Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Nguema ya sami kaso 94.85.%  da hakan ya mayar da shi akan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takara.

Nguema dai tsohon janar ne wanda ya yi juyin Mulki a cikin watan Ogusta na 2023 da ya kifar da gwamnatin Ali Bongo Odnimba.

Magoya bayan Nguema sun yi bikin  hukuncin da kotun ta yanke na samun nasarsa. Zaben ya kawo karshen matakin rikon kwarya bayan kifar da gwamnatin iyalan Bongo da su ka yi kusan rabin karni akan karagar Mulki.

Zababben shugaban kasar ta Gabon ya yi alkawalin sake gina cibiyoyin gwamnatin kasar da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

Gabon dai kasa ce mai arzikin man fetur, sai dai kuma mafi yawancin mutanen kasar suna rayuwa a cikin talauci.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsofaffin Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu Tare Da Bashi Shawarwari Kan Matsalolin Tsaro
  • An Fara Zaman Jin Ra’ayoyin Jama’a Kan Sauya Kundin Tsarin Mulki A Kano
  • Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba
  • 2027: Masu Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP Sun Kara Matsa Kaimi Bayan Ficewar Atiku
  • Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
  • Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
  • Kungiyar “Human Right Watch” Ta Yi Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Kasar Nijar Muammad Bazoum
  • Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati
  • Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na kasa
  • Brazil Ta Shiga Yaki Da HKI, Inda Ta Kudurin Anniyar Goyon bayan Afirka Ta Kudu A Kotun ICJ