Shugaban rikon kwarya na kasar Siriya Ahmed Al-sharaa ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta samar da hulda da HKI a dai-dai lokacinda ya dace.

Jaridar Middle East Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Ahmed Sharaa yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa shugaba Donal Trump

Har’ila yau shugaba Al-sharaa ya fadawa wani dan majalisar dokokin kasar Amurka kan cewa gwamnatinsa zata samar da huldar jakadanci da HKI a lokacinda ya dace, sannan a bangaren kasar Siriya kuma tana bukatar da farko a dagewa kasar takunkuman da aka dora mata, sannan yana son a yi maganar yankunan kasar Siriya wadanda HKI ta mamaye bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Dan majalisar dokokin kasar ta Amurka Cory Mills na hannun daman Trump ya ziyarci kasar Siriya a makon da ya gabata inda ya gana da shugaban, na kimani minti 90, don tattaunawa wadannan al-amura

Mill dai wanda ziyarci kasar ta tare naukar nauyin yan kasar Siriya a Amurka ya bayyana kamfanin dillancin labaran Bloomberg kan cewa ya fadawa shugaban matakan da yakamata ya dauka don ganin an daukewa kasar takunkuman tattalin arziki.

Ya kuba bukaci shugaban wargaza sauran masana’antun makaman guba a kasar, ya shiga cikin kasashen yankin masu yaki da ayyukan ta’addanci, ya kuma san yadda zai yi da yan kasashen waje wadanda suke cikin HTS, wanda suka taimaka masa ya sami damar kifar da gwamnatin Bashar al-asad.  Sannan dole ne ya amintar da HKI kan cewa ba zai kai mata hari ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Siriya

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja

Ya ce ya sayi layin wayar ne daga hannun wani Audu, ɗan kungiyar Vikings wanda ya tsere yanzu.

A wani lamari kuma, ‘yansanda sun kama wasu mutum huɗu da suka shiga gonar wani mutum a Lapai Gwari, inda suka saci kifi da darajar kuɗinsu ta kai Naira 750,000.

Babban wanda ake zargi, Hussaini Garba, ya amsa laifi tare da bayyana Ahmed Yusuf, Ibrahim Musa da Abdulazeez Bawa a matsayin mutanen da suke sayen kifin idan ya sato.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna  Bago