Kasar Sin Ta Kyautata Tsarin Mayar Da Kudin Haraji Domin Karfafa Gwiwar Yin sayayya A Kasar
Published: 27th, April 2025 GMT
Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki.
Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da shakatawa da wuraren raya al’adu da filayen jiragen sama da otel-otel da tashoshin tafiye-tafiye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ƙaryata jita-jitar kai wa coci hari a Gombe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ce labarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na kai wa cocin ECWA da ke Kashere hari, ba gaskiya ba ne.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana haka, inda ya ce sun bincika tare da gano cewar jita-jita ce.
Ya ce DPO na Pindiga da shugaban ofishin ’yan sanda na Kashere, sun tuntuɓi wani dattijo da ya halarci cocin domin yin addu’a a ranar Lahadi.
Dattijon ya shaida musu cewa babu wani abu da ya faru, kuma ’yan sanda suna harabar cocin tun safe a domin kula da sha’anin tsaro kamar yadda suka saba.
Rundunar ta ce yaɗa irin wannan jita-jitar na iya tayae da hankalin jama’a.
Ta kuma ce ta fara bincike domin gano wanda ya ƙirƙiri wannan labari domin ɗaukar matakin doka a kansa.
DSP Abdullahi, ya roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da ci gaba da harkokinsu, inda ya tabbatar da cewa ’yan sanda za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.