Tawagar ‘Yan Sama Jannati Na Shenzhou 19 Za Su Dawo Doron Kasa A Ranar Talata
Published: 28th, April 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba.
Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu.
Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na banaAn tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci.
Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS.
Haka kuma, ya nemi a mayar da waɗanda ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali domin suke samun damar ganawa da lauyoyinsu cikin sauƙi.
Lauyan DSS, David Kaswe, ya ƙi aminta da wannan buƙata.
Ya ce lauyoyin dole ne su rubuta wa DSS buƙatunsu kafin su ziyarci waɗanda ake tuhuma.
Alƙalin kotu, Emeka Nwite, ya yanke shawarar bai wa lauyoyin waɗanda ake tuhuma ƙarin lokaci domin shirya wa shari’ar.
Ya ce wannan zai tabbatar da adalci, sannan ya sanya ranar shari’a 15 ga watan Janairun 2026, domin fara sauraren shari’ar.
DSS, tana zargi waɗanda ake tuhuma da jagorantar kai harin gidan yarin Kuje da ke Abuja a 2022, inda fursunoni sama da 600 suka tsere.
Hakazalika, ta zarge su da kai hari wajen haƙar ‘uranium’ a Jihar Neja, tare da sace mutane da dama, ciki har da injiniyan ƙasar Faransa, Francis Collomp, a shekarar 2013.