Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
Published: 30th, April 2025 GMT
A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana.
An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida.
DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a BornoPSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba.
Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0 a Emirates a cikin watan Oktoba.
Arsenal da Paris Saint-Germain da Inter Milan da Barcelona su ne kungiyoyin da 4 da suka kai matakin zagayen daf da karshe na gasar.
A wannan Larabar ce kuma za a yi karon batta tsakanin Inter Milan da Barcelona, bayan kimanin shekara 15 da aka yi makamancin wannan karawar daf da karshe tsakanin ƙungiyoyin biyu a Gasar Zakarun Turai.
Inter Milan ce ta kai zagayen ƙarshe a 2010, sai dai wannan karon Barcelona na fatan lashe kofin bana da zarar ta fuskanci Arsenal ko Paris St Germain a watan gobe.
Sai dai, Barca da Inter sun fuskanci juna a gasar ta zakarun Turai a 2022/23, inda ta Italiya ta yi nasara 1-0 cikin Oktoban 2022 a wasa na biyu suka tashi 3-3 a Sifaniya.
Wannan shi ne karon farko da Barcelona ke fatan kai wa karawar ƙarshe a Champions League, tun bayan da ta lashe na biyar jimilla a 2015.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arsenal Barcelona Gasar Zakarun Turai
এছাড়াও পড়ুন:
China Ta Maida Martani da Haka Kayakin Kiwon Lafiya Na Tarayyar Turai Shigowa Kasar
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China.
Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba.
A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.