2025-06-26@20:51:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2075

«Ammar dan Yasir»:

    Shettima zai kuma ziyarci manyan masana’antu da gonaki a sassa daban-daban na Habasha. Masana’antun sun haɗa da Adama Industrial Zone, Mojo Poultry Farm, Shera Dibandiba Mojo Family Farm, Lume Avocado Nursery, da Bishoftu Pea Youth Farm. Wannan ziyara na da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Habasha, musamman a fannin noma da masana’antu. Firaminista Abiy zai kuma shirya wata liyafa ta musamman a Fadar Shugaban Kasar domin girmama Shettima da tawagarsa, a matsayin alamar ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Nijeriya da Habasha na da daɗaɗɗen tarihin aiki tare, musamman a fannonin tsaro, kiyaye zaman lafiya da kuma haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Wannan ziyara na da burin ƙarfafa wannan dangantaka da kuma samar da damar haɗin gwiwa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke...
    An harbe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne a ranar Talata a yayin wani artabu da jami’an tsaro suka yi a unguwar Makera da ke Kakuri a Jihar Kaduna. Rundunar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin tare da ƙwato tarin makamai da kayayyaki masu daraja da aka sace daga mazauna garin. An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja A cewar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 3:10 na tsakar dare, inda wasu ’yan bindiga 8 suka kai hari a rukunin gidaje na Estate...
      Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin.   Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya.   Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    An kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja. Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu da wani direba a kusa da kauyen na Daku. An sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Izom. ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir Mutanen da aka sace ɗin dai a wancan lokacin sai da suka biya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau An yi jana’izarsu a ranar Talata a Babban Masallacin Abuja, inda manyan jami’ai suka halarta, ciki har da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. An birne su a maƙabtar Gudu, inda Ribadu da Gwamna...
    Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro,  Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa, maharan sun kashe mazauna yankin da dama, tare da hana ayyukan noma, da kuma haddasa durkushewar ayyukan kasuwanci na yau da kullum a yankin. “Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga karkashin jagorancin babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. An hana noma daga Marabar Kankara zuwa ‘Yantumaki, an kashe mutane da dama, an yi garkuwa da wasu, kiwon lafiya ya durkushe. Mazauna garin...
    Ɗaya daga cikin baƙin da suka tafi ɗaurin aure daga Zariya, Abbas Rufa’i, ya bayyana yadda ya kuɓuta daga harin da wasu matasa suka kai musu a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. A cewarsa, “Da muka tsaya a hanya domin yin tambaya, na fito daga motar domin neman hanya. Amma sai na ga yadda mutanen da ke wajen suka fara mana wani irin kallo. Gwamnatin Gombe za ta sayi takin N8.8bn don tallafa wa manoma 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi “Na ji ɗaya daga cikinsu yana cewa, ‘a kashe su gaba ɗaya, a ƙone motar.’” Rufa’i ya ƙara da cewa, “Na cire rigata, na shiga cikin daji har na sai da na samu...
    Majiyoyi sun kuma ce “an kashe adadi mai yawa na ‘yan bindigar”.   Shugaban karamar hukumar, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya ce harin ya kara firgitar da manoman yankin.   Ya ce taimakon gaggawa daga barikin soji na Kontagora ya tilastawa ‘yan bindigar tserewa zuwa dazuka.   Ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu, sun farfasa shaguna tare da kwashe kayan abinci da kayayyaki masu daraja a shagunan mutanen yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata.   Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani ‘yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikin su ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita. Ko wadanne matakai ya kamata ‘yan Najeriya su ringa dauka wajen kare kan su da ma lafiyar jikin su? NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kashe ’yan fashi biyu, sannan sun kama wasu biyu a unguwar Makera da ke Kakuri. Wannan ya biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaro suka da ’yan fashin. Gwamnan Nasarawa ya sanya wa gadar sama sunan Tinubu PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:10 na dare, bayan da suka samu kiran gaggawa daga mazauna unguwar Gashash a Barnawa. Rahotanni sun ce ’yan fashi guda takwas sun shiga wani gida ɗauke da bindigu da makamai, sun sace wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki. Bayan kiran gaggawar, DPO na Barnawa, Kakuri da Sabon Tasha tare da sojoji daga Rundunar 312 Artillery...
