Wace Kungiya Ce Za Ta Lashe Kofin Zakarun Turai?
Published: 26th, April 2025 GMT
Kungiyar kwallon kafa ta PSG – wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar Zakarun Turai ta bana saboda karfin da tawagar take da shi sannan kuma kungiyar a gine take hadi da kwararren mai koyarwa, Luis Enrikue, tsohon kociyan Barcelona da Roma da tawagar kasar Spaniya, yana daya daga cikin kwararrun masu horarwa.
Wani shahararren masanin wasanni dan kasar Sifaniya, Guillem Balague na ganin PSG ce za ta lashe gasar. ”Suna da duk wani abu da ake bukata domin lashe kofin, sun iya rike kwallo, a yanzu kungiyar na da karfi, tana da masu kai hari, da na tsakiya haka ma masu tsaron baya”
Ya kara da cewa hanya guda da za a iya doke kungiyar ita ce idan ‘yan wasanta suka tare a baya domin tsare gida. ”In dai suka tsananta tsare gida to sai an cinye su, amma idan za su fito, to komai zai iya faruwa” a cewarsa.
Sai shi ma Phil McNulty, babban marubucin wasanni na BBC na ganin PSG ce za ta yi nasara a gasar. ”Suna da zaratan ‘‘yan wasa masu kai hari, misali Ousmane Dembele da Khbicha Kbaratskhelia da a yanzu ke kan ganiyarsu, ga kuma Desire Doue da Bradley Barcola wadanda matasan ‘yankwallo ne masu hazaka ”, in ji shi.
Inter Milan
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, kungiya ce wadda za a iya cewa babu mai kwarinta a kasar Italia domin yanayin yadda take buga wasa da yadda ba ta bari ana zura mata kwallaye a raga abu ne wanda ya kamata a kalla, sannan kuma akwai zakakuran ‘yan wasa da dama da za su taimaka wajen ganin kungiyar ta kai wasan karshe tare kuma da lashe kofin.
Shima babban wakilin sashen wasanni na BBC, Ian Dennis ya ce Zakarun na Italiya na da kwarin gwiwar lashe gasar, saboda yadda kungiyar ke da karfi musammna masu tsaron bayanta. Ya ce ”Sun fi kowace kungiya da ta rage a gasar karfin tsaron baya, kawo yanzu babu mai tsaron ragar da ya kai Yann Sommer, hana kwallo shiga raga a wasannin gasar ta bana’.
Ya kuma ce ta bangaren masu kai hari ma, kungiyar na da maciya kwallo, musamman Lautaro Martinez da a yanzu ke kan ganiyar zura kwallaye. Sannan wannan ne karo na biyu a kaka uku da kungiyar ke kai matakin wasan kusa da na karshe. Kuma kungiyar – da ke jan ragamar teburin Gasar Serie A – za ta hadu ne da Barcelona a wasan na kusa da karshe.
Arsenal
Kamar yadda kowa ya sani kungiyar Arsenal ce ta fitar da Real Madrid daga gasar a matakin kusa da na kusa da na karshe bayan doke ta 5-1 gida da waje. Wakilin sashen wasanni na BBC, Aled Howell na ganin kungiyar ce za ta lashe gasar. ”Duk da matsalolin da kungiyar ta fuskanta a bana, amma ta iya kai wa wannan mataki a gasar, ai kasan sun shirya wa gasar”, in ji shi.
”Ta fannin tsaron gida, kungiyar na da karfi sosai, haka idan ka duba ‘yan wasan gabanta hadakar Saka da Martinelli da Odegaard za su iya doke duk wata kungiya da suka ci karo da ita.
Kungiyar ta Mikel Arteta, wadda ke matsayi na biyu a teburin Gasar Premier ba ta taba lashe gasar ba a tarihi kuma ‘yan wasan kungiyar irinsu William Saliba da Bukayo Saka da Martin Ordegaard sun bayyana cewa suna son su rubuta sabon tarihi a kungiyar saboda haka za su yi iya yin su domin ganin cewa sun dauki gasar a karon farko a tarihin kungiyar.
Barcelona
Ita kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kungiya ce wadda a yanzu babu kungiyar mai sharafinta kuma ita ce ta fitar da Borussia Dortmund daga gasar. Babban wakilin sashen wasanni na BBC, Simon Stone ya ce yana ganin kungiyar ta Sifaniya ce za ta lashe gasar, saboda yadda take kara farfadowa a baya-bayan nan. ”A yanzu kungiyar ta kara karfi musamman bayanta da tsakiya da masu kai hari”, in ji Simon Stone.
Kungiyar, wadda ke matsayi na daya a gasar La Liga na da zaratan matasan ‘yan wasa da ke haskakawa a fagen kwallon kafa da suka hada da Lamine Yamal da Cubersi da Balde da Fermin da Gabi da sauransu. Sanann rabon da kungiyar ta lashe gasar tun 2015 lokacin da take da zaratan ‘yanwasa irin su Lionel Messi da Luis Suares da kuma dan wasa Neymar na Brazil.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ta lashe gasar wasanni na BBC masu kai hari kwallon kafa kungiyar ta da kungiyar Kungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu
Hukumomin ’yan sandan Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke na daƙile munanan laifuka a ƙasar.
Na baya-bayan nan dai shi ne ceto mutanen da aka sace, da kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ƙwato manyan bindigogi da alburusai a jihohin Delta da Katsina.
Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a AustraliaA wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce a jihar Katsina an samu gagarumar nasara a ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda haɗin gwiwar JTF da suka haɗa da jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suka daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a hanyar ƙauyen Danmusa zuwa Mara Dangeza a ƙaramar hukumar Danmusa.
Adejobi ya ce hakan na iya yiwuwa ne ta hanyar shigar da wasu gungun ’yan bindiga da suka yi yunƙurin guduwa da waɗanda aka yi garkuwa da su a wani artabu da ya kai ga ceto mutum 11.
Nasarar da aka samu yankin Kudu maso KuduA halin da ake ciki kuma, a yankin Kudu maso Kudu, Jihar Delta, hukumar ’yan sanda ta kama wani Abubakar Hassan, wanda babban wanda ake zargi da aikata laifin satar mutane ne a tsakanin jihohin Delta da Ribas da Imo, da Enugu.
Jami’an da ke da alaƙa da samun nasarar sun yi hakan ne yayin da suke aiki da sahihan bayanai.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, Hassan ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci gudanar da hari a yankin Ughelli-Ozoro na jihar mai arzikin man fetur.
Ya kuma jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa maɓoyarsa a wani daji da ke Ozoro. A can jami’an sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da tarin alburusai huɗu da harsashi guda talatin da biyu.