Iran Ta Musanta Zargin Nethalands Na Cewa Tana Da Hannun A Kokarin Kisa A Kasar
Published: 25th, April 2025 GMT
Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu a shekarar da ta gabata.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tace Ofishin jakadancin Iran da ke Netherlands ta fidda wannan sanarwan ne a jiya Alhamis.
Ta kuma kara da cewa, kasar Iran wacce ta fi ko wace kasa a duniya fama da yan ta’adda, ba za ta yi kokarin kasashe wani a wani wuri ba.
Sanarwan ta bayyana cewa wannan al-amarin siyasace ta tsakanin jami’an siyasa na kasar ta Netherlands don neman amincewar masu kuri’a.
Kafin haka dai wata cibiyar ayyukan tsaro ta kasar Netherlands mai suna AIVD ta bada rahotomta na shekara shekara kan abinda ya shafi ayyukan ta’addancin inda ta ammabi kasar Iran a ciki.
Har’ila yau wannan rahoton yasa ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Netherlands ta kira jakadan JMI a kasar zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don gabatar da korafinta.
Gwamnatocin kasashen Turai musamman kasar Faransa tana gudanar da taron yan adawa da JMI a kasashensu, wadanda kuma sune suka kashe Iraniyawa da dama a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya.
A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran mai girma. Qalibaf ya yi nuni da cewa, wannan mutum mai rauni yana son canza haryar tafiyarsa a kullum rana saboda tsoron kada a kama shi sakamakon kasancewarsa mai laifi da yafi zama abin ki a tarihin wannan zamani.
Qalibaf ya kara da cewa; Bayan shafe shekaru da dama Netanyahu yana yaudarar kafafen yada labarai, a halin yanzu gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta fito fili kuma ta bayyana hakikanin fuskar wannan azzalumi ga duniya, musamman ga matasan Amurka da Turai. Qalibaf ya kara da cewa babu wani abin da wannan gwamnatin ta cimma sai kai hare-haren bama-bamai kan makarantu da asibitoci, kuma ba ta cimma burin da ta ayyana a farkon yakin ba, kuma halin da ake ciki yana da matukar rashin tabbas.