Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
Published: 29th, April 2025 GMT
“Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi.
El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC.
Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba.
“Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan ba don kaina ba ne – don ceton ƙasa ne,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dole a zaɓi shugaban ƙasa mai nagarta da hangen nesa, ba wai kawai din ya fito daga wata jiha ba.
“Matsalolin da muke fuskanta sun fi girman la’akari da inda mutum ya fito. Muna buƙatar shugabanni masu hangen nesa da ƙwarewa don gyara Nijeriya,” ya bayyana.
Da yake magana kan sauya sheƙar wasu ‘yan siyasa zuwa APC, El-Rufai ya ce jam’iyyar SDP tana mayar da hankali ne kan gina goyon baya daga jama’a, ba wai kawai neman manyan ‘yan siyasa ba.
“Gwamna ɗaya yana da ƙuri’a ɗaya ne kawai. Jama’a ne ke yin zaɓe, ba manyan ‘yan siyasa ba,” ya jaddada.
A ƙarshe, El-Rufai ya ce tafiyar SDP tana ci gaba da karɓuwa a dukkanin sassan Nijeriya, ba a yankuna kaɗan kaɗai ba.
“Muna ci gaba da gina goyon baya a faɗin ƙasar nan. Aikin gina ƙasa yana faruwa ne a tsakanin talakawa, ba kawai a kafafen yaɗa labarai ba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi
Tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Najeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi abin damuwa ne da ke da ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar.
Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa na X.
Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jalloObi ya bayyana cewa, barazanar turo sojojin Amurka su yaƙi ta’addanci da ma sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurkan take da damuwa da su, lamari ne da dole dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar ya ja masa hankali.
“Babu shakka Nijeriya na fama da matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da ma asarar dukiya.
“A cewar Ƙungiyar Amnesty, aƙalla mutum 10,000 aka kashe a Nijeriya daga watan Mayun 2023, kuma kamar yadda na sha nanatawa, kashe-kashe a Najeriya abin takaici ne, kuma abin Allah-wadai da ya zama dole a tashi haiƙan wajen magancewa.”
Obi ya ce za a iya magance matsalar ta hanyar samun shugabanci na nagari, “duk da cewa ba a wannan gwamnatin matsalar ta fara ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin takaɓus daga ɓangaren wannan mulkin na gwamnatin APC wajen tunkarar matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.”
Ya ce Najeriya da Amurka suna da tarihin alaƙa da juna mai kyau, “kuma bai kamata a watsar da wannan alaƙar ba a yanzu.
“Wannan sabuwar dambarwar na buƙatar haɗakar diflomasiyya da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu domin lalubo hanyoyin magance matsalar.”
Barazanar da Trump ya yi wa NijeriyaA bayan nan ne dai Shugaba Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirye-shiryen yiwuwar kai hari ƙasar, bayan ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a ƙasar.
Trump ya bayar da umarnin ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, kwana guda bayan da ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Tinubu ya mayar da martaniShugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin-kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ’yan ƙasa daga kowane yanki da addini.
Tinubu ya ƙara da cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ’yancin yin addini.