      Wasu jihohin da suka hada da Benuwe, Filato, da Borno, a ‘yan kwanakin nan sun samu tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sa sojoji da sauran jami’an tsaro suka kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da kalubalen tsaron ke kara ta’azzara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yaya girman neman fadadar kungiyar NATO yake? Alkaluma ne za su iya fayyacewa: Abun da aka kashe a duniya kan aikin soji a shekarar 2024 ya kai dala triliyan 2.72, inda kungiyar NATO ta dauki dala triliyan 1.5, wato kaso 55 na jimillar ta duniya. Duk da rashin daidaiton karfin soji tsakanin kasashen duniya, NATO na ci gaba da sanya mambobinta su kara abun da suke kashewa a bangaren tsaro zuwa kaso 5 na alkalumansu na GDP. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kaso 67.4 na wadanda suka bayar da amsa sun yi tir da yadda NATO ke gaggauta fadada karfinta na soji, suna gargadin hakan ka iya haifar da sabuwar takarar makamai da yin gagarumar...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna. An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta A cewar wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, motar ‘yan sandan na bin wata mota ƙirar Golf kafin a ji ƙarar harbe-harbe. Nan take mutane suka fara kwanciya a ƙasa domin tsira da rayukansu. Wannan...
    Gwamnan ya buƙaci kamfanin da ke aikin da ya yi aiki mai kyau kuma ya kammala a kan lokaci. Ya ce dole ne a gina gidajen cikin inganci domin taimakawa wajen rage matsalar rashin gidaje da jama’a ke fuskanta a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin. Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori. Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13. Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci...
    Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar, Abdullahi ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa matafiyan a ranar Juma’a, a lokacin da suka bata kan hanyarsu a yayin da suke tafiya don halartar wani daurin aure a karamar hukumar Mangu.   Ya ce, wadanda aka kashen, ba su dauke da wani makami, kawai suna kan hanyarsu ne ta zuwa daurin aure, wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai musu hari tare da kashe su, lamarin da ya jefa ‘yan uwan matafiyan cikin jimami. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da safiyar ranar 3 ga watan Satumban bana, tare da gabatar da jawabi. Kazalika a ranar, kasar Sin za ta gudanar da gagarumin bikin faretin soja a filin Tian’anmen dake nan Beijing, inda shugaba Xi zai duba faretin. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu kuma sun jikkata a harin. Gwamna Sani ya ce kisan rashin imani ne, kuma ya bayyana cewa ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika. Ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira daga harin a Asibitin Rundunar Sojin Naieriya na 44 da ke Kaduna, sannan ya yaba wa jama’ar Kaduna kan zaman lafiya da kaucewa fitina. Ya kuma roƙi shugabannin Filato da su hana faruwar irin wannan mummunan lamari. Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau, ba kira da tura saƙo kawai ake yi da wayar hannu ba; baya ga haka, muhimmiyar hanya ce ta samun kuɗi da bunƙasa sana’o’i. Ko kun san dabarun amfani da wayoyinku don samun kuɗaɗen shiga? NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Idan ba ku sani ba, ko kuma kuna buƙatar ƙarin sani, ku biyo mu a shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci. Domin sauke shirin, latsa nan
    2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
    Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.”   Ya bayyana cewa hukumomin tsaro a Nijeriya suna aiki tuƙuru dare da rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya ƙara da cewa tsarin tsaro a Abuja yana aiki yadda ya kamata tare da nasarori masu yawa wajen gano duk wata barazana da kuma daƙile ta kafin ta faru.   Ministan ya ƙara da cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ba ya nuni da wata...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da gidauniyar Milano Cortina 2026, wanda aka dorawa alhakin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026 dake tafe. Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, sassan biyu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a sassan yayatawa, da tsara ayyukan watsa gasar ta Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina, tare da aiwatar da musayar jami’ai. Sakamakon wannan hadin-gwiwa, CMG ya samu ikon watsa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina dake tafe a shekara mai zuwa a hukumance. An kafa gidauniyar Milano Cortina 2026 a watan Disamban shekarar 2019, domin ya tsara, da...
    Rundunar ‘yansandan jihar Benuwe ta tabbatar da garkuwa da dukkan fasinjojin wata motar bas ta kamfanin Benue Links a hanyar Eke, Ugbokolo a karamar hukumar Okpokwu ta jihar a yammacin Lahadi. Wani ganau da ya zanta da LEADERSHIP ta wayar tarho, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Lahadi, inda wasu ‘yan bindigar suka tare wata motar bas din da ta taho daga Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, suka yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta bayan sun kwace kayayyakinsu, sannan suka tafi da su cikin daji. 2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega Ina Da Isassun Kuɗi, Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ɗaya Don Gyara Jihar Zamfara...
    Bayan faruwar lamarin ne, wasu fusatattun dalibai matasa suka tare hanyar Agaie-Lapai, suna nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa abokin su.   Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Yau 23 ga watan Yuni, 2025 da misalin karfe 3 na dare, rundunar ta samu labarin cewa, da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan daba sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai dake unguwar Ndakitabu ta Lapai, amma maharan sun tsere a lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wurin”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Rikicin Isra’ila da Iran ya kara dagula tabarbarewar harkokin man fetur da iskar gas a cikin fargabar barkewar rikicin Gabas ta Tsakiya wacce ta kasance jigo wajen hada-hadar man fetur da iskar gas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun da ka yi karatu a Italiya, yaya kake kwatanta ci gaban Kano, da na wasu biranen zamani da ka sani? Wannan tambaya ce mai amfani. Birane irin su Milan da Florence da Turin, suna da dogon tarihi a fannin ci gaban birane amma abin da ke bambanta Kano a yanzu shi ne saurin aiki da kuma hangen nesa, kuma wannan gwamnati tana da tsari a fagen. A matsayina na mai tsara gine-gine, zan iya saurin gano kyakkyawan shiri idan na gan shi. Kuma abin da ke faruwa a Kano ya na da kyau sosai. Ana gabatar da abubuwa masu alaƙa da biranen zamani, wato wuraren shakatawa da sanya fitilun titi da magudanan ruwa da kuma kula da tsarin taswirar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na ƙara tsananta, musamman a yankunan Arewa. Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya a kashe su a hanyar Abuja zuwa Kano. A kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a hanyar su ta komawa Kano. Sai na kwanan nan da ya faru a Jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure. NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne da...
    Yanzu haka ana shirye-shiryen gudanar da taron kasa da kasa na tattauna batutuwan raya tattalin arziki na Davos na yanayin zafi karo na 16, taron da aka fi sani da dandalin Davos. A bana za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun Talata 24 zuwa Alhamis 26 ga watan nan na Yuni, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, bisa taken “sana’o’i a sabon zamani.” A bana taron zai mayar da hankali ne ga muhimman fannoni biyar, wadanda suka hada da warware batu game da tattalin arzikin duniya, da hange game da kasar Sin, da halin da masana’antun duniya suka fuskanta na taka musu birki, da zuba jari kan al’umma da duniyar bil’adama da batun sabbin makamashi da hajoji. Game...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce zai so ya taka leda tare da matashin ɗan wasa Lamine Yamal a Barcelona, Rashford mai shekaru 27, wanda ya shafe rabin kakar wasan bara ya na zaman aro a Aston Villa, a halin yanzu yana atisayen ƙara kuzari a ƙasar Sifaniya kafin a fara wasannin share fage na kulob ɗin, yayin da ake ta raɗe raɗin makomarsa a United. Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar yin wasa tare da Yamal, Rashford ya ce: “E, tabbas, kowa yana so ya yi wasa tare da mafi kyawun dan wasa, don haka nima inada wannan burin kuma zamu gani, Yamal, mai shekaru 17, ya taka rawar gani sosai yayin da Barcelona...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ta gudanar da bikin murnar cika shekaru biyar da kafawa, da kaddamar da dokar tsaron kasa ta yankin. Yayin bikin da ya gudana a jiya Asabar, Xia Baolong, wanda shi ne shugaban ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a kwamitin kolin JKS, da ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya ce dokar tsaron kasa ta yankin Hong Kong da aka kaddamar a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2020, ta samarwa yankin damar fita daga hargitsi zuwa yanayi na daidaito, tare da shigar da yankin sabon zamani na gudanar da tsarin “kasa daya tsarin mulki biyu”. Xia Baolong, ya ce...
    Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya zabi dan wasan tsakiya Bernardo Silba a matsayin sabon kyaftin din kungiyar, jaridar Daily Mail ta rawaito Guardiola ya yanke hukuncin da kan sa inda ya ki ya nemi shawarar sauran yan wasan kungiyar, Silba ya maye gurbin Kebin De Bruyne bayan dan kasar Belgium din ya bar Etihad a karshen kwantiraginsa. Guardiola ya kuma nada mataimakan kyaftin guda uku kafin fara gasar kakar wasa ta gaba da suka Ruben Dias, Rodri da Erling Haaland, Silba wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa, ka iya daura kambun kyaftin na Manchester City na kakar wasa daya kawai idan bai samu karin kwantiragi a kungiyar ba. Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun...
    An yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a garin Mangu, da ke Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Waɗanda aka kashe sun haɗa da maza, mata da yara. Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Mahaifin Rahama Sadau ya rasu Dukkaninsu mazauna unguwar Basawa-Anguwan Rimi ne da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna. Sun tashi ne daga Zariya zuwa Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure, amma aka kai musu hari a hanya. An yi jana’izarsu tare da birne su da yammacin ranar Asabar a maƙabartar Hayi, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro. Malamai a Mangu sun ce iyalan mamatan sun amince a birne su...
    Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
    Daga ranar 18 zuwa 21 ga watan nan bisa agogon Rasha, an gudanar da dandalin tattaunawa tattalin arziki na kasa da kasa na St. Petersburg karo na 28 a kasar ta Rasha. Yayin taron, an sake gayyatar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG don halartar dandalin a matsayin abokin huldar yada labarai. CMG, ya gina wani wurin baje koli mai zaman kansa a cikin wurin taron, da kafa dakin nuna shirye-shirye, da yin hira da manyan baki, kuma ya ba da rahotanni game da dandalin a cikin harsuna da yawa. Ban da wannan kuma, a yankin baje kolin, an nuna sabon sakamakon aikace-aikacen fasahohin zamani na AI, wanda CMG ya yi nazari da kansa, da...
    Daruruwan mutane ne suka halarci taron bikin bauta na Fuxi, wanda yake zaman kakan al’adun gargajiyar kasar Sin, a birnin New Taipei na yankin Taiwan na kasar a yau Asabar. An gudanar da taron bautar ne a daidai lokacin da aka yi irinsa a birnin Tianshui dake arewa maso yammacin lardin Gansu, inda ake kyautata zaton a nan ne aka haifi Fuxi. Wannan dai ita ce shekara ta 12 a jere da al’ummomin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ke gudanar da bukukuwan bauta a lokaci guda ga fitaccen jarumin, tun bayan da aka fara gudanar da ire-iren wannan bikin a shekarar 2014. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya yi kiran hada karfi da karfe a bangaren kasa da kasa don karfafa tattaunawa domin ganin an yayyafa ruwa ga rikicin Isra’ila da Iran. Wakilin, Fu Cong ya ce, yayin da rikicin yake-yaken sojoji na Isra’ila da Iran ya shiga kwana na takwas, abin bakin ciki ne ganin yadda lamarin yake janyo asarar rayukan fararen hula da dama tare da lalata kayayyakin aiki a dukkan bangarorin biyu. Ya kara da cewa, idan har wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, ba kawai bangarorin biyu ne za su tafka babbar asara ba, hatta sauran kasashen yankin lamarin zai yi musu mummunar illa. Fu Cong, ya fada wa wani taron gaggawa na kwamitin sulhun...
    Ana fargabar mutum biyar sun mutu a sakamakon tashin bom a Jihar Kano a ranar Asabar. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ba bayyana cewa bom ɗin soja ne ya tashi. Kwamishinan ya ce akwai yiwuwar kuskure wurin safara ko kuma wurin kula da abin fashewan. Ya bayyana haka ne a yayin ziyarar gani da ido da ya kai wurin da abin ta tashi.  
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako.   Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu, da tunanin jama’a, da kuma a matakin aiki. Yanzu ‘yan Nijeriya za su iya tabbatar da cewa manyan hanyoyin mu sun fi samun tsaro ƙwarai idan aka kwatanta da ‘yan shekarun baya.”   Ya lissafa nasarorin da rundunonin sojin Nijeriya suka samu a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da yankin Arewa-maso-gabas da gaɓar teku. “Daga nasarar ragargaza sansanonin Boko Haram da ISWAP...
    Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv. Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500. Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci. Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran. 2027: Manyan ’Yan...
    A yau Juma’a, mai magana da yawun rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin reshen gabashi Liu Runke, ya soki lamirin kasar Birtaniya, bisa yadda ta zuzuta abun da ya wakana yayin wucewar jirgin ruwan sintirinta ta zirin Taiwan a ranar Laraba. Liu Runke, ya ce rundunar ta PLA reshen gabashi ta girke dakaru domin sanya ido ga yadda daukacin lamarin ya faru, tare da tabbatar da kasancewa cikin matakin koli na ko-ta-kwana, tare da aiwatar da matakai yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    4- Nisantar duk wani abu da zai cutar da shi, saboda musulunci ya yi umarni da kula da rai. Don haka, zai yi kyau a matsayinki na sabon aure, ki nemi shawarar magabata da kuma likitoci, saboda ki gujewa abin da zai cutar da yaronki. 5- Zuwa asibiti lokaci bayan lokaci, don tabbatar da lafiyar yaronki. Allah ne mafi sani   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar  Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba. Jami’an tsaro sun ƙwato makamai da kama mutane 398 a Kaduna Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom Takardar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, wanda shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka...
    Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya da nasara tare, muhimman ginshikai ne na ci gaba mai dorewa na hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fuskar raya tattalin arziki da kasuwanci, inda dukkan bangarorin biyu gami da duniya ke cin gajiya. A halin yanzu, habakar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya, kuma kara hada kai ita ce mafita daya tilo ta shawo kan hakan. Ya ce ci gaban kasar Sin zarafi ne ga...
    Hukumar tantance fina-finai ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wani da ya yi amfani da sunan barkwanci don yada abin da ya kira da “nishadi mai tada zaune tsaye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao, ya janyo hankalin ƙungiyoyin Arsenal da Bayern Munich a bana. Amma ɗan wasan mai shekaru 22 ya amince da kwantiragin shekaru shida a Barcelona, wanda hakan zai sa ya hadu da abokinsa kuma abokin wasansa a matakin ƙasa Lamine Yamal a Nou Camp, Williams ya buƙaci Yamal da ya taimaka masa wajen zuwa Barcelona, bayan kakar da ya yi a Bilbao inda ya taimaka musu...
    Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin karshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a wadannan kasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntubar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun karin umarni.” Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da fada tsakanin Isra’ila da Iran, tare da bukatar bangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare hakkin dan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci. Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yan Najeriya da dama ne dai da suka yi ilimin zamani dole ta sa suka rungumi sana’o’in da a baya ake ganin na kaskantattu ne don su samu na sakawa a bakin salati. Mai yiwuwa hakan ne ya sa wasu, musamman matasa, suka yanke kauna da cewa shafe lokaci ana karatun kan iya taimaka wa mutum magance bukatunsa nay au da kullum. NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamnan ya ƙara da cewa: “Tinubu ya cancanci goyon bayanmu, kuma ba za mu daina yaba masa ba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shawara ta uka ita ce, hawa teburin tattaunawa da shawarwari ta zama babbar hanyar samar da mafita. Inda ya ce, dole ne mu yi tsayin daka wajen tabbatar babbar alkiblar da za a fuskanta kan warware matsalar nukiliyar Iran ta zama ta hanyar siyasa. Ta hudu, ya bayyana cewa kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya abu ne mai matukar muhimmancin gaske. Kuma ya kamata kasashen duniya musamman ma manyan kasashen da ke da tasiri na musamman kan bangarorin da ke rikicin, su yi kokarin yayyafa ruwa amma ba akasin haka ba. Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na son ci gaba da karfafa zantawa da gudanar da tsare-tsare da dukkan bangarorin, da kuma taka...
    Dangane da sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar na cewa za ta maido da yin tambayoyi ga dalibai kafin a ba su biza kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta lura da batun, kuma tana fatan Amurka za ta aiwatar da kalaman shugaba Trump na maraba da daliban kasar Sin da su zo Amurka don yin karatu. Dangane da wani rahoto da wata cibiyar bincike ta kasar Switzerland ta fitar, inda ta bayyana cewa, matsayin karfin yin takara na yankin Hong Kong na Sin ya karu zuwa matsayi na uku a duk fadin duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan na nuni da matsayin Hong Kong na musamman da kuma alfanun da ake da shi, da kuma...
    Brig.-Gen. Abu-Mawashi ya kara da cewa an kama ‘yan ta’adda 14,138 da sauran masu aikata laifuka yayin da aka ceto mutane 5,365 a cikin wannan lokaci.   Abu-Mawashi ya ci gaba da cewa, sojojin sun kwato daruruwan makamai da kuma harsashi da yawa duk acikin wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.” Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma hakan ya saɓa da Sashe na 391 na Dokar Laifuka 89, Dokokin Tarayya na shekarar 1990. Hukuncin laifin yana ƙarƙashin Sashe na 392 na wannan doka. A wani tuhumar daban, an zargi Sanata Natasha da yin irin waɗannan kalaman game da Akpabio a cikin wata tattaunawa ta waya da wata Sandra C. Duru a Abuja, a ranar 27 ga watan Maris, 2025. An ƙara tsaurara...
    Wasu na ganin jita-jitar ta samo asali ne bayan wani abokin aikinsa na baya, Sani Sidi, ya koma jam’iyyar APC tare da magoya bayansa a Kaduna. Amma Sambo ya ce hakan bai shafe shi ba. Hakazalika, an shirya Sambo zai halarci bikin ƙaddamar da asibiti mai gadaje 300 da ke Kaduna a ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Ya halarci bikin kuma hakan ba yana nufin ya goyi bayan wata jam’iyya ba ne. Ƙungiyarsa ta nanata cewa Sambo yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, kuma labarin sauya sheƙar nasa ƙarya ce da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da ƙoƙarin cimma wasu muradu na siyasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar. Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar. Taron na...
    Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba. Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kashe akalla manoma 20 da wasu mutum uku da kuma wani dan sinitiri a jihar Katsina. An kashe mutanen ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai karamar hukumar Kankara, daya daga cikin yankunan da suka fi fama da kalubalen tsaro a jihar. A cewar wani mazaunin yankin da bai amince a bayyana sunansa ba, “Kimanin kwanaki shida da suka gabata ’yan bindiga suka kai hari kauyukan Yargoje, Kwakware, Danmarke, Gidan Dawa da kuma Burdugau. Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a Zamfara NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na “Sun kashe kusan manoma 20, sun sace wasu sannan suka sace shanun da manoman ke amfani da su wajen huda...
    Al’ummar garin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara, sun gudanar da sallar roƙon ruwa bayan da aka shafe kwanaki ba tare da an samu ruwan sama ba. Mutane da dama sun fara nuna damuwa saboda har yanzu babu ruwa ba, duk da cewa an shiga lokacin damina tun da daɗewa. NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi Wasu manoma da ke jiran ruwa domin su yi shuka sun ce har zuwa ranar Laraba sun fito domin roƙon Allah Ya saukar da ruwa. Babban limamin garin Kaura, Malam Badamasi, ne ya jagoranci sallar. Ya ce sun ga dacewar yin wannan addu’a ne domin tun mako...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan. A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan...
    Idan dai za a iya tunawa, a baya an kai hari gidan dangin Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 15 ga Afrilu, 2025, ba tare da an kama ko daya daga cikin maharan ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari.   Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya...
    Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha mai tsafta wanda kamfanin CGCOC na kasar Sin ya tallafa wajen gudanar da shi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, ta yin aiki tukuru a fannin samar da ababen more rayuwa, da kai tsaye za su inganta rayuwar al’ummun kasar. Shugaba Tinubu ya bayyana aikin a matsayin muhimmin mataki na tabbatar da al’ummun birnin sun samu ruwa mai tsafta, mai dorewa kuma isasshen a gidaje da hukumomi, da dukkanin sassan birnin. Ya kuma godewa gwamnatin kasar Sin da kamfanin CGCOC, bisa hadin gwiwarsu wajen tabbatar da nasarar aikin. Yayin da yake nasa tsokaci kuwa a bikin kaddamar da aikin, mukaddashin jakadan Sin...
    Aiki ceton, ya samu hadin gwiwar kungiyoyin ceto da suka hada da Red Cross da Hukumar Kula da Ruwan Kogin (NIWA) da jama’ar garin Yauri.   A ranar Laraba, an yi jana’izar Mutane uku, a garin Hikiya da ke karamar hukumar Rohiya a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada. Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare...
    Sauran sun hada da: Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun.   Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a kan karagar mulki, sannan gwamnatin jihar ta siya musu motocin alfarma.     Bincike ya kuma nuna cewa, motocin da aka ce kudinsu ya kai Naira biliyan 2.5. Bayan sun sauka akan mukaminsu, sun tafi da motocin kuma duk kokarin da aka yi na su dawo da su, lamarin ya ci tura.   Sai da gwamnatin jihar ta sake sayo wa ‘yan majalisar na yanzu motocin da kudinsu ya kai kimanin...
    An gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar Kazakhstan, daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Yunin shekarar 2025, don halartar taron koli karo na biyu na Sin da tsakiyar Asiya. A karshen ziyarar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da lamarin. Wang Yi ya ce, babban abin da ya fi daukar hankali a wannan taro shi ne sanarwar da shugaba Xi Jinping ya yi ta “Ruhin Sin da Tsakiyar Asiya”. Inda shugabannin kasashen yankin tsakiyar Asiya suka amince baki daya kan kiyaye wannan ruhi, da inganta tsarin kasar Sin da tsakiyar Asiya don samun sabon babban ci gaba. Bugu da kari, dangane da halin da ake ciki a yankin...
    Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara asibiti da ke Makurdi, Babban Birnin Jihar Benuwe, domin duba waɗanda da suka jikkata a hare-haren da ‘yan bindiga suka jihar. Shugaban ya je ne domin ganin irin ɓarnar da aka yi, tare da nuna alhini da goyonnsa baya ga al’ummar jihar. Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti  Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato Hotunan ziyayar sun nuna Tinubu yana duba da waɗanda abin ya shafa. Go hotunan a ƙasa:
    Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka. Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi...
    Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan ziyara a matsayin gwada gwamnati kan yadda za ta shawo kan matsalolin tsaro, musamman a jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da na ƙabilanci. Kisan da aka yi a Yelwata, wanda shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren, ya janyo suka damuwa a faɗin ƙasar tare da ƙara matsin lamba ga shugaban ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa don tabbatar...
    Wani mazaunin yankin, Abdullah Zuru, ya ce yankin ya samu zaman lafiya a baya, inda manoma suka koma gonakinsu kafin wannan mummunan hari. Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba dangane da harin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Da farko mun ɗauka yana wasa ne, amma kafin wani ya kai ɗauki, ya riga ya kunna wa kansa wuta.” Wata mazauniyar yankin, Aisha Salisu, ta ce yana matashin yana shaye-shaye. “Ba ya cikin hayyacinsa. Ana jin warin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, kuma yana karkarwa da ihu,” in ji ta. Mutane sun yi ƙoƙarin taimaka masa. Wasu sun ja shi zuwa cikin ruwan da ke wata magudanar ruwa a gefen hanya, amma wutar ta riga ta yi masa ƙone sa. “Abun ya zama kamar fim kuma mai ban tsoro,” in ji wani direban adaidaita sahu mai suna Ibrahim Jafar. “Ko bayan da suka jefa shi cikin ruwan, wutar ba ta daina ci nan take ba. Fatar jikinsa duk...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya.   Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya. Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya. Kazalika a kwanakin nan wani hari da aka kai a wasu yankunan jihar Binuwe yayi sanadiyyar halakar mutane da dama, wadda hakan ya jawo...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF. An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53 Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da...
    Daga karshe Musa ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin na baya-bayan nan, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.   Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 200 ne aka kashe a wani hari da aka kai a Yelwata da ke karamar hukumar Guma, wanda galibi ya hada da ‘yan gudun hijirar da ke neman mafaka a wani cocin Katolika na yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron koli na kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu. A cikin jawabinsa, Xi ya ce, yayin da kasar Sin da kasashe biyar na yankin tsakiyar Asiya ke tafiya kan hanyar samun ci gaba a cikin dogon lokaci, sun kafa “Ruhin Sin da kasashen tsakiyar Asiya” na “Mutunta juna, da amincewa da juna, da moriyar juna, da taimakon juna, da inganta zamanantarwa tare ta hanyar samun ci gaba mai inganci”. Yayin da ya ambaci yanayin rashin kwanciyar hankali da duniya ke fama da shi, ya ce ta hanyar tabbatar da adalci ne za a iya cimma burin kare zaman lafiya, da samun ci...
    Sinawa tun zamanin baya na ganin cewa, samun dadi ga kowa shi ne dadi na gaske. A zamanin yanzu, kasar Sin ba kawai take jin dadin sauye-sauyen da ke faruwa a sassan hamada na kasar ba, hatta ma tana fatan ganin karin yankunan hamada sun zama dausayi a fadin duniya. Don haka, take kokarin bayar da fasahohinta ga kasashen Afirka da su ma suke fuskantar kalubalen kwararar hamada. Bisa nazarin da masanan Sin da kasashen Afirka suka yi, sun gano cewa, fadin sassan hamada a yankin Sahel ya ragu daga kaso 72,31% zuwa 69.23% tsakanin shekarar 2000 zuwa ta 2020. Daga Taklimakan zuwa Sahara, karin abubuwan al’ajabi na ci gaba da faruwa bisa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta...
    Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa gwamnatin Jihar Katsina na ƙoƙarin sasantawa da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar. Wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke Jibia, Batsari da DanMusa sun amince da zaman lafiya tare da miƙa makamansu. Sai dai wannan hari na baya-bayan nan ya sa al’umma sun fara shakkar ko zaman lafiyar zai ɗore. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila.  Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game da lamarin. Ya bayyana haka ne a yayin da yake hawa jirgi domin barin ƙasar Kanada, inda ya halarci taron ƙasashen G7. A yayin taron, shugabannin ƙasahen sun bayyana Iran a matsayin barazana, da bai kamata a bari ta mallaki makaman nukiliya ba. A ɗaya bangaren kuma sun bayyana ’yancin Isra’ila na kare kanta. Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan harin Iran Sarki ya...
    Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
    A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev gabanin taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na biyu. Kazalika, daga bisani duk dai a yau shugabannin biyu za su halarci bikin musayar rubutaccen daftarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kazakhstan. Xi ya isa Astana, babban birnin Kazakhstan yau Litinin, domin halartar taron koli karo na biyu tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Za a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a lokacin ziyarar shugaban ƙasa. Tun da farko, Tinubu ya yi Allah-wadai da rikicin da ke faruwa a Benuwe, inda ya yi kira da a zauna lafiya. Haka kuma, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a sanadin rikicin. Tinubu ya shirya kai ziyara Jihar Kaduna a ranar Laraba domin ƙaddamar da ayyukan gwamnatin jihar, amma yanzu ya ɗage ziyarar zuwa ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi  Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
    A cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, mai lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, na cewa, IGP ya bukaci a mika Bature zuwa gaban wani jami’i, SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis 29 ga Mayu, 2025, domin amsa tambayoyi.   In ba a manta ba, IGP a watan Disamba, 2024 ya ba da irin wannan umarni tare da tura jami’an sa ido na IGP domin su kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano tare da kai shi hedikwatar rundunar da ke Abuja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Sojojin kasar Iran sun cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan HKI a dazuda nan nan, wayo yau lahadi a ci gaba da musayar wauta da suke yi da sojojin HKI kwanaki uku da suka gabata. Kamfanin dillancin  labaran kare kai na kasar Iran Tasnim ya nakalto sojojin kasar na cewa sun cilla makamai masu linzami da Drones a karon farko da rana ido na ganin ido a kan HKI kuma tuna makaman sun fada a inda yakamata su fada a cikin haramtacciyar kasar. A safiyar ranar jumma’a ce sojojin HKI suka kai hare-hare kan birnin Tehran inda suka kai manya-manyan jami’an sojojin kasar ga shahada, sannan suka kashe mutane fararen hula wadanda...
    Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyaana cewa kasarsa bata rufe kofar diblomasiyya dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, matukar HKI zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kasar. Kamfanin dillancin  labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Lahadi a taron yan jaridun da ya kira a birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana son ta ci gaba da shirinta na makamashin Nukliya ta zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya idan an bata damar yin haka. Ministan ya ce ikidar JMI ne warware dukkan matsaloli da farko ta hanyar Diblomasiyya, da kuma tattaunawa amma ba zamu taba amincewa  wani ya hanamu hakkimu na mallakar makamashi nukliya ta zaman lafiya ba....
    Babban kwamandan dokarun khatamul Ambiya (s) a nan birnin Tehran ya bayyana cewa sojojinsa zasu ci gaba da fafatawa da HKI har zuwa lokacinda zata dakatar da kawowa Iran yaki, ko kuma ta sami nasara a kansu, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Shudmoni, yana fadar haka a yau Lahadi bayan da suke cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu da nesa kan HKI a karon farko na rana, a cikin kwanaki uku da fara yakin. Janar Shodmani ya kara da cewa zasu ci gaba da kaiwa yahudawan hare-hare har zuwa lokacinda zasu yi nadama sun daina yakin. Kwamnatin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun saminar kasar lalata cibiyoyin da...
    Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran ta shiga yaki, kuma don haka dole sai an sami sauyi a rayuwar mutane ba. Fatima Muhajirani ta bayyana cewa daga yau ramukan layin dogo a cikin birnin Tehran wuraren mafaka da muyewa ne na mutanen da suke birnin har’ila yau za’a bude masallatai da makarantu don su zama wuraren samun mafaka. A wani bangare fatimeh Muhajirani ta bayyana cewa an rufe sararin samaniyar kasar Iran, don haka babu jirgi wanda zai tashi a ciki ko wajen kasar har zuwa abinda hali yayi ta kuma kara da cewa a halin yanzu jirgin kasa zai zama hanyarb tafiya mafi sauki a wannan haling a mutane. Tace mahajjan Iran zasu dawo ta hanya...
    Bisa la’akari da haka, a fili kasar Sin tana adawa da matakin da Isra’ila ta dauka na keta dokokin kasa da kasa, inda ta kai wa kasar Iran hari, lamarin da ba za a amince da shi ba, musamman ma ta la’akari da yadda kasashe daban daban ke ci gaba da neman hanyar daidaita batun nukiliyar kasar ta Iran ta hanyar siyasa. Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci Isra’ila da Iran da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da lalubo bakin zaren kasancewa tare cikin kwanciyar hankali da lumana. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    An shiga zaman ɗari-ɗari a garin Makurdi na Jihar Benuwe, bayan ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu masu zanga-zanga a shataletalen Wurukum. Masu zanga-zangar sun fara taruwa da misalin ƙarfe 9:30 na safe domin nuna fushinsu kan kisan mutane sama da 100 a garin Yelewata da ke Ƙaramar Hukumar Guma, a ranar Asabar. Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina Tun kafin fara zanga-zangar, jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban sun mamaye manyan hanyoyi a birnin Makurdi. Da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na safe jami’an tsaro, ciki har da motar yaƙi ta ‘yan sanda...