Hakimin Kafin Hausa Ya Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyuka Cigaban Al’umma
Published: 27th, April 2025 GMT
Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa.
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Umar Namadi ya yi jinjina ga marubucin littafin bisa rubuta cikakken tarihi da zai amfani al’umma, musamman matasa masu tasowa.
Malam Umar Namadi ya kuma yi alkawarin umurtar ma’aikatar ilimi ta jihar da ta sayi kwafin littafin domin amfanin ɗalibai a makarantun gwamnati.
Gwamna Umar Namadi ya kuma sayi kwafi bakwai na littafin a madadin iyalinsa kan kudi naira miliyan daya, yayin da Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar ta sayi kwafi kan kudi naira miliyan biyu, sannan Sanata mai wakiltar Jigawa Arewa Gabas ya sayi littafin kan kudi naira miliyan daya.
Sauran sun hada da Kananan Hukumomin da ke karkashin Masarautar Hadejia, inda kowanne ya bayar da gudummawar naira dubu dari biyu, Shugaban Karamar Hukumar Kafin Hausa ya bayar da naira dubu dari biyar, tare da wasu hukumomin gwamnati, da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma mutane daban-daban.
An tara sama da naira miliyan bakwai a yayin kaddamar da littafin tarihin Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, a garin Kafin Hausa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa naira miliyan Umar Namadi
এছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar
Ta ce, yayin ziyarar, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai zurfafa musayar ra’ayoyi tare da jagororin kasar Masar, game da ciyar da alakar sassan biyu gaba, da zurfafa hadin gwiwa mai samar da gajiya, da batutuwan dake jan hankulan sassan biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp