Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa.

(Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin. Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa babu ma’aikatan jinya da za su duba ta da sauran wadanda aka shirya za a duba su a ranar Alhamis. Da aka tambaye ta game da matakin da za ta dauka na gaba, Misis David ta ce za ta koma gida har sai an dakatar da yajin aikin. Mista Nde Danladi John daga karamar hukumar Kanke wanda shi ma ya zo ya kwashe iyalinsa, ya ce babu wanda ya duba su a asibiti tun ranar Laraba. Haka kuma, a sashen kula da lafiya na matakin farko na Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, ba a ga wata ma’aikaciyar jinya da ke kula da marasa lafiya ba yayin da likitan da ke bakin aiki ya halarci wasu tsirarun marasa lafiya, ya ce sauran su dawo ranar Juma’a. Wakilinmu ya ruwaito cewa, yajin aikin da aka fara da tsakar daren ranar 30 ga watan Yuli, 2025, ya janyo janyewar ma’aikatan jinya da ungozoma baki daya a dukkanin cibiyoyin lafiya na tarayya da ke fadin kasar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing
  • Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato
  • INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Shugaban Ivory Coast Ouattara zai sake takara wa’adi na huɗu
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Babu Wata Karamar Hukumar Dake Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
  • NiMet Ta Yi Hasashen Samun Mamakon Ruwan Sama A Sassan Nijeriya Cikin Kwana 3