Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork  ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude.

Jaridar Middle eart Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Al-shaibani ya na cewa takunkuman suna hana ruwa guda a cikin al-amura da dama a kasarsa, kuma suna hana kafuwar gwamnatinsa su kamar yadda ya dace.

Ministan ya ce dage takunkuman ya zama wajibi don samun ci gaban kasar don kuma rage matsin lamban da mutanen kasar suke ciki.  Kasashen yamma musamman Amurka da tarayyar Turai da kuma MDD sun dorawa gwamnatin tsohon shugaban kasar Bashar al-asada takunkuman tattalin arziki, don bawa yan tawayen da suke taimakawa nasara a yakin basabsan da aka dauki shekaru kimani 14 ana fafatawa a kasar.

Ya zuwa yanzun dai kasashen Burtaniya da tarayyar Turai da kuma Amurka duk sun daukewa kasar wasu takunkuman tattalin arzikin. Amma har yanzun akwai wasu da dama wadanda ba’a dauke ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya.

Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi

Bankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito.

Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba da tafiyar hawainiya.

Bankin Duniyar ya ce har yanzu mahukuntan Nijeriya ba su ɗauko hanyar fitar da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki talakawan ƙasar ba.

A cewarsa, abin takaici ne yadda talakawan ƙasashe masu tarin albarkatu ke fama da talauci saboda rashin mayar da hankali daga shugabanni.

Bankin ya ce duk da ci gaban da Nijeriya ta samu a sauran fannonin da ba na man fetur ba musamman a bara, amma duk da haka babu alamar samun ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin talakawan ƙasar ta yammacin Afirka.

Rahoton ya jaddada cewa har yanzu yankin ƙasashen Sahel ne ke kan gaba a talauci a duniya gaba ɗaya, yayin da yankin ke da kaso 80 adadin mutane miliyan 695 na mutanen da ke fama da baƙin talauci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki
  • Xi Jinping Ya Bukaci A Hada Karfi Wajen Farfado Da Kasar Sin
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA