannoni guda uku a matsayin muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar Iran da Nijar, wadanda ya ce kwamitin hadin gwiwa zai duba su.
Yayin da yake tsokaci kan dangantakar tattalin arziki, ya ce, ya kamata kamfanoni masu zaman kansu na kasashen biyu su zuba jari don ciyar da matakin hadin gwiwa zuwa matsayi mafi girma.