Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum
Published: 25th, April 2025 GMT
Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu.
Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano
A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan Naira 70, kafin samun wannan karancin wutar lantarki, wanda a halin yanzu kuma ake sayar da ita kan Naira 120.
“Muna wahalar samun ruwan sha da arha a wannan yanki namu, manyan hanyoyin samun ruwa a Kano su ne, ta hanyar rijiyoyin burtsatsai (Boreholes), sannan ana iya samun ruwan ne ta hanyar amfani da wutar lantarki.
Don haka, da zarar an ce babu wutar lantarki, dole ne masu sayar da ruwan su nemi wata hanya daban, wanda hakan zai sa dole sayar da ruwan ya yi tsada. Sannan, a inda babbar matsalar take shi ne, ba kowa ne zai iya amfani da inji wajen samar da ruwan ba, wanda hakan ke kara sanya wa a samu karancin ruwan matuka gaya a wasu wurare”, in ji shi.
A wasu wuraren, labari ya iske mu cewa; wasu tun karfe shida na safe suke fita neman masu sayar da ruwa, sannan su kuma masu sayar da ruwan na ikrarin cewa; a kan layin neman ruwan suka kwana, don kawai su samu ruwan da za su sayar a wannan rana.
An kuma bayyana cewa, kankarar da ake sayar da ita Naira 100, yanzu ta koma 200.
Me Yasa Aka Samu Matsalar Wutar Lantarki?
Da yake magana kan matsalar katsewar wutar lantarkin a jihar, babban jami’in sadarwa na KEDCO, Sani Bala Sani, a cikin wata sanarwa da ya bayar ranar Asabar, ya bayyana faruwar hakan ne kan kokarin da ake yi na sake sabunta kayan aiki na rarraba wutar lantarkin.
Yayin da yake bayar da hakuri, kan ci gaba da matsalar da ake fuskanta ta wutar lantarkin, Sani ya ce kamfanin na kan kokarin kawo karshen matsalar, wanda hakan ke bukatar lura wajen aikin da kuma tsaron Injiniyoyinsu.
“Muna neman gafara ga abokanan cinikayyarmu masu girma da kima a wajenmu, sakamakon raguwar wutar lantarki da aka samu a halin yanzu.
“Ku tuna cewa, mun samu ci gaba kwarai da gaske wajen inganta rarraba wutar lantarki, wanda sakamakon a bayyane yake, ana samun wutar na tsawon awanni, ba tare da katsewa ba, sannan muna amsa kokenku cikin gaggawa, muna kuma ba ku wutar daidai gwargwado.”
Mun dage wajen yin wadannan gyararraki ne, sakamakon ganin yadda lokaci na Damuna ke karatowa, wannan ne ya tilasta mana sake bunkasa hanyoyin samar da wutar, don gudun samun katsewarta.
“Muna matukar ba ku hakuri da dukkanin matsalolin da aka samu tare kuma da tabbatar muku da cewa; wutar za ta dawo kamar yadda aka saba da zarar an kammala aikin. Muna godiya da uzurin da kuka yi mana da kuma hakurin da kuka yi”, in ji Sani.
A Jihar Jigawa, mutane sun koma amfani da rijiyoyin da aka yi watsi da su don samun ruwa, sannan kuma an dakatar da wasu sana’o’i daban-daban da suka hada da Walda da sauran masu alaka da ita, sakamakon karancin wutar lantarki.
Har ila yau, an kuma gano cewa; karancin ya shafi farashin wasu kayayyaki kamar Man girki da Kankara da kuma cajin Waya, sakamakon yadda masu gudanar da aikin suka kara kudade, domin karin da su ma suka samu.
A cewar wani mai sana’ar sayar da ruwan, Sani Talle ya ce; kwana uku kenan ba su samu wutar lantarki a yankinsu ba, wannan dalili ne ya sa bai loda ruwa a motarsa ba, sakamakon karancin wutar lantarkin a fadin jihar. Ya kara da cewa, karancin wutar lantarkin, ya tilasta wa masu sayar da ruwa yin watsi da manyan motocinsu, tare da neman wasu hanyoyin da za su ciyar da kawunansu.
“Wutar awa biyu ko uku kacal suke bayarwa a rana, sannan kuma a nan Jigawa, hanyoyin samun ruwan su ne, rijiyar birtsatsai (boreholes), sannan za ka yi mamakin yadda cikin awa biyu kacal wutar lantarki ke jan ruwa zuwa wannan rijiya. Yanzu haka, kwana uku kenan ina zaune babu ruwan d azan sayar. Idan ka zaga yanzu, za ka ga yadda mutane suka koma amfani da ruwan rijiyar da a da suka yi watsi da ita”, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, akwai da dama daga cikin masu irin sana’ar tasa da suke tunanin barin sana’ar su nemi wata, sakamakon irin wannan matsala da kan faru dangane da wutar lantarki.
Har ila yau, tattaunawa ta barke a shafukan sada zumunta na Nijeriya, inda ake yin korafin cewa; sai tsawon wane lokaci KEDCO, za ta yi magana kan wannan matsala ta rashin wutar lantarki.
Da yake mayarwa da kamfanin KEDCO martani a shafinta na Twitter (D), Abdulmalik Attah ya bayyana uzurin da kamfanin ya bayar a matsayin ‘labara’ kawai, inda ya kara da cewa; hakan na nufin ba za a samu wutar lantarki ba, har nan da zuwa tsawon mako uku, idan aikin ya ɗauki tsawon wannan lokaci.
Wani shi ma, mai amfani da shafin na sada zumunta (D), Muhammad Madaka ya ce, sanarwar da kamfanin ya bayar, a makare ta zo, wadda kusan ana iya cewa; ba ta da wani amfani.
“Sai bayan kun ji mutane suna ta faman korafi ne, sannan kuka yanke shawarar kawo wannan uzuri na sanarwa, babu wani lokaci da ake da yakini wannan aiki naku zai kammalu.”
Rabiu Adam, wanda ya yi wa hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) sharhinsa, ya yi zargin cewa KEDCO na bai wa Kani fifiko, sakamakon yadda Katsina ke shan wahala a hannunta (KEDCO).
“Ko ma’aikatan KEDCO da ke Jihar Katsina, ba su san dalilin katsewar wutar lantarkin ba, kusan mako guda kenan babu wutar, don haka batun cewa; ba wata babbar matsala ba ce, rainin wayo kawai.”
An Rufe Matsakaita Da Kananan Kamfanonin A Jihar Katsina
Haka ma al’amarin yake a Jihar Katsina, yayin da mazauna yankin suka yi ikrarin cewa; ba sa samun wutar da ta wuce awanni uku a rana. Kazalika, sun kuma bayyana yadda kamfanoni ke rufewa, sakamakon wannan matsala ta katsewar wutar lantarkin.
Hukumar Kula Da Wutar Lantarki Ta Kasa Ta Ci Tarar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantar Takwas
Wannan dai, na zuwa ne mako biyu bayan Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC), ta sanar da cin tarar wasu Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarkin (DisCos), su kimanin takwas Naira miliyan 628,031,583.94, sakamakon karya dokar da ta sanya a kan kudin da aka kiyasta ga kwastomomin da ba a tantance ba.
A cewar Hukumar ta NERC, kamfanonin da suka hada da KEDCO, an ci tarar su ne bisa ga sashe na 34(1)(d) cikin baka, na dokar samar da wutar lantarki ta 2023 da kuma rashin cika ka’idojin da hukumar ta fitar a tsakanin watan Yuli da kuma na Satumbar 2024.
Sauran, sun hada da Hukumomin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja, Iko, Inugu, Ikeja, Jos, Kaduna da kuma Yola.
Fadar Shugaban Kasa Na Shirin Kashe Naira Biliyan 10 Don Sama Wa Kanta Wutar Lantarki
A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke fama da matsalar wutar lantarki, fadar shugaban kasa na shirin kashe Naira biliyan 10 wajen samar da wuta ga fadar shugaban kasar.
Kamar yadda aka samu lamuni a 2025, aikin samar da wutar lantarkin da aka yi wa lakabi da “Samar da wutar lantarki ta hanyar na’ura mai amfani da hasken rana a fadar shugaban kasa”, wanda aka ware wa Naira biliyan 10 a cikin kasafin kudin da za a batar ayyukan fadar ta shugaban kasa.
Matakin na zuwa ne daidai lokacin da ake kara nuna damuna kan rashin tabbacin wutar lantarki da kuma tsadar wutar kan daidaikun al’ummar wannan kasa da kuma sauran cibiyoyin gwamnati.
Ana sa ran aikin samar da hasken wutar zai rage dogaro ga tsarin samar da wutar lantarki na kasa tare kuma da takaita tasirin karin kudin fiton, kan kudaden gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Jigawa Wutar Lantarki samar da wutar lantarki karancin wutar lantarki da wutar lantarki ta da Wutar Lantarki ta fadar shugaban kasa masu sayar da ruwa Da Wutar Lantarki wutar lantarkin sayar da ruwan
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce a halin yanzu jam’iyyar APC ba ta buƙatar dawowar Kwankwaso cikinta saboda tasirinsa a siyasance na ci gaba da gushewa.
DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a BornoDarekta Janar na KASASCO, Kwamared Yahaya Usman Kabo, ya ce jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abbas ta yi tsayuwar daka da kafa tubalin samun nasara a Zaɓen 2027 da ke tafe, la’akari da cewa tana da Sanatoci biyu da kuma wakilci mai ƙarfi a matakin jiha da tarayya.
Ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ke kaɗawa a jam’iyyar NNPP na da nasaba da tasirin jiga-jigan jam’iyyar da suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da nasararta a Zaɓen 2023.
Sai dai ya ce a yanzu jiga-jigan jam’iyyar ta NNPP na ficewa daga cikinta zuwa APC saboda zargin rashin adalci da mayar da su saniyar ware da ’yan Kwankwasiyya suka yi.
Aminiya ta ruwaito cewa daga cikin jiga-jigan NNPP da suka sauya sheƙa zuwa APC a bayan nan akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo da Zubairu Hamza Massu.
Akwai kuma Abbas Sani Abbas da Baffa Bichi da kuma Sha’aban Ibrahim Sharada.
Ya ce “sauyin sheƙar waɗannan jiga-jigan ’yan siyasa ta karya garkuwar jam’iyyar a Kano. Saboda haka yanzu APC ta warware duk wasu matsalolin cikin gida da take fuskanta domin tabbatar da nasarar a 2027.”
APC ta ce tana da yaƙinin samun nasara a zaɓen da take tafe wanda take fatan bai wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a Jihar Kano.
Sai dai ta ce dawowar Kwankwaso jam’iyyar babu abin da zai haifar sai kawo ruɗani a cikinta.
“A yanzu Kwankwaso ba shi da wani tasiri a siyasance, shi ya sa yake neman mafaka da babu inda zai same ta face a jam’iyyar APC.
“Sai dai yana da kyau ya fahimci cewa APC ba wuri ba ne na samun mafaka kuma ba ta buƙatar irinsu [Kwankwaso] da babu abin da za su kawo wa jam’iyyar face ruɗani.”