ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno
Published: 30th, April 2025 GMT
Ƙungiyar ISWAP mai yaƙi da tayar da ƙayar baya a yammacin Afirka, ta ɗauki alhakin harin da ya yi ajalin mutum 26 a Jihar Borno.
Ƙungiyar ta iƙirarin ɗaukar alhakin harin ne a wani saƙo da ta wallafa a shafin Telegram kamar yadda BBC ya ruwaito.
Aminiya ta ruwaito yadda wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.
Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da PortugalMajiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata.
Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta tafiya Gamboru Ngala ne daga Rann lokacin da suka isa inda ‘yan ta’addan ISWAP suka ɗana bam ɗin.
Bayanai sun ce baya ga mutum 26 da suka mutu, ƙarin mutum uku sun ji munanan raunuka.
“Mun tura wasu masu ba da agajin gaggawa inda lamarin ya auku domin kwashe mutane tare da tabbatar da tsaron sauran fararen-hula a wurin,” kamar yadda wata majiyar sojin da ba ta yarda a bayyana sunanta ba ta shaida wa Anadolu.
Ali Abass, wani ganau wanda ke tafiya a kan hanyar a lokacin da lamarin ya auku, ya ce sojojin da ‘yan sa-kai sun kai waɗanda suka jikkata wani asibiti.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Harin yana zuwa ne yayin da hare-hare ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, inda ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke ƙara ƙaddamar da hare-haren bama-bamai da kwanton-ɓauna kan motocin fararen-hula da na sojoji.
An ba da rahoton hare-hare irin wannan a ranakun 21 ga watan Maris da 12 ga watan Afrilu. Kawo safiyar ranar Talata dai, jami’an tsaro a Borno ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ISWAP jihar Borno da lamarin ya
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya ta bayyana sabbin mutanen da suka mutu sakamakon harin Suweida
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Siriya (SOHR) ta bayyana wasu sabbin fararen hula tara da aka ci zarafinsu a lokacin abubuwan da suka faru a Suweida a watan Yulin da ya gabata.
Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta bayyana cewa, wadanda aka kashen da suka hada da mata biyu, an kashe su ne a filin wasa a lokacin da wasu ma’aikatun tsaro da na cikin gida na gwamnatin rikon kwarya suke lardin na Suweida, tare da halartar mayakan ‘yan kabilar Larabawan Bedouin.
Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta ce adadin mutanen da suka mutu a watan Yulin da ya gabata a tsakanin al’ummar Druze a Suweida ya kai 1,592, yayin da adadin wadanda suka mutu tun safiyar Lahadi 13 ga watan Yuli, sakamakon arangama, da kisa a fili, da kuma harin bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai ya kai 2,047.
Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta yi bayanin cewa, “a ci gaba da bincike, akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu, ganin cewa akwai wadanda suka bace daga irin wadannan abubuwan da har yanzu ba a tantance makomarsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